← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 201

Sashe 113

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Deeja da ke sauraron su kuwa bushewa ta yi da dariya hada dafe cikin ta, tana fadin, "Allah ya
ara maku, masu kunnan
ashi, maganinku kenan.

Ni dai Allah ya so babu ruwana, bansan anyi ba."
arashe maganar tana yi masu gwalo, haushin ta duk ya cika su kamar su rufe ta da bugu.

Daga bisani Danejo ta soma lallashin su ta ce su yi hakuri ita wasa ta ke yi masu tasan shima Sajeed din ba lallai ya hukunta shi ba.
~________________________________
CSH (Combat Support Hospital)
Katafaren Military Hospital ne masu jinyar majinyatan sojojin da suka samu rauni a gurin ya
i, asibitin ba a cikin garin Abuja ya ke ba, a kusa da sansanin su yake.

Yana da matu
ar tsaro, cikin shi da wajen shi soldiers ne ke tsaron shi, ga na'urorin dake sanya ido ga duk wani mai motsi ciki da wajen asibitin.

Lokacin da Motar Chief Owais ta
araso cikin asibitin, drivern dake driving nasa yana yin parking sojoji suka bude mashi motar ya fito, a hanzarce suka buga
afa tare da sarah ma shi.

Zagayawa ya yi ta bayan motar ya bu
e boot dinta, lokacin da ya
aura idanunsa akan Sajeed da ya du
une a ciki kamar musaki saida ya ji tausayin shi ya kama shi, ganin yadda idanunsa suka yi jawur saboda kukan da ya sha.
o hannunsa ya yi tare da taimaka mashi ya fito daga motar, koda ya ga sojoji ta ko'ina suna sintiri ruke da bindigu a hannunsu sai ya kuma fashewa da wani kukan yana ro
on chief ya yafe masa kada ya hukunta shi bazai
ara ba, ya taimaka ya maida sa gurin
an uwansa.

Wani ba
in soja mummuna mara fara'a dake tsaye a gaban su ya ce, "Sir wannan
an shilan fa?

Karairaya maka shi kake so mu yi ko tsallan kwadi zamu sanya shi?" Da jin wannan maganar, yasa jikin Sajeed ya kama kerma kamar mazari, a tsorace ya la6e bayan Chief Owais ya rurru
esa yana ro
onsa, dariya sosai sojojin suka yi.

Da yasan yadda Chief ke
aunarsu da bai
aga hankalinsa ba, ko sauro baison ya ta6a lafiyarsu balle shi ya hukunta su da hannun shi never.

Ruko hannunsa ya yi suka nufi cikin asibitin yana ta zare idanunsa cike da zullumin Ina Chief Owais zai kai shi.

Duk inda suka gifta military doctors din dake zarya tare da nurses with respect suke sara mashi tare da gaishe da su..

Sajeed dake ta
an kalle kalle idanunsa suka dinga hango masa patient din dake a
akunan da aka kwantar da su, ta glass din jikin
ofofin yake hangosu, wasu ma sai yawon su suke yi a ciki,
an matasan mata da samari irin shi.

A gaban wani medical room suka tsaya da tafiya, wani doc ne ya fito da fara'arsa ya sara ma chief shima ya sara masa bayan sun gaisa.

D.r din har ya bu
e baki zai yi magana ya katse shi tare da kashe mashi ido
aya sannan ya nuna masa Sajeed.

"Me laifi ne!

Baya jin magana, ina so ka shiga da shi cikin dakin, ku cire masa kunnansa daya, sannan ku yanke harshen sa.."
Sajeed ya fasa
ara yana fadin, "Nashiga uku, wayyo Inna lillahi!

Yaya Owais na tuba bazan kara ba, na ro
e ka dan Allah ka yi hakuri, ka yafe min, wlh mutuwa zan yi idan suka cire min harshe na.."
a gigice ya zu6e kan gwiwowinsa ya rurruke kafafun Owais, ya dinga rokonsa yana kuka..

Murtuke fuska Owais ya yi, "Ku yi abun da na ce!

Kar ku saurare shi." Rushewa ya yi da wani kukan,
Docs din suka ce, "An gama sir,"
Da ya ga dagaske suke, jikinsa na bari ya mike tare da watsawa da gudu, sai dai kafin ya fuce, sojojin dake sintiri suka cafkoshi suka dawo da shi gaban Chief Owais, Docs din suka rurruke shi yana turjewa tare da waiwayen Owais da ya kawar da kansa gefe, docs din suka tura shi cikin dakin..

"Ku sake ni, ku kyale ni in tafi, wallahi kada ku ta6a ni.." Bai
arasa maganar ba, sakamakon abun da idanunsa suka nuna mashi wanda yake ganin kamar ba gaskiya ba ne..

Tana a kwance kan medical bed sanye da patient gown, sai sharar baccinta take yi, daga kan table din gefenta kayan marmarine a cikin plate data fara sha ta rage sauran.

Murza idanunsa ya yi da hannayensa don ya ga ko gizau take yi mashi amma still ita ya gani.

Gaba
aya ya ru
e ya rasa gasgata abun da yake gani.

