← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 201

Sashe 121

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sir Mubarak ya ce, "Bamu san komai game da yaron ki ba, bayan da ya rasu su wanene su ka yi jana'izar sa?"
Cikin shesshekar kuka ta ce, "Bayan da muka je asibitin suka tabbatar mana da mutuwar sa, na dinga kuka kamar raina zai fita, docs da nurses suka dinga lallashina a lokacin ma bana jin harshen hausa ban san me suke cewa ba, sai idan Praveen ya fassara min da indiyanci nake fahimtar me suke fa
i, a
arshe na fita hayyacina na yanke jiki na fa
i a sume, ban
ara sanin meke faruwa ba, lokacin dana farfa
o na ganni a gadon asibiti kwance ga Praveen a gefe, cikin ru
u na tambayesa da gaske Naufal ya mutu ko mafarki na yi?

Ya ce min inyi hakuri ba mafarki bane, da gaske Naufal ya rasu, yau sati
aya kenan bana a hayyacina, harma sunyi jana'izarsa, sun
one gawarsa a crematorium kamar yadda muke wa mamaci a al'adarmu ta hindu, bazan iya misalta maka halin da na shiga ba a lokacin.

Bayan rasuwar Naufal da wata
aya, ya ce zai kawo ni gurin dangin matarsa, amma yana so ya garga
e ni kar in kuskura in fa
a ma wani akwai aure a tsakanin mu, idan ba haka ba, zai rasa auran shi, kuma zasu kai
arar mu kotu.."
Ya yi min barazana sosai, ya ce duk abun da ya fa
a akaina in amsa da haka ne na amince masa, ranar dana fara tsintar kaina a cikin estate
inku bazan misalta farin cikin da na ji ba, duk da wasu basu kar6e ni da hannu bibbiyu ba, wa
anda nake ta zumu
in gani saida na yi danasanin ha
uwa na da su saboda
yarar da suke mini.

Hajiya Saratu ta tsane ni,
anta ma sun tsane ni, basu san ni auntyn su bace, kuma ni ka
ai ce dangin ubansu da ya rage a duniya, amma na yi masu uziri komai da ya faru Praveen ne sila, da tun farko ya fa
a masu matsayina a gurin su ya kuma daraja ni da ba su tsane ni ba, kuma hada
arin muna zaune a gidanku shi ya ja min
anci a gurinsu.

Kuma wlh ya so ya maida ni gidansa amma ni na nuna bana so saboda na saba da ku, ina son ahlinku, na
aukeku kamar dangina da na rasa..."
Bata
arashe maganar ba, ta ji ya saka hanky kan fuskarta, a hankali yake share mata hawayenta, idanunsu a cikin na juna, duk sai ya ji ba da
i, ya yi danasanin marin da ya yi mata, kuma da ya san bata da sanya hannu da ba abun da zaisa ya tuhume ta.

"Ya Mubarak, ka taimaka ma rayuwarmu, ku yafe mana, ku bar mu mu ci gaba da zama tare da ku, zamu gyara kuskuren mu"
Murmushin takaici Sir Mubarak ya yi.

"Ki fa
a min meyasa kika bi Praveen kuka gudu?

Kinsan laifin da ya aikata..?" Gabanta ne ya fa
i rass!

Cikin rashin nutsuwa ta fayyace masa komai da ya faru.

Girgiza kai ya yi cike da takaicin
aryar da Praveen ya yi mata.

"Hmmmm, Praveen ba gaskiya ya fa
a maki ba, ba Hajiya Saratu bace me laifi, batasan da aure a tsakanin ku ba, kuma ba ita bace ta tura maku aljanu ba, hasila ma tsoron hul
a da mai aljanu take yi balle har ta yi mu'amala da su, bayan haka yanzu haka da nake maki magana, Hajiya Saratu tana a kwance gadon asibiti.."
Cikin ru
u da tashin hankali ta furta, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un!

Meya faru da ita?

Meke damunta?

Meyasa praveen ya yi min
arya ne?

Ni dai Allah Ya sa bashi bane ya yi silar kwanciyarta gadon asibiti ba..!"
Ta fa
a da damuwa akan fuskarta.

"Ya Mubarak ka fadamin meke faruwa?

Wani laifi Praveen ya aikata ma ku?

Shiru ya yi yana sauraron muryar Owais dake yi masa magana ta cikin earbuds din dake a ma
ale da kunnansa, komai da suke tattaunawa yana sauraron su, Sir Mubarak ne ya kira shi don ya ji komai.

Cikin harshen yarbanci ya ce, "Owais, ina fata ka ji komai?"
On the Other hand Owais ya ce, "Na ji Uncle, Hajjaty bata da laifi, bata san komai da Praveen ya aikata ba.."
"Ta nemi in fa
a mata meke faruwa kana ganin yakamata mu sanar da ita?"
"Uncle, ka fadamin ta yi 6arin ciki, nasan i war haka jikinta babu lafiya, jininta zai iya hawa, a yadda na ji sha
uwarta da Praveen, idan ta ji abun da ya aikata zata shiga mawuyacin hali ne, amma me zai hana mu bari sai ta ji sau
i sosai?"
"Owais, ka yi magana mai ma'ana, na gode da shawararka."
Daga haka suka yi sallama ya mayar da dubansa ga hajjaty, dama jiran shi take yi ya gama wayar,
"Pls ka fa
amin wani laifi ya aikata?

