← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 201

Sashe 42

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai amsa masa ba Yace"ba wannan na tambayeka ba, baka cancanki ka sani ba, kaida kaso ka kashe ta Allah bai nufa ba, kawai ka fadamin su wanene sauran Elders saboda tace min kun kai ku goma sha biyu, shida suna jagorantar gidan kurkukun kaddara, sauran shiddan kuma ba'a kasar nan suke ba, sune suke safarar yara daga kasashen waje suna shugo maku da su gidan kurkukun
addara.."
"Owais, naso ace zan iya fada maka su wanene su amman ba zan iya ba, dokar aikin mu ce, amana ne kuma alkawari ne a tsakanin mu, wani bazai tona asirin wani ba, don haka kayi hakuri ba zaka taba ji abakina ba, nidai na mika wuya, Aminina basai kun sha wahalar kama shi ba, shima ya mika wuya zai kawo kan shi, su kuma sauran ba zasu taba canza ra'ayin su ba, tun da har kun ceci rayuwar sauran yaran da suka rage, kuyi
ari ku sanya musu tsaro, sannan taimakon da zanyi maku shine ku yi gaggawar gano su wanene sauran Elders din ku kama su, idan ba haka ba, kama ni da kukayi kamar kun kashe maciji ne baku sare kan shi ba, ko dai ku kamo sauran Elders din, ko kuma ran kurkukun kaddara ya dawo fiye dana da..."
wani irin faduwar gaba Chief yaji, Cikin rawar murya ya fara yi masa magiya akan ya fada masa su wanene in ba haka ba taya zai iya gano su? su da suke matsafa kama su zaiyi masa wuya.

Baba Obie yace"Owais, Kai fa musulmi ne, meyasa zaka nemi taimakon matsafi uhum?

Shiru yayi bai tanka masa ba.

"Ka nemi taimakon Allah Owais, shi kadaine zai kawo maka mafita, duk da banyi Imani da Allah ba, amma bayan da asirina ya tonu na zauna nayi nazari na gane cewa Allah yana da karfin ikon da babu wani mahalukin da yake da shi, zai iya mayar da abu mara yiwuwa ya zama mai yiwuwa tabbas naga ishara akaina Owais, Dan Haka inaso ka mika lamuranka gare sa, kuma bana so damuwar abun da na aikata yasa kayi rauni Owais, bana so kayi sanya, bana so ka karaya, jarumtakar nan taka da kwazon ka, da kaifin basirarka su nake so ka farfado da su gurin bada himma akan aikin ka..."
hakika yayi mamakin kalaman baba Obie, Har cikin ransa yaji dadi daya fara gane Allah daya ne, kuma Yaji dadin karfafa masa gwiwa da yayi duk da bai samu abunda yakeso agurin sa ba..

"Danish Yana araye ko ya mutu"?

Kamar daga sama yaji ya tambaya..

"Bani da masaniya akan hakan, tun ranar da muka je kai farmaki ya fada cikin rijiya tare da sabon garkuwar ku amma meyasa ka tambaye ni bayan nasan kasan komai"?

"Hmmm, kawai Ina mamakin wani abu ne, amma ina kokwanto owais.."
"Zan iya sani"?

"Kawai kayi abun da nace maka owais, shi kadaine taimakon da zan iya yi maka ayanzu, sannan idan har aka kawo maku farmakin bazata, Kayi gaggawar sanar dani Owais..."
yaso ya kara yi mashi wasu tambayoyin amma saiya hakura ya bari zuwa wani lokacin yanzu hankalinsa ya karkata akan gano su wanene sauran Elders din..
_"kaddara da bugun zuciyar kurkuku, Ku sanya musu tsaro, rayuwarsu tana a cikin hatsari, da su ka
aine za'a iya dawo da ran kurkukun kaddara a halin Yanzu"_
Lokacin da Obie ya furta maganar shi ta karshe, Chief owais bai jiyo shi ba.
baisan Ya tafi ba saida yaji shiru babu motsin mutun tukunna ya sauko daga kan gadon Ya nufi kayan abincin da Owais ya jefo masa ya zukunna yana tattara warmers din guri guda..
*Daga Al
alamin Boss Bature
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*~___________________________________
Lokacin da sheikh Imam zai tafi rokonsa suka dinga akan kada ya tafi yabarsu, ya zauna atare da su, ya fahimci kamar suna jin tsoron ya tafi yabar su, gani suke kamar idan ya tafi zasu kara shiga cikin damuwa ne, lallashinsu yayi tare da basu hakuri yace in sha Allah kullum zai dinga kawo masu ziraya sannan su jure su danne damuwarsu kada su bari tun yanzu agane halin da suke a ciki, yakamata su cigaba da zuwa masallaci yin sallah saboda mutane sun damu da rashin zuwansu, su cigaba da gudanar da komai kamar yadda sukeyi ada, cike da ladabi suka amsa mashi da toh har bakin motarsa suka rako shi, har zai shiga ciki ya juyo ya fuskance su, idanunsa cike tab da kwalla, suma idanun nasu kwallarce ta cika su, bayin Allah sun koma abun ban tausayi, kafin tafiyarsa yace ma Owais ya jira kiransa, sannan yace ma sharafuddeen next zuwan da zaiyi zasu raka shi asibiti ya dubo jikin Hajiya saratu da momma daga bisani ya yi musu sallama ya tafi har saida sukaga motar shi ta bace ma ganin su tukunna suka koma ciki jikinsu asanyaye...

