← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 201

Sashe 54

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan na dawo gidana, na shiga social media na fara bincike akan shafukanka, ta hanyar comment din da mutane su ke yi maka yasa na fahimci irin
wazon dake gare ka, abun da ya fi burgeni yadda mutane suke yabonka da jinjina maka akan gaskiyarka da son adalci, duk wanda zai yi magana akan ka sai ya kurantaka, bayan haka mutane marasa gaskiya suna jin tsoron case dinsu ya shiga hukumarku saboda baku yi masu da sau
Bayan na gama bincike na akan ka, abu
aya da nake tunanin zai yi min wahala shine ta yadda zan tunkare ka, nasan kaitsaye idan na fa
a maka komai ba zaka taba yarda ba tun da kakanka ne mafi soyuwa agare ka, har kulle ni zaka iya yi, shiyasa na yanke shawarar kiran ka asirrance, kafin na yi hakan saida na nemi ilimi akan ta yadda zan yi hakan batare daka bi diddigin layina ba saboda na gano you're a cyber expert..

Lokacin da ya
arasa masa labarin, kwata kwata hankalinsa bai tashi ba, saboda a halin yanzu babu abun da zai
ara bashi mamaki a duniyar nan tun daga kan kakansa..

"Owais, yanzu tun da na fa
a maka komai, pls ka yi
arin yin magana da kakan naka, tun da yana kula ka, ina so ka tambayesa game da malam Jazuli nasan ba zai rasa sanin sa ba, duk da ina ji araina kamar basa a raye, amma duk da haka ka tambayesa,
wara mu san meya faru da su, wlh har yau danginshi nemansu suke yi musamman matar shi.

Jiki asanyaye Chief Owais ya mi
e tsaye, cikin sanyin murya ya ce,
"Baba Imam thank you for sharing everything, na ji dadi, kuma in sha Allah zanyi magana da grandpa, duk yadda muka yi da shi zan sanar maka."
Hugging
in juna suka yi, kafin ya ru
o hannunsa har bakin motar Taj ya rako shi.

Har ya bu
e motar zai shiga sheikh Imam ya ce ya
an jira akwai sa
o da zai bashi, ya amsa mashi da toh.

Cikin sauri Imam ya koma Cikin apartment nasa, jim ka
an ya dawo hannun shi ru
e da date boxes (kwalayen dabino) Ya mi
a ma Owais ya sa hannu ya kar6a,
"Idan ka koma gida, ka ba su Unaisah da Ummi, ka gaishe min da su.."
Tsananin tausayin shi ne ya kama Chief Owais, saboda ya fahimci sa
on na Ummi ne yake son ya bata, amma sai ya fake da sunan su Unaisah kafin nata saboda baya son ya gane komai baisan ya riga da ya sani ba.

"In sha Allah zan kai masu, ina
ara godiya baba Imam, you have done so much for us, we can't repay you, Allah yasaka maka da alkhairinsa..."
Murmushi sheikh Imam yayi masa tare da amsawa da Amin, bayan sun yi sallama ya shige cikin motar tare da kai hannu ya
an dafa kafa
ar Taj dake sharar bacci, firgigit ya farka yana tambayar waye ne..

"Daga yin waya na ji ka shiru baka dawo ba." Murmushi ya yi."Na kira ummu Unaisah ne mun da
e muna waya bayan mun gama kuma bacci yai awon gaba dani, "
arashe maganar tare da tambayar ina sheikh Imam ya ce ai har sun yi sallama da shi ya koma ciki su tafi kawai.

Amsa mashi yayi da toh kafin suka tafi...

Kafin su karaso Taj ya lura da yanayin fuskar chief kwata kwata babu walwala kamar an
ara ninka masa damuwarsa..

"My in-law, meya faru ne?

Na ga kamar babu walwala atare da kai." Yamutsa fuskarsa ya yi ya furta, "Kada ka damu pls.." gya
a kai Taj ya yi tare da kallon date boxes din dake akan laps dinsa bai dai tanka ba....

Can ya tsinkayi muryarsa a kunnansa, "Zaka iya tuna sunan malamin nan da matsafa suka handame shi da
a'yan shi a lokacin da ku ka yi ma su leken asiri?" Ya tambaya yana duban shi..
shiru ya
an yi jim yana kokarin tunanowa.

"Am.. kamar Jazuli ne amma ban ji da kyau ba saboda a lokacin sun yi nesa damu, bamu iya jin me su ke cewa sosai..."
Murmushin takaici Chief yayi jin abun da yake tunani ya tabbata, amsa mashi ya yi da okay, daga haka bai
ara tambayar shi ba, shima kuma bai nemi sanin meyasa ya tambaye shi ba har suka koma gida.
*Welcome, Littafin kurkukun
addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*
3196407426
First bank
Bature Hafsat Muhammad,
*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*~_____
______
_____
_____
______
_____
_____
___~
*daga Alkamin Boss Bature
Bari mu koma baya mu ji meya faru bayan kwana
aya da afkuwar lamarin
Bayan sun koma cikin main falo kowan nan su ya samu wuri saman Sofa ya zauna, yanzu da suka
an samu nutsuwa damuwar su da tunaninsu ya karkata akan halin da Hajiya saratu da momma suke a ciki, sun so da suka fita raka imam daga can su wuce Villa, amma sai basu yi hakan ba saboda akwai bu
atuwar su fara yin nazari akan wani muhimmin abu..

