← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 201

Sashe 107

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwata kwata baya iya hangensa saboda ya kashe light din dakin, duhu ne ko'ina.

Sautin kukansa da baba Obie ya jiyo yayi matu
aga hankalinshi, cikin raunanniyar muryarsa ya shiga ambaton sunan shi Owais Owais, jikallena?

Meya faru?

Kukan ka nake ji ko kunnena ne su ke jiyo min ba daidai ba?"
Cikin shesshekar kuka ya ce, "Baba muna a cikin tashin hankali, jiya da daddare baka ji jiniyar motoci ba?"
"Owais na ji, wani abu ya faru ne?"
"Eh baba, jiya an kawo mana farmaki, muna tsaka da bacci, wasu miyagu suka ritsa da mu, kafin mu
auki mataki sun raunatar da wasu daga cikin mu..."
Bai
are maganar ba, ya ji baba Obie yana ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, cikin ru
u da tashin hankali, "Owais dawa dawa suka farmaka..."
"Gidana, harma sun
auki yara biyu daga cikin yaran da nake kula, bayan haka sun farmaki auta, baba muna zargin da sa hannun Elders.

Muryarsa da tashin hankali ya ce, "Owais me suka yi mata?

Sun cutar min da ita?

Tana raye?

Owais ka fadamin!

Ina Saratu take?"
"Tana a kwance rai hannun Allah, gaba daya sun faffasa mata fuskarta da glass, kwata kwata bata a hayyacinta sunan ka ka
ai take fada, ba don munyi saurin kaita asibiti ba da tuni rai ya yi halinsa, ga shi ka kalli videon ta da na
auko maka." Ya fada tare da tura wayar ta cikin tagar.

Baisan sa'adda ya sanya hannu ya kar6a ba sai dai ya ji babu wayar a hannunsa alamar ya
auka, cike da zumudi yake jiran ya gama ya ji me zai ce fatansa Allah yasa ya taimaka masa.

"Owais, ku yi hakuri, komai ya faru ni ne na ja maku, laifina ne!

Da nasan zasu ci amanata da ban boye maka su wanene sauran ba, gashi nan har sun fara farmakar ahalina, dama nasan za'a rina tun da ba Allah ne a ransu ba, wallahi tun da har suka ta6a jinina bazan
yalesu ba, sun ja ma kansu bala'e da musiba..."
Farin ciki ne ya lullu6e zuciyar Owais.

Aje masa wayar yayi kan tagar ya zura hannu ya
auka.

"Baba kada ka damu dan Allah, ni ban nuna maka don na
aga maka hankali ba face don ka taimaka mana mu nemi mafita, in ba haka ba zasu iya
ara farmakar mu..." Bai kare maganar ba, ya katse shi cikin fushi ya ce, "Owais, yaran da suka
auke meye sunayen su?"
"Unaisah yarinyar da zan aura,
ayar kuma sunan ta Batool, mun neme su sama ko
asa mun rasa baba!

Na manta ma ban fa
a maka ba, na gano mutun biyu cikin Elders, Musa da
an iya, kuma muna zargin Musa ne ya shirya komai.

Da jin wannan maganar yasa baba Obie ya gano me suke shirin
ullawa wato basu daddara ba bayan gargadin da ya yi masu akan su aje makaman ya
insu su gudu su nemi mafaka, amma saboda ha
ama
arfin ikon shi suke so su
wace shiyasa suka
auke yaran don su cika sharuddan, kuma yafi zargin musa ne kamar yarda ya fa
a, saboda yasan mugun halin shi zai iya komai don ya cika burin sa.

"Baba ka yi shiru ba ka ce komai ba, meya kamata muyi yanzu?

Yaran tun jiya suka sace su bayan isha'e suka tafi da su, bana so su cutar da rayuwar su, gaba daya komai ya kwance mana!"
"Owais, you have my word babu abun da zai faru da su, in har ba sun riga da sun cutar da su ba saboda jinkirin da kuka yi baku sanar da ni ba, amma ku shirya rundunar sojoji ku tafi kurkukun
addara yanzun nan, suna a can tare da yaran, kafin ku isa taimakona zai riga ku isa."
Godiya ya yi masa cike da zumudi ya juya cikin sauri ya tafi.

Kafin ya bar gidan saida ya fara zuwa falo ya sanar da Uncles dinsa yadda suka yi da baban, sun ji dadi bayan sunyi masa fatan alkhairi ya fito daga gidan ya shige motar shi, Ya ce da driver dinsa ya kaishi Headquarter
insu, kafin su isa ya kira layukan senior agents dinsu ya ce su yi gaggawar shirya rundunar sojojinsu daga ya
araso zasu tafi kai farmaki gidan Kurkukun
addara
(Kunji Yadda aka yi Suka yi Nasarar Kama Elders)
Wani taimako baba Obie ya yi masu?

Bayan tafiyar Owais, cikin duhu ya zauna kan kujerar gaban madubin dakin sa, da tsafi ya yi amfani, Duk Elder din da ya kira sunan shi zai bayyana ta cikin madubin, gaba daya saida ya kira Elders din kurkuku mazauna kasashen waje, ya ce sun kuwa san da makircin da Musa ke shirin
ulla masu?

