← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 201

Sashe 40

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sanyin murya ya tambaye su tun da suke arayuwarsu sun taba fuskantar mummunar kaddara ko wata jarabawar rayuwa irin wannan"? har suna hada baki gurin furta aa sukace su tun da suka taso rayuwarsu basu ta6a fuskantar kaddara mara kyau ko wata jarabawar rayuwa ba, nasara da jin dadin rayuwa kadai suka sani, idan ma akwai abun daya taba sanyasu kuka da idanunsu to bai wuci ranar da suka rasa mahaifiyarsu ba, acewar su His excellency, gyada kai sheikh imam yayi idanubsa cike tab da kwalla yace"wannan ne karo na farko da zasu fara fuskantar mummunar jarabawar rayuwa, yace shi tunda ya taso rayuwarshi yana jin labarai iri iri na irin jarabawowin da mutane suke fuskanta wasu su daga hankalinsa wasu su sashi zubar da kwalla saboda tausayi, amma bai taba jin kaddarar data girgiza shi irin tasu ba, yajiye masu bakin ciki da takaicin abunda mahaifinsu ya aikata musu, ya tausayawa rayuwarsu, amma kada su karaya, nan ya fara yi musu nasiha mai tsuma zuciya...
_Abun da akeso a yayin da Allah ya jarabce bawa da wata mummunar kaddara, Ana kwadaitar da su da su amsa jarabawan da hakuri da godiya suyi biyayya ga Allah, domin hakan yana tabbatar da gafara da lada daga Allah, kuma Allah yana tare da masu hakuri, sannan dukkan tsanani yana a tare da sauki_
_Wani lokaci Allah yakan jarrabi bayinsa da musibu domin ya daukaka su, kuma ya kankare zunubansu, kamar yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yake cewa_
_(For every misfortune, illness, anxiety, grief, or hurt that afflicts a Muslim, even the hurt caused by the pricking of a thorn, Allah removes some of his sins.")_
Duk wata musiba, ko rashin lafiya, ko damuwa, ko bakin ciki, ko cutarwa da ke damun musulmi, ko da wata
aya ce da ta same shi, Allah yana kankare masa wasu daga cikin zunubbansa"_
A cikin suratul Ankabut ayata 2
_Allah buwayi yace"Ashe Mutane Suna Tsammanin Cewa Za'a Barsu, (Don Kawai) Sunce Munyi Imani, Alhalin Kuma Su Baza'a Jarabcesu / Baza'a Fitinesu Ba?_
_Acikin suratul Surah Al-Baqarah Allah yana cewa_
_Wa lanablu wannakum bishai
im minal khawfi waljoo
i wa naqsim minal amwaali wal anfusi was samaraat, wa bashshiris saabiroon._
_"Kuma lalle ne, zamu jarrabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da nakasa daga dukiya da rayuka da 'ya'yan itace, kuma ku yi bushara ga masu hakuri."_
_"Ku tuna cewa hikimar Allah da iliminsa sun wuce fahimtar mutum, Maimakon tambayar dalilin da ya sa Allah ya jarrabe mu, ya kamata mu mai da hankali ga amsa jarabawowin da imani, da hakuri, da godiya_
_Annabi Muhammad (SAW) ya ce, "Babban lada yana tare da fitintinu masu girma, idan Allah ya so mutane sai ya jarrabe su, kuma wanda ya yarda da shi ya samu yardarsa"_
_Kaffarar Zunubai Allah yana iya jarraba mutane domin ya tsarkake su daga zunubansu, kuma idan suka yi haquri za a gafarta musu zunubansu._
_And sometimes Allah tests us with calamities and sometimes with blessings, to show who will be thankful and who will be ungrateful, and who will obey and who will disobey, then He will reward or punish them on the Day of Resurrection _
_Kullum ka
auka cewa kana cikin jarabawa ne, domin dukkanin rayuwarka jarabawa ce, Allah zai jarabceka da abubuwa daban daban, wa
anda ka sani da wa
anda baka sani ba, tsammaninka kayi juriya kayi ha
uri_
_Ba kullum ne zaka samu rayuwarka ta kasance maka yadda kake so ba, akwai ranar farin ciki, sannan kuma akwai ranar ba
in ciki, akwai ranar samun riba, sannan kuma akwai ranar (fa
uwa) yin asara"_
_Haka jarabawar rayuwa take, amma babu makawa duk abinda ya faru gareka, idan kayi biyayya ga Allah, sannan kuma kabi manzonsa, ha
a zaka kasance daga cikin masu cin nasara a duniyarsu da kuma lahira"_
Tunda Imam Ya fara yi musu nasiha jikin su yayi sanyi lakwas, Imani ya kara shigarsu, nasihar shi ta ratsa zuciyarsu sosai, musamman daya tunasar da su irin yadda annabawa suka fuskanci jarabawowin rayuwa masu tsanani kuma sukayi hakuri sukai biyayya ga Allah, sai suka ga tasu jarabawar bakomai bace somun ta6i ne, sannan yace yasan basu fara ganin komai ba, sai lokacin da abun ya fallasa duniya ta sani a wannan lokacinne zasu fara fuskantar kalubalen rayuwa amma baya son su karaya, kuma su daina jin fargaban mutane su sani, laifin nan basu suka aikata ba, Allah ya sani, kuma yana atare da su, don haka su mika lamuransu gare sa, sannan su dage da yiwa kansu addu'a akan halin da suke a ciki, shima zai tayasu, In sha Allah wata rana sai labari, zai zama kamar ba'ayi ba, sai dai tashin zance, kuma kada su kuskura duk runtsi duk wuya su jefa kansu a mawuyacin hali saboda maganganun da mutane zasu fada akansu, koda zasu rasa mukamansu ne kada su karaya, mutane basu da wuta basu da Aljanna ba zasuyi masu hisabi ba, kada su ji kunyar laifin da basu suka aikata ba, koda za'a cuzguna masu ne, ayi musu kazafi, ko azage su aci zarafin su, kada su kuskura su canza daga yadda suke, saboda sau dayawa mutane suke jaza ma mutun bakin cikin da zai zaiyi silar da zai tsani kansa ya kuntata har yayi tunanin kashe kanshi bayan yin hakan kuskure ne babba ba...

