← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 201

Sashe 91

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bakasan ranar mutuwarka ba, a wace rana, a wani lokaci?

Don haka mu ji tsoron Allah!

Duk a wannan zaman Taj ya fa
a masu game da sace su Unaisah da Musa ya yi, kuma ya bayyana masu
iyar Shureim ita ce Batool yarinyar nan dake a tare da Unaisah.

Sun shiga damuwa sosai, duk da halin da sheikh Imam ya ke a ciki saida ya taimaka da yi masu nasiha ganin yadda su Benazir suke kuka, ya ce su daina kuka bazai ta6a yi masu maganin damuwarsu ba, in har sun dogara da Allah, kuma sun yi imanin shi kadai ne zai iya nema masu mafita toh su tashi a cikin daren su yi nafilfili In sha Allah babu abun da zai same su, Bi'iznillah...

Sun ji da
in shawarar da Baba Imam ya basu.

Ba tare da 6ata lokaci ba, Taj Ya nuna masu
akunan da zasu shiga su yi alwala..
kafin su gama yin alwalar Taj ya yi ma ma'aikatan gidan magana suka shimfi
a masu prayer mats a nan main falo, darduma ce mai fa
i da tsawo, Ummi ce ta
auko hijabs taba Benazir da Anila.

Sheikh Imam Malik ne ya ja su sallar da kyakkyawar niyyarsu, mazan suna a sahun gaba, yayin da matan su ke a sahun karshe na bayansu gwanin ban sha'awa kamar a masallaci
Yadda suka ga rana haka suka ga dare, nafilfili suka dinga yi batare da gajiyawa ba, har saida kafafunsu suka fara zogi tukunna suka kammala sallar, kowan nan su ya
aga hannayensa sama, Sheikh Imam ya dinga karanto addu'oi cikin harshen larabci suna amsa mashi da Ameen Ameen.

Sun yi ma su Unaisah addu'o'in tsari da kariyar Ubangiji, suka yi ma su Chief addu'o'in nasara da kariya, sun kuma la'anci su Musa da sauran Elders na kurkukun
addara..

Akan kunnuwansu aka fara kiraye kirayen sallar asubahi, nan ma suka kuma mi
ewa su ka yi Salatul fajri.
babu wani mai kwanciyar hankali a cikin su, sun damu sosai, zukatansu sun cika fal da fargaban a wani hali yaransu suke a ciki?

Suna a raye ko ya kashe su?"
Meya faru bayan tafiyar Chief Owais?

Tun a daren ranar ya kira CI ya sanar da shi abunda ke faruwa ya kuma umarce shi da ya tattara Senior Agents dinsu da Isod soldiers dukansu Su bazama neman Alhaji Musa, ya kuma Kira Commender James ya Fada masa akwai matsala, Yana son ganin shi tare da sauran yan team
insa.

Daga bisani ya kira Taj ya ce ya ba Alhaji Ubaid waya yana son yin magana da shi, bayan Taj ya ba Alhaji Ubaid wayar, chief ya yi masa tambayoyi game da wuraren da yasan Alhaji Musa yana yawan zuwa.

Alhaji Ubaid ya bayyana masa guest houses dinsa da location din da suke, Cos yana yawan zuwa da shi wasu lokutta in zai yi baki daga kasar waje.
godiya chief ya yi masa daga bisani su ka yi sallama.

Cikin
anin lokaci jiniyar motocin jami'ai ta kara
e ilahirin birnin Abuja, wiwi wiwi, ga sautin bikes din Isod soldiers dake sintiri kan titituna, duk wani rai da ke bacci saida ta girgiza saboda yadda
arar jiniyar ta cika kunnuwan mutane kamar za'a tada garin, sa
o da lungu na garin da kowani titi ma
il yake da sojoji harma da
an sanda.

Hankulan jama'an gari ya tashi haikam, ganin yadda Jami'ae ke sintiri, Kowa so Yake ya ji meke faruwa?

