← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 201

Sashe 80

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

It's not true, it will never be true"
Yana magana zufa tana wanke fuskarshi, Ummi dake kallon shi gaba daya tabi tasha jinin jikinta ganin yadda lokaci daya big boss ya nemi zaucewa, yama rasa ina zai sa kanshi kamar mahaukacin, kanshi ya daure da Jin abun da bai ta6a zata ba, ko a mafarki, mamakin shi taya akai Unaizah ta tafi da diary din ta batare daya ankara ba?

Yana nan sake da baki Yana ganin cewa wayonsa da dubararsa ba zasu taba bari asirin shi ya tonu ba sai gashi
aramin kuskure yana nema yaja masa matsala.
wata irin
ara ya fasa tare da nufar maidaidaicin glass table din dake a seating area din dakin Ya kinkime shi, da sauri Ummi tabi bayanshi, Kafin Ta karaso Ya buga table din kasa nan take Ya tarwatse, ruko hannayensa tayi a cikin nata,
cikin shesshekar murya ta furta"big bosa kada ka lahanta kanka, na fada maka ni ban yarda da su ba, dama nasan idan na fada maka zargin da su ke yi maka dole kaji ba dadi, pls kazo muyi magana, nayi maka alkawarin in har baka da laifi zan yi iya
arina don wanke ka daga zargin da ake yi maka"
bangajeta yayi da hannun shi tayi taga taga zata fadi, da sauri Ya damki arm dinta yana huci ya furta"har yanzu baki fadamin tayaya akai suka san ina atare da ke ba"?

Tamkar zata fashe mashi da kuka tace"wallahi bani na fada masu ba, ka yarda dani, ban ta6a fitar da sirrinka ba.."
muryarsa da tsawa yace"karya ki ke yi Ummi, ba zasu taba neman ku hada baki ba gurin kamani batare da sunsan muna a tare ba, saboda ganina ba abune mai sau
i ba.."
cike da jin shakkar shi tace"hakane, ay na fada maka, hotonka dana Natasha suka gani a cikin diary din, aranar da mu ka je airport a america tare da Natasha sun ganta, babu wanda baisan
awata bace, bayan haka akwai ranar daka kira video call, bana akusa na shiga toilet,
aya daga cikin yaran da nake kula da su ta shigo dakina da karanbani ta dauki wayar ta
aga kiran anan taga fuskarka, wallahi big boss yarinyar ko waya bata iya ba, babu komai akanta bansan ya akai ta
aga kiran ba...."
bata boye masa komai ba.., Sakin arm dinta yayi tare da dafe kanshi da tafin hannunsa.

Ita kanta ta tsorata da yanayinsa karfin hali tayi gurin firta"tunda na fada maka abun da ka ke son ji, Nima inaso ka amsa min tambayana big boss, tayaya akai Unaizah ta zama daya daga cikin fursinonin kurkukun kaddara?

Waya kaita bayan a labarin da naji mahaifinta ne Ya sadaukar da ita,...."
tiryan tiryan ta zayyana mashi labarin Unaizah, ta kara da cewa"Abun ya dameni, tun da naji labarin ta, saboda nasan Unaizah
arka ce, kuma kaine mahaifinta, amma na ru
e da naji yadda suka bada labarin cin amanar da mahaifinta yayi mata, ya yaudare ta ya kai ta kurkukun kaddara da sunan High school na korea, Big boss Ina Unaizah?

Kuma wacece Zeenatu diyarka mai bala'en kama da Unaizah...
bata kare maganarba Ya balbaleta da masifa, yana fadin meyasa take yi mashi tambayoyi kamar tana tuhumarsa?

Ko itama ta yarda da abunda ake zargi akansa?