Dan Allah kada ka ce zaka 6oye min, na fada maka bani da kowa in ba Praveen ba, shine gata na, bana so na rasa shi! kuma me ke damun Hajiya Saratu?"
Numfasawa ya yi kafin ya ce, "Allah shine gatan bawansa Hajjaty, zan fa
a maki amma ba yanzu ba, ki fara samun lafiya tukunna, sannan karki damu da maganar hajiya Saratu, ta ji saukin jikin ta yanzu."
In a cool voice ta ce, "Shike nan zan jira har zuwa lokacin da zaka fadamin!

Amma dan Allah ina Praveen ya ke?"
"Karki damu, Praveen yana a wurin mu, kuma mun sanya doc sun yi masa treatment na rauninsa."
"Zan iya ganin shi?"
"A'a, ba yanzu ba." Gya
a kai tayi, "Shikenan..."
"Amma yana inane?

Kuma ni a ina nake?"
Bai amsa mata ba sallamar Nurse ta katse su, mikewa ya yi ya nufi nurse din, "Pls, ki ci gaba da bata kulawa, duk abun da take bukata ki yi mata shi, ina so ta samu cikakkar lafiya."
"Okay sir, zan yi iyakar bakin kokarina.." Juyawa ya yi tare da kallon Hajjaty da ke kallon shi.

"Zata kula da ke, ko me kike bukatar ci ko sha ki tambaye ta zata yi maki, idan kika zauna salin alin, Praveen zai kasance cikin
oshin lafiya..

"
tana kokarin yi masa magana ya sa kai ya fuce daga
akin, kamar ta fasa ihu..

"Pls, baiwar Allah, ki fadamin ina ne nan?

Meyasa ya kawo ni?

Kuma meke damuna ne?"
"Am sorry ma'am, bai bani izinin in fa
a maki inda kike ba, bansan komai ba, abun danasani ya kira ni ne don in duba lafiyar ki.." Shiru ta yi zuciyarta duk ba dadi.
~_________________________________~
To fa manema labarai sun fara dandazo a layin Obie Estate sun ha
a uban cunkuso, burin su kawai su samu damar ganawa da ahalin Obie don su samu na
aukar rahoto, ba dan dakarun sojojin da ke a kewaye da Estate din ba da tuni sun 6urma ciki saboda tsabar za
uwa, masu ruwa da tsaki a mulkin
asar, sun kasa sun tsare suna jiran jin meke faruwa?

Haka zalika
an jami'iyar Jdp da App sun
agu da su san meke faruwa, saboda duk sun ji labarin kewaye gidajen
an jam'iyarsu da soldiers suka yi, dama cikin yan kwanakin nan mutane sun fara tsegumin rashin jin
uriyar baba Obie, basu ji labarin yana a
asar ne ko ya yi tafiya ba, haka Alhaji Musa ma sun ji shiru babu duriyar shi,
an-iya da ya fi kowa baki kusan kullum suna samun labaran yan siyasa a bakinshi ta gidajen radio da shafukansa na social media shima sun ji shiru ba labarinsa.

Saboda yadda mutane ke kiran layukan su a waya yasa suka kashe wayoyin su.

Alhamdulillah Hajiya Saratu ta samu lafiya, har an sallame ta, amma momma har yanzu memory
inta bai dawo ba.

A main Falo na gidan baban suka ha
u gaba
ayan su domin tattaunawa game da shawarar ya zasu yi da jama'ar da ke jiran su ji daga bakin su?

Kowan nan su yana fargaban asirin mahaifinsu ya tonu, saboda gudun tozartar da zai yi da kuma su kansu, suna zullumin mutuncinsu da zai zube a idon duniya.

Gaba
aya sun nuna basu san a fallasa sirrin, saboda basu son asirin shi ya tonu a bainar jama'a, suna jin fargaban abun da zai biyo baya, da kuma halin da uban nasu zai shiga, kuma basu son a gurfanar da shi gaban kotu, sun
wammace su bashi poison ya sha ya mutu, saboda basu son ma su ga tashin hankalin da zai fuskanta,
wara ya mutu su san babu shi a duniyar, duk da mutuwar ba hutu bace a gare shi, amma su a wurinsu
wara tun da ba a gabansu zai fuskanci abun da ya shuka cikin kabarinsa ba, amma in yana a raye sun san ba
yale shi za'a yi ba, dole ya fuskanci mummunan hukunci mai tsanani, ba zasu iya jure ganin halin da zai shiga ba, kuma ba zasu iya kashe shi da kan su ba, sannan basu son ya kashe kan shi, sun rasa ya za su yi da shi?

Duk da fushin da suke yi da shi hakan baisa sun daina jin
aunar shi ba, kwata kwata ba su son ya wulakanta a idon duniya, duk da sun san ko sun rufa mashi asiri hakan ba zai hana asirin shi ya tonu ba, sannan Allah yana sane da komai, ko sun rufa masa asiri wallahi ba zai tsira ba tun a gidan duniya sai ya ga sakayyar abun da ya aikata, sai Allah ya kamasa, tayaya ma zasu goyi bayan rufawa azzalumi asiri?

Bayan sun san Allah baya a tare da azzalumai, sun kuma san hakan ba daidai bane zama su ja ma kansu ne, bayan haka idan har suka nuna son kai, suka nemi su rufa masa asiri ko su 6oye shi, Allah ba zai bar su ba su kansu.

Hajiya Saratu ta yi kuka tamkar ranta zai fita, ta dinga magiya tana ro
on yayyan nata akan kar su tona asirin Baba, kada su mi
a shi ga hukuma, su taimaketa su taimaki rayuwarta, idan ta rasa baba ina zata saka ranta?
Chapter 121 · 0% Book details