Musamman
an jarida tun safe suke ta sintiri jami'ai sun hana su yi aikin su, ko kusa da su basu isa su
araso ba.

Ba a ta6a fuskantar tsaro irin na yau ba a garin, kan al'umma ya
aure tamau, ko ina zancen ake yi, wasu ma
an jaridan har sun fara buga labaran
arya suna ya
awa don su karkato hankalin al'umma.

Idan muka koma Isod Headquater, wasu gungun cyber expert ne masu fikra a cikin katafaren Surveillance room din su, na'urorine
an bala'i cike da
akin, Kowani agent ya tasa computer dinsa a gaba sun baza basirar su da
warewar su gurin yin binciken su.

Ta cikin na'urorinsu suna kallon komai dake wakana a cikin garin abuja, sun sanya ido sosai akan motsin komai da ke gudana.

Agent Ethan Kim ne yake jagorantar su, a bisa Umarnin Chief Owais, duk bayan
an mintuna sai ya le
akin ya duba su don ya ga in ana samun cigaba.

Duk bayanin da suka bashi batare da bata lokaci ba yake kiran Dg a waya ya sanar da shi halin da ake a ciki.
~_________________________________
Shin Meke Faruwa A gidan Alhaji Musa
Sakamakon jiniyar da ta kara
e cikin gidan ne ya yi silar farkawar wadanda ke bacci.

Da gudu Zeenatu ta fito daga bedroom dinta hannayenta rungume da pillow, hada duvet
inta da ya nanna
e jikinta, tsabar rudu ne yasa ta rikice ta rasa ina zata dosa.

"Mommy!

Daddy!

Ya Shureim!

Aunty Benazir!

Mommy Layla!

Uncle! wai kuna ina ne?

Babu mai jina ne?"
Da sauri maids din gidan suka fito daga part dinsu daga gani bacci bai ishe su ba, hankulansu a tashe jin Jiniya.

"Meke faruwa ne?

Su wanene ke shigowa gidan?

Daga Ina nake jin jiniyar nan?

Kai jama'a kamar za'a fasa dodon kunnan mutane?

Wannan
ara haka ta lafiya ce kuwa?"
Maids din ne suke ta suratai...

A lokacin Hajiya Sarah tana a kishingi
e kan gadonta, ta daura kanta saman pillow idanunta suna a lumshe, jiniyar ce ta farkar da ita sai dai har yanzu baccin bai sake ta ba, sam ta kasa tashi saboda kasalar da ta mamaye gabbanta.

"Mom!mommy, where are you?

Mommy, ki tashi ki gani!

Wani abu na faruwa!"
cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Zeenatu dake tunkaro dakin.

Batai aune ba ta ji abu ya fado kanta, a firgice ta zare blue eyes dinta, ta yi zaton wani mugun abunne ashe Zeenatu ce ta fa
o kanta, ta
ameta kamar zata shige cikin ta.

Jikinta sai kerma yake yi hakan ba karamin
aga hankalinta ya yi ba.

"Zeenat!

Meke damunki?

Meke faruwa iye?" Cikin rawar murya take fadin, "Mommy, sojoji a cikin gidan nan, sun zagaye ko'ina, hannayensu ru
e da bindigogi, kuma shugowa za su yi..."
sai da Zeenatu ta yi wannan maganar ta tuna da abun da ya yi silar farkawarta daga bacci.

Jikinta na 6ari ta banbare Zeenatu daga jikinta ta sauko daga kan gadon ta
auko mayafi ta lullu6e sumar kanta.

Fitowa tayi daga dakin da sauri Zeenatu ta biyo bayanta.

Tun kan su karasa suka hango maids din gidan a gaban kofar shigowa falon suna ta le
en waje.

Suna ganinta suka dare tare da bata hanya don ta wuce.