Sheikh Imam yana driving yana share kwallar dake kokarin gangaro masa kan kuncin sa, bakomai ya ke tunawa ba face labarin rayuwar prisoners daya ta6a Zuciyar shi, ga tausayin Ahlin Obie daya mamaye zuciyar shi, shiyasa ya za6i ya tafi yabar su saboda ya samu damar da zai huce radadin da ya ke ji a zuciyar shi..
_____________________________
Da marece
a lokacin gaba
ayan su suna a falo zazzaune kan Sofas zun zabga tagumi kamar masu zaman makoki, damuwar rashin dawowar chief ne ya hana su sukuni, Unexpected suka jiyo motsin shigowar mutun falon, ransu ne ya basu shi ne ya dawo, Kusan atare suka mike cike da zumudin ganin shi, kwata kwata basu lura da halin da ya ke a ciki ba, jikin su na bari suka nufe shi don suyi mashi sannu da zuwa, sai dai ko kallo basu ishe shi ba, bai kula kowannansu ba hatta Taj Da Unaisah, kaitsaye ya juya ya nufi part dinsa batare daya waiwaye su ba, Ya Ilahi, jikinsu ba karamin sanyi yayi ba, ganin yadda Chief ya sauya babu annuri ko walwala akan fuskarsa, abun dayafi daga hankulansu share sun da yayi, Batool har kuka saida ta yi..

Kasa jurewa su ka yi hakan yasa suka wanki kafa suka nufi part dinsa, a bakin kofar dakin suka tsaya gaba dayansu, suka soma yin knocking din kofar hadi dayi mashi magiya akan ya taimaka ya bude musu kofar amma yayi shiru bai tanka musu ba, babu alamun zai bude masu kofar.

Lamarin Ya
aure musu kai, sunyi matu
ar damuwa da shi, Yadda ya wuni a cikin
aki ba ci ba sha, haka suma suka wuni abakin kofar dakinsa baci ba sha, lokacin salla ne kadai ke tayar da su, haka zasuje suyi sallar ko sun dawo bakin kofar a datse suke taras da ita, da suka matsa da rokonsa akan ya fada musu mai ke damunsa dakyar yace su taya shi da addu'a Allah ya yaye mashi abunda ke damun shi, Ya kuma kawo masa mafita acikin lamuransa, badan sun so ba, suka amsa ma shi da toh, kuma su ka daukar mashi alkawarin zasuyi mashi addu'a, yayi wannan maganar ne acikin dakinsa yayin da suke awaje suna sauraron shi, Zuciyar su ta karaya ba ka
an ba.

Almost hours, Chief bai le
o daga part dinsa ba.

Wuni su ka yi kamar marasa lafiya, saboda damuwar da su ka yi da shi.

Ko sun kira layin shi baya yin picking.
__________________________________ELDERS
gaba
ayan su suna a kwakkwance kan wasu hadaddun Plush poolside loungers dake a cikin Katafaren Gidan Gonar su, aljanar duniya an kawata shi da kayan alatu kamar ba za'a mutu a barshi ba, kwata kwata babu riguna a jikinsu sai short, kirjinsu da bayansu a zane yake da tattoo na tambarin kurkukun
addara, sun rufe rabin fuskokin su da gold mask su shida ne gefe da gefen su matasan yan mata ne masu jini a jiki sanye da short gown a jikin su, launin ja, sun saki gashin kansu ta baya, hannayen su ruke da madaidaicin tray mai dauke da expensive bottles na whisky wanda a kalla farashin kowace kwalba yakai 1.5 million dollars, cikin kulawa su ke yi serving dinsu a cikin wasu hadaddun crystal glasses yayin da wasu daga cikin yan matan suke yi masu tausar kafadun su.
daga gabansu wani tankameman Swimming pool ne makil da ruwa launin pure blue sky, ga wasu ha
un Floating bean bags da ke shawagi saman ruwan, tantiran karuwai ne kwance asaman su masu dirarran jiki, sanye da swim suit da suka bayyana tsiraicin su, kowaccensu ta manna Sunglasses a idanun ta, saboda haduwar su idan ka kallesu saika sake kallon, sukai su goma sha biyar, daga ganinsu ba jinsi da ya bane, hankalinsu kwance suke shakatawarsu ga iska dake ratsa fatar su..

A hankali ya ke zukar cigarettes din dake a hannunsa idan ya sha
a har ta hanci yake buso hayakin ta tsabar kwarewa...

"Maganar da Jan harshe ya fa
a ta kona min rai, na kwana da ita acikin zuciyata, arayuwata na tsani mutumin da zai yi min magana da tsawa, bayan haka ya kira ni da kaskantacce, har ni zaice wai ban kai darajar takalmin Elder ba?

Kawai saboda sun taba taimakona arayuwa nayi aiki a karkashinsu shine har suka samu damar da zasu yi min gori...." rai abace ya fa
Jan le6e yace"ni banga abun damuwa ba, yanzu fa tasu ta
are, kabarsu suji da kunyar duniya, ai sun tabka babban kuskure da suka amince zasu mika wuya, ban taba sanin elder maloho bane sai wannan karon da ya karaya, saboda son ya'ya ya rufe mashi ido, har shawara ka basu basu dauka ba, saboda dakikanci da shafewar basira, ka jira ka gani da kansu zasuyi danasani...."
gaba
aya suka bushe da dariya da wannan budaddiyar muryar tasu mara dadin ji...

Jan Ido yace"ni abun daya bata min rai, meyasa suka ki bamu sihirinsu bayan sunce sun tuba?
Chapter 42 · 0% Book details