Bayan bai ma taba sanin ina ne gidan kurkukun da take magana akai ba, balle wasu elders, shi bazai iya aikata munanan laifukan da ake tuhumarsa ba, tafi kowa sanin halin shi don haka ta rabu da shi, Yarinyar da take magana akai ba Yar shi bace, shi
aya gare shi Zeenatu, Kuma itace baby preetyn da take magana akai.."
Yana magana yana huci kamar zai rufe da bugu, baima kare maganar ba Ya fuce daga dakin tabi bayan shi sai dai kafin ta karasa taji ya datse kofar, bubbugawa tayi taji ta a datse.

Wani irin matsanancin ciwon kaine Ya taso mata, a daddafe ta nufi gefen gadonsa ta zauna, Zuciyarta ta karaya, saboda ta ga tsantsar rashin gaskiya atare da big boss din ta, abunda take jiyema fargaban Ya zamana gaskiya, Ya zatayi da rayuwarta?

Ina zata sa ranta taji dadi?meyasa big boss Zai daga hankalinsa akan abunda Yake ikirarin bai aikata ba?

Meyasa ya canza mata a lokaci?

Meyasa ba zai kare kansa ba?

Ya salam
Kifa kanta tayi saman pillow, hawaye suka cika idanun ta, ga wani bugun barazanar da zuciyarta keyi mata, tana jin tsoron abin da zai biyo baya, wayarta ta
auko don tayi Kira sai dai koda ta duba screen din wayar ya tsastsage bata iya ganin komai, gashi ya kulle ta adaki no way out..
~_______________________________
Bacci ya
aurace wa idanunsu ganin shiru Aunty Ummi bata dawo ba, kuma har time din Chief da daddynta basu dawo ba, sun yi jiran har sun gaji.

Suna akwance kan gadonsu sanye cikin pyjamas, sun hada kai suna kallon wani korean drama a wayar Unaisah, ba laifi kallon Ya
ebe masu kewa duk da hankalin su ba akwance ya ke ba.

Kiran wayar Taj ne ya shigo wayar Unaisah, a hanzarce tayi picking ta kara a kunne.

"Unaisah har yanzu bakuyi bacci ba"?

Muryarta da shagwa6a tace"daddy ba zamu iya bacci in har baku dawo gida ba"
"Kuyi hakuri ku kwanta, Ku huta pls, nan bada jimawa ba zan dawo gidan"
"Toh daddy, Ina mommyna ba zata zo taga babynta ba" yar dariya yayi"gatanan a gefena, tana sauraronki.." bai kare maganar ba, Muryar Benazir ta katse shi"Babe barka da dare Ya kuke Ina fata Kuna lafiya"?

"Lafiyalou mommy, nayi missing naki, inason ganinki, Kin ki zuwa kiga babynki"
dariya Benazir tayi"Sorry, Kina araina, Gidan naku ne sai da izni ake shigar shi, ni da anila munata jira, sun ce zasu tuntu6emu in sha Allah zamu zo"
bata kaiga furta kalma ma, Batool ta kwanto da kanta saman wuyan ta,"Mommy, barka da dare, Batool ce, Ina uncle Shureim din mu, munyi missing nashi.."
"My baby Batool, Uncle shureim yana lafiya, shima yayi missing naku, kullum sai ya tambayeni ina babyn nan mai kama da shi"
dariya batool tayi saboda dadin da taji"please mommy, ki gaishe min da shi, ki fada mashi ina kaunar shi"
"In sha Allah zai ji, don ma baya akusa da mu ai dana bashi kun gaisa, amma zan sa ya kiraku ku gaisa" washe baki tayi"mungode mommy"
"Okay, babes, ku kula mana da kanku, Ku kwanta kuyi bacci, yanzun nan daddynku zai dawo.."
amsa mata sukayi da toh bayan sun katse kiran, Unaisah ta daura phone dinta akan ta batool dake akan Nightstand, hugging din juna sukayi babu alamun zasu runtsa saboda tunanin Aunty Ummin su da bata dawo ba.