A rude suka ce basu gane me yake nufi fa?
ya yi murmushi saboda ya gane Musa bai sanar da su ba, shi kadai ya ke shirin shi,
Ya ce dama ya san bazai sanar da su ba, saboda baya son su sani, amma zai fada masu yanzu haka Musa ya dauke
addarar kurkuku, da bugun zuciyar kurkuku, Kuma ya tafi da su gidan Kurkukun don ya aiwatar da sharuddan dodon tsafinsu, in har suka bari Musa ya cimma burinshi, babu tantama zai
wace sihirin jikinsu ne sannan ya kashe su, ya ce abun da ya sa ya fa
a masu saboda ya tsiratar da su daga kaidinsa saboda shi ma Musa bai
yale shi ba, jiya ya turo da giants sun farmaki ahalinsa, tun da har shi da ya yi mashi halacci ya butulce masa su su wanene da suke tunanin ba zai ci amanar su ba?"
Maganar da Obie ya fada masu tayi matu
ar daga hankulansu, da ya ga sun yarda da shi ya kuma cewa, "Ni ban damu wani daga cikin ku ya samu karfin ikona ba, amma ku yi tunani idan Musa ya hau karagar mulkin Elder me zai biyo baya?

Kun dai san halinsa ba sai na fada maku ba, kun kuma san me zai iya da wanda ba zai iya ba, " Abun da ya harzu
a su ta yadda Musa ya 6oye masu abun da yake shiryawa, shi yasa suka yi amanna da maganar baba Obie..

Daga karshe ya ce masu yanzu ya rage nasu!

Ko dai su yi gaggawar zuwa gidan kurkukun kaddara kafin rana ta fadi ko kuma su yi dana sani na har bada, yana
are maganar, ya rufe madubin nashi da sihiri.
auko wayarsa ya kira layukan sirri na Jan ido da Jan le6e bayan sun
aga suma ya fa
a masu abun da Musa ke shirin aikatawa.

Jan Ido ya ce shi bai damu ba don hankalinsa ba a kwance yake ba, asirin shi ya riga da ya tonu, neman mafaka ya ke yi,
Baba Obie ya ce mafaka
aya ta rage masa, ya gaggauta zuwa gidan kurkukun
addara, Musa yana a can zai cika sharuddan dodon tsafi, idan suka samu
arfin ikon shi zasu fi
arfin kowa, in ma suka so zasu iya shafe memory
in mutanan da suka san sirrin su.."
Da jin wannan maganar yasa suka amince zasu je gidan Kurkukun
addara...
(Kun ji yadda a kai Obie ya ha
a Elders gaba daya a gidan kurkukun kaddara saboda ya sawwa
awa su Chief Owais don su kama su duka, da yake
wararrun matsafa ne har wadanda ke a nesa da zarar sun so zasu 6ace su dira a inda suke son su kasance, shiyasa suka ha
u cikin
anin lokaci.)
Sannan kuma ya tura Evils din jikinshi zuwa Prison Temple don su hukunta Musa, wa
annan Evils din da suka zane Musa da bulalai ba asalin Temple Evils bane, ba mutane bane, shai
anun aljanu ne masu ha
arin gaske, su
in amintattun Obie ne babu mai iya sarrafa su sai shi a cikin mutane, umarnin shi ka
ai suke ji, tushen su daga jikin mahifiyarsa ne a ranar da aka haifeshi a ranar suka koma jikin shi, tun yana jariri suke a tare da shi.

Duk fa yana a cikin
akinsa ya aiwatar da komai, hatta Mark da ya butulcewa Musa Obie ne ya yi silar komai..

Yasan cewa shine amintaccen likitansa kuma yana tunanin shi zaisa ya cire masa zuciyar yarinyar saboda yasan jikinta bazai jure sihirin su ba.

Aikuwa da ya tashi kawai daga inda yake ya tura Evil
aya na jikinshi ya umarce shi da ya shiga jikin Mark, ya fa
a ma evils din jikinshi shine ya turo shi don su sarrafa tunanin Mark, su hana shi cire zuciyar yarinyar su kuma taimaki rayuwar yaran..

Gaba
aya komai da ya faru bada sanin Mark ba, gangar jikinsa ce kawai, amma bashi ke sarrafa kanshi ba, aikin Evils ne.

Obie ba
aramar tsiya ya yi masu ba, lokacin da haya
in nan ke fita daga hancinansu shine ya umarci kowani Evil da ya bar jikin Elders harma da Giants ya kuma
wace garkuwar sihirin jikinsu ya lalata komai ya barsu da halin su..

Sun da
e suna she
e ayarsu sai gashi rana
aya a lokaci
aya Allah ya nuna masu iyakarsu, yanzu kuma saura su gir6i abun da suka shuka
Ta yadda akai Batool ta ku6uta, lokacin da ta farfa
o daga suman da ta yi, ta tsinci kanta a cikin
akin fi
a saman gado, cikin ru
u da razana ta soma kiciniyar kwance sar
in jikinta, tana ta kuka kamar ranta zai fita, adaidai lokacin Musa da Mark suka shigo
akin tiyatar, wani irin tsoro ne ya mamaye zuciyarta ko magana bata iya yi sai zazzare idanu ta ke, akan kunnanta suka tattauna game da yadda zasu cire zuciyarta, gabanta ya shiga fa
uwa ta rasa ya zata yi, gashi babu Unaisah a kusa, a cikin zuciyarta ta dinga karanto La'ila ha'illa anta subhanaka Inni kuntu minazzalimin.

Bayan da Musa ya fuce daga
akin, Dr.
Chapter 107 · 0% Book details