Gaishe da ita su ka yi, bata amsa masu ba ta ce, "Meke faruwa ne?" Ta tambaya tana duban su.

Tani ta ce,"Hajiya wallahi mu kanmu bamu sani ba, muna tsaka da yin bacci jiniya ta farkar da mu!"
Bata
arasa sauraronsu ba, ta le
a waje kaitsaye idanunta suka sauka akan soldiers din da suka kewaye gidan ta ko'ina sune.

Kwata kwata babu securities din da ke tsaron gidan.

Gabanta na fa
uwa ta furta, "Inna lillahi...."!

Zeenatu dake la6e a bayanta sai le
a kai take tana kallon sojojin.

Bari mu koma baya mu ji tayaya akai soldiers suka shigo gidan?

Kuma Ina Security officers din gidan su ke?"
Abun da ya faru jiya bayan barin su Dr shureim gidan, kwatsam Security Officers din dake tsaron gidan suka soma jiyo
arar mashina, aikuwa suka mimmi
e hannayensu ru
e da bindigogi suka kewaye gaban main gate din suna jiran su ga daga ina jiniyar ke fitowa.

Unexpected suka ga bike yana
arin Shugowa ciki, Officer din da ya yi kokarin tare mashin din, buge shi ya yi ya fadi gefe
aya, hankali a tashe sauran officers din suka saita jami'in dake akan bike din da guns, sun yi tunanin farmaki suka kawo masu.

Basu kaiga harba bindigar ba, mai mashin
in ya
aga hannayensa sama alamar yayi surrender, "Ku dakata!

Ba dan fashi bane, jami'i ne daga hukumar Isod!"
"Wata shaida gare ka?

Me Kuma ya kawo ka?"
aya daga cikin security officer
inne ya tambaya Yana tunkararsa da bindiga.

Zura hannunsa ya yi cikin aljihun wandonsa ya zaro Id Card dinsa ya mi
a ma Officer din, Bayan ya kar6a ya dudduba ya tabbatar da gaske agent ne.

"Agent Jabeer Osman." Ya furta tare da kallon shi,
"Ka cire helmet din dake a kanka, muna so mu ga fuskarka." Bai musa ma su ba ya zame helmet din..

Kasantuwar akwai hasken electricity tamkar da rana hakan yasa suka ga fuskarsa dakyau.

"Kaida su wanene kuma meya kawo ku?" Ya jefa mashi tambayar yana binsa da kallon tuhuma.

"Megidan muke nema, idan kuma bayanan mun zo ne don mu yi bincike"
Dariyar rainin wayau officer
in ya yi, "Bawan Allah ko dai 6atan hanya ku ka yi ne?

Baku ga gidan wanene ku ka shugo ba?

Ai baku da hurumun da zaku iya shiga gidan nan idan har megidan bai bada izini ba, don haka tun wuri ina shawartarku da ku koma inda kuka fito idan ba so kuke ku rasa aikin ku ba."
Wata tsawa Agent Jabeer ya kwatsa masa yana huci ya ce, "Kai zan yi ma warning ka shiga taitayinka idan ba so kake ka rasa aikin ka ba, kasan su wanene jami'an isod kuma kasan wanene Dg din mu, bisa umarninsa mu ka zo nan, kuma ba mu zo don muyi jayayya da ku ba, saboda baku ne agaban mu ba, ubangidan ku muke nema, zai fi ku bar doka ta yi aikin ta, idan ba haka ba jikinku ne zai gaya maku."
"Ko kuma ku jikinku ya gaya maku, don na lura kamar kuna da ta6in hankali, kun san wanene Alhaji Musa, a
arkashin ikonsa muke, dole saida umarninsa zaku samu iznin shiga, kuma idan kuka nemi ku wuce gona da iri, hmm, wanda ke a lahira sai ya fi ku jin dadi."
wani tantirin officer ne ya fa
a da muryarsa ta
waya..
Chapter 91 · 0% Book details