A hankali wata dankareriyar Mota baka, ta shararo izuwa main entrance gate Na villa din owais, ko da ganin ba
uwar Mota, Security Officers suka yi saurin nufo motar, tare da yiwa mata
awanya, knocking Glass din motar sukayi tare da bashi Umarnin Ya sauke glass don suga wanene shi, banza akayi da su har saida suka fusata kamar zasu 6a66ake window glass din motar tsabar yadda suke kwankwasa shi.
sai da na cikin motar ya mula yasha iska tukunna ya zuge masu window glass, Tare da sauke Shade din dake akan fuskar shi, Waro idanu waje su ka yi cike da mamaki, a hanzarce suka buga kafa tare da sir mashi kusan atare suka furta"Sorry Sir.."
ayataccen murmushin gefen fuska ya dan saki, yayin da yake a zaune saman Driver's seat.

"Ina fata na same ku lafiya"?

"Lafiyalou Sir, munyi mamakin ganinka, bamu san ka samu lafiya ba,Ya jikin naka" still da murmushi yace"Alhamdulillah, naji sau
i, Owais bai fada maku bane?

Ya tambaya da mamaki kan fuskarsa su ka ce wallahi bai sanar da su ba, basu san komai ba game da samun lafiyar shi ba, ko sun tambaye shi sai dai yace masu da sau
i jikin shi.

"Ku yi masa uziri, Kunsan yanayin aikin namu, Yana a ciki"?

"A'a sir, tun safe daya yabar Gidan har yanzu bai dawo ba"
Okay, ya fa
a tare da yiwa motar key, Ya shige cikin gidan.

Fitowa yayi daga Ciki, Jikin shi sanye da Kaftan, ya fito fess abun shi ko tabo babu akan skin insa, kamar bai taba jin rauni ba.

Lokacin daya shiga Falon gidan bai Iska kowa ba, zama yayi a falon tare da daura kafarsa daya kan
aya.

Chef ne ya shugo falon daga kitchen, yana hangosa da sarsarfa Ya nufe shi bayan sun gaisa yayi mashi ya jiki.
daga bisani chef din ya tambaye sa ko yana bukatar abinci ya kawo masa?

Da bu
ar bakinsa sai cewa yayi"ina Unaisah da Batool"?

"Suna a cikin dakin su"
"Ka kira mun su, Inason ganin su"
Amsa mashi yayi da toh, kafin ya juya ya nufi
akin su Unaisah
Bayin Allah har sun fara bacci, suka farka jin knocking, Batool ce ta bude kofar tana mika da hamma ta dubi Chef din
"Big guy, yazo, yana a falo yana son ganin ku"
waro idanu waje ta yi cike da mamaki tace"big guy Yaji sauki!

Da kanshi yazo, Wayyo Allahna, Alhamdulillah ka fa
a masa, gamu nan zuwa.."
juyawa tayi ta nufi Unaisah dake ta juyi kan gado, ta bubbuga kafafunta"sis Ki tashi, Big guy ne ya zo, ya samu lafiya yana a falo, yanzu chef ya fadamin yana son ganin mu"
dakyar ta samu Unaisah ta sauko daga kan gadon tana mika tace"Dagaske Ya omar ne Ya yazo?

Shi ka
ai yazo ko tare da wani"?

"Kinga ki zo mu je mu gaishe shi daganan sai muyi mashi ya jiki"
Mayafi kowaccen su Ta yafa ma kanta, suka fito da sauri suka nufi falo, tunkan su karasa suka hango shi zaune kan sofa mai mazaunin mutun uku ya daura kafarsa daya kan daya, Yayin da yake danna wayarsa a hankali
Jin motsin tafiyar su ne yasa shi
agowa da lumsassun idanunsa da suka kada jawur ya dube su.

Cikin girmamawa suka zauna suna fuskantar shi.

"Ya omar dagaske kaine?

Munyi kewarka!

Ya jikin naka?

Ina ya salsabeel"?
Chapter 80 · 0% Book details