Kafin su fara tattaunawar, Sharafudeen ya zaro waya ya kira layin sarauta, bayan ta
aga kiran muryarta cike da damuwa ta soma tambayar shi.

"Why babe ka barni cikin damuwa, ko bacci ban yi ba jiya saboda rashin kwanciyar hankali, pls ka fada min menene ya faru da hajiya Saratu? how did she get the shards that hurt her face, na tambayi su twins sun ce suma basu sani ba, amma suna zargin fa
a ne ya ha
ata da hajjaty, shin da gaske ne? kuma meyasa ina ta kiran ka baya shiga, baka dawo ba kuma baka fa
amin zaka kwana a gida ba, kodai wani abu ya faru ne?"
"Ki yi hakuri da ban samu
aga kiran ki ba, ban kuma kira na ji a wani hali kuke ciki ba, am really sorry, in sha Allah nan da 30 mins, zamu shigo villa din, and we can discuss then" Ta amsa mashi da toh,
"Ya jikin marasa lafiyan namu?"
"Babe the doctors gave me some information about Sarah's condition since yesterday, they've cleaned and treated her facial lacerations, and she's receiving antibiotics to prevent infection, they assured me she'll feel better in a few days, in sha Allah"
Da yake handsfree ya sanya wayar gaba
aya suna sauraron maganar Sarauta.

"What about Momma?

Ita ya jikinnata?

Is she getting better?"
"Who's Momma?" Ta tambaya saboda bata gane wa yake nufi ba.

"I mean the old lady" Ya amsa mata.

"Oh, she's getting better, according to the doctor's explanation, Her brain injury has caused short-term memory loss, and they can't restore her memory, If she doesn't remember herself."
Da damuwa a fuskarsa ya dubi
an'uwan nasa dake sauraron bayanin sarauta..

"Babe, zan iya sanin wacece? tayi min kama da momma, amma tafi momma tsufa, ba dan momma ta mutu ba da sai in ce ita ce, and One thing puzzled me when I sat next to her she was mentioning Honeyboy and Superstar, who are they?

Bai san sa'adda murmushi ya kubce mashi ba ya
ago suka ha
a ido da prime minister, wanda idanunsa suka cicciko tab da kwalla.

"Nagode da kulawarki agare su, idan na shigo zamu yi magana, Saratu tana magana?"
"Bata farka ba, allurar da su ka yi mata ne bata sake ta ba, amma muna sa ran zata farfado nan bada jimawa ba."
Sallama su ka yi da juna, Ya aje wayar tare da maida hankalinsa akan yan uwansa dake kallonsa.

"Menene mafita?

Bai kamata mu ja baki mu yi shiru ba, batare da mun
auki mataki akan abunda aka yi wa Auta ba"
His excellency Deen ya ce, "Ni so nake insan wani mugunne yayi mata haka?

Meyasa?

Me kuma ya kai ta
akin Hajjaty?"
Abdul Razak ya ce, "Wallahi raina ya 6aci abun ya
ona mini rai, muna a cikin mawuyacin halin nan aka samu wani mara imanin ya zagaya ta baya yaje ya cutar da ita, so yayi ma ya kashe ta badan Allah ya kaddara maids sun je
akin ba har suka gani ai da tuni ta jima da mutuwa."
Chief Owais da sauran matasan dake agurin sunyi shiru suna sauraron su.

Deen ya sake cewa, "Baku zargin fa
a ne ya ha
a ta da hajjatyn har tayi mata bugun kawo wu
Girgiza kai Abdul razak yayi.

"Bana tunanin hajjaty zata iya cutar da Saratu, tsawon shekaru bata ta6a cutar da wanin mu ba, bawai don na yarda da ita ba, ni yanzu na yi hankali, mugu bashi da kama, kowa zai iya rayuwa da kai da fuska biyu na tsawon lokaci yana kyautata maka saboda wata muguwar manufa ta shi, tun da har mahaifinmu ya ci amanar mu balle ita da take bare, kawai abun ya
aure min kai ne na rasa wa zan zarga..." Ya
are maganar fuskarsa a yamutse.

"Zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya, kada mu yi saurin yanke ma hajjaty hukunci saboda ganin hajiya Saratu da aka yi adakinta, ba dole ya kasance ita ne ta cutar da ita ba..."
Sharafuddeen da ya
auko maganar bai kaiga direta ba, Sir mubarak ya dan yi gyaran murya, gaba
aya suka maida dubansu a gare shi, tun da suka fara magana bai saka baki ba sai yanzu.

"Tun
azu da ku ka ga na yi shiru, nazari nake yi akan abubuwan da suka faru abaya, maganar gaskiya bana zargin hajjaty ce ta cutar da auta, sai dai idan Pravin ne ya yi mata hakan.."
an ru
u akan fuskarsu suke kallon shi, sam sun shafa'a sun manta da Pravin basu lura ma babu shi agidan ba.

"Meyasa ka ce haka?" Deen ya tambaya.
Chapter 54 · 0% Book details