Yayin da yake yi masu nasihar ya ha
a gumi akan fuskarsa kamar babu A.c a falon, har lokaci bai zauna ba, yana daga tsaye yana fuskantar su batare da gajiyawa ba, wlh ji sukayi kamar ana wanke damuwar dake a cikin zuciyarsu, ga wani sanyi dake ratsa jikinsu, imam ya karfafa masu gwiwarsu, Ya farfado da jarumtakarsu, aransu har sunji zasu iya fuskantar kowani irin kalubale da zasu fuskantar...

"Kuma ku sani, Nima ina atare daku, zan tayaku ya
i atare zamu cinye jarabawar nan da take tunkaro mu, in sha Allah, zan tsaya maku tsayin daka don ganin baku tozarta a idon duniya ba" ya fa
a yana kara jaddada musu da murmushi akan fuskarshi, wannan maganar da yayi ta faranta ransu, har basu san sa'adda suka saki murmushi akan fuskokinsu ba, kusan atare suka mike tare da nufar shi, atare suka hada baki gurin yi mashi godiya kamar zasu durkusa kasa, sun ma rasa bakin magana, sukace su basu san dame zasu iya biyanshi ba, saboda basu da abun da zasu biyashi da shi Allahne kadai zai iya biyan shi, Bazan iya misalta dadin da imam malik yaji ba, daya bayan daya yabisu ya rungume su a kirjinshi..

Daga bisani Ya umarce su da suje suyi wanka kuma in akwai sallar da basuyi ba toh suyi gaggawar ramata dama so yake ya samu su samu natsuwa sannan yayi masu magnar sallar, babu musu suka amsa mashi da toh..

Gaba dayansu a part din iyayen su mata da ke a cikin gidan Suka shiga, wanda tun bayan rasuwar su, basu daina amfani da shi ba, masu aikin gidan suna shiga su gyara shi akai akai, kullum zaka taras da part din a atsaftace kamar akwai me rayuwa acikin sa, aduk time da suka ji kewar iyayen su mata, idan suka zo gidan a part din suke huce gajiyar su.

Bayan sun yi wanka sukayi sallah, daga bisani suka fito falo, kamar yadda suka bar sheikh Imam haka suka taras da shi, a kewaye da shi suka zazzauna, ya tambayi ina yan aikin gidan suka ce tun jiya suka hana wani daga cikin su shigowa main falo..

Sheikh Imam yace a kira su, don su girka musu abinci, bai kare maganar ba, Prime minister ya tari da numfashin shi da cewa"basai an kirasu ba, daga rana irin ta yau, ko ruwan gidan ba zasu
ara sha ba..."
sauran ma suka goyi bayan maganarsa, sheikh imam bai musa masu ba, sai dai yace shi bazai barsu da yunwa ba, yana ji kamar Allah ne ya kaddara zuwansa gare su don ya taimaka musu don haka suyi hakuri su bar shi yayi aikin shi Yana kwadayin ladar da zai samu ta silar taimakon su da zaiyi.

Badan sunso ba, suka amince masa amma fa bisa sharadin ba zasu ci abincin gidan ba.

A karshe shi ya basu shawarar tunda matayensu suna da restaurant na hadin gwiwa kuma bada dukiyar mahaifinsu suka gina shi ba, halal din su ne, me zai hana su kira manager ayi musu order na kayan abinci da duk wani abu da zasu bukata naci..

Shawarar shi suka
auka, batare da bata lokaci ba, Mai girma sharafuddeen ya dauko wayarsa bayan ya kunnata ya kira hajiya laura, lokacin data daga kiran nashi kuka yaji tanayi tare da tambayarsa meke faruwa ne?

Jiya taga an kawo hajiya saratu asibitin su rai hannun Allah, fuskarta duk ta baci da raunuka garin ya ya hakan ta faru da ita? har su twins ta tambaya suka ce mata hajjaty suke zargin tayi mata haka!

Shin dagaske ne?

Kuma wacece dattijuwar da aka kawo su a tare?

Sannan suna ta kiran layinsa basa samu tun jiya bai dawo villa ba" kamar yar jarida ta tsare shi da tambayoyi ga kukanta daya cika kunnansa.
bai bata amsar tambayarta ba, sai dai ya kwantar mata da hankalinta, yace tayi hakuri su jira shi idan ya dawo villa zaiyi masu bayanin komai, dakyar ya samu ya shawo kanta kafin daga bisani ya bata umarnin tayi musu order na kayan abincin dana sha daga restauranta dinsu akawo masu anan estate dinsu..." maganarsa ta jefa ta a rudani tana kokarin
ara tambayar shi ya katse kiran..

Cikin abunda baifi mintuna ba, Delivery Vans (motocin daukar kaya) biyu suka fara shigowa estate din, masu dauke da tambarin Royal Courtyard Restaurant.
bayan sun tsayar da motocin a parking space, Delivery staffs suka fara fitowa daga cikin motocin kafin suka fara jigilar
auko Containers na kayan abinci da kayan sha daga cikin motar suna kaiwa Cikin Store din gidan..
Chapter 40 · 0% Book details