"Kamar twin sister dina?

Ni ka
ai nake ganinta!

Ko mafarki ne..?" Fusge kanshi ya yi daga hannun docs din a rude ya nufi gadon ya
an zauna daga gefe ya
ura idanunshi akan fuskarta.

Jini
aya ba wasa ba, ko a mafarki ya ganta zai shaidata, duk min canzawar da za ta yi, saboda warinsa ce.

A hankali ya
aura yatsunsa dake kerma saman fuskarta, ya
an shafa ta har izuwa kan curly hair
inta, komai nasu iri
aya, jinsi ne ka
ai ya bambanta su.

Muryarsa na rawa ya furta, " GAB.. riella!

Da gaske ke ce?

Ke nake gani?

Ba mafarki nake ba.?"
Sambatunsa ne suka katse mata baccinta, a hankali ta bu
e idanunta, tana
aura su kanshi ta zabura ta mi
e zaune, wani irin tsantsar farin ciki ne ya bayyana akan fuskokinsu.

"My twin Bro!

Kai ne da gaske nake gani a gabana?

Ashe da rabon zamu gana da juna, na yi zaton bazan
ara ganinka a rayuwana ba.."
wata irin ruguma suka yi wa junansu kamar zasu koma mutun daya, a lokaci
aya suka fashe da kukan farin ciki.

"Kasan irin u
ubar dana sha?

Baka ta6a nemana ba, Ka manta da ni!

Ba ka damu ina a raye kona mutu ba, ni kadai nake hauka na akan ka, ganin ka da na yi ya tabbatar min da ka riga ni barin kurkukun
addara.."
cikin kunci ta furta tana kallon shi.

Duk sai ya ji ba dadi, cikin karyayyar murya ya ce, "Ba haka bane, kina a raina, na damu da ke, kamar yadda kike nema na nima haka nake neman ki, ki yi hakuri nasan ban kyauta maki ba, ba yadda zan yi ne..."
Bai
are maganar ba ta daka mashi tsawa, "
arya kake yi Gabriel, na tsani kaina dana damu da kai.

Dama na sani na kashe kaina tuntuni, kalli yadda ka sauya kana cikin kwanciyar hankali, ni ina a can cikin azabar rayuwa, ban taba mantawa da kai ba, in ni ce wallahi bazan iya barin ka ba, koda zan rasa raina ne .."
Kasa
arasa maganar ta yi saboda bakin cikin da ta ji, jikinshi duk ya yi sanyi zuciyarshi ta karaya, yasan sister din nashi da zuciya, sai anyi da gaske zata sauko daga kan dokin zuciya..

"Dan Allah ki daina kuka zanyi maki bayani.." Bai
are maganar ba ta rufe shi da bugu kamar ta samu jaki, ta dunkule hannu ta shiga kai mashi naushi.
saboda yasan bai kyauta mata ba yasa shi kasa dakatar da ita.

Komai dake faruwa akan idanun Chief Owais da Docs din dake a
akin, tsantsar tausayin su ne ya kama su.

"Gabriellah, ki daina bugunsa, i will explain to you..

"
Owais ne ya fa
a, cikin shesshekar kuka ta ce, "Ka barni in ci ubansa, baisona banza shasha, wa nake da shi in bashi ba?

Ni fa
anwarsa ce, twin sister
insa, ciki
aya muka fito, don me zai barni cikin wahala ya tafi?

Kunsan irin cin zarafin da aka yi min?

Wannan mahaukaciyar karyar ta sa giant ya yi raping
ina, ni ka
ai nasan azabar dana sha, mutuwa kadai ne ban yi ba..."
gaba
aya ta labarta musu abun da ya faru da ita, Gabriel ya yi kukan bakin ciki kamar ransa zai fita.

Docs din dake a dakin duk saida idanunsu suka ciko da
walla saboda tausayinta.

Chief Owais ya karaya da jin abun da ya faru da ita.
uwa suka yi su duka suka dinga lallashinta har saida suka samu ta tsagaita da kuka.

Chief Owais ya ce ta yi hakuri, sun san an cutar da rayuwarta amma ta sani Gabriel bada son ranshi ya tafi ya barta ba, bashi da mafita ne saboda ba a guri
aya suke ba, bayan haka sune silar da har suka san labarin kurkukun
addara, da labarin ita kanta, saboda Sajeed shine ya dinga yi masa maganar
ar uwarsa dake a kurkukun kaddara akan ya taimaka ya
aukko ma shi ita, bayan haka mahaukaciyar karyar da take magana akanta ta riga da ta mutu tun ranar da suka kai farmaki!

Maganganun Chief Owais sun yi tasiri a cikin zuciyarta, jikinta ya yi sanyi har ta nemi yafiyar Gabriel akan fa
an da ta yi masa ya ce mata kada ta damu komai ta yi shi baiga laifinta ba, shi yakamata ya nemi yafiyarta, ta ce ta yafe masa amma kar ya
ara tafiya ya barta, ya yi murmushi ya ce bazai
ara maimaita wannan kuskuran ba, hugging din juna suka
ara yi cike da farinciki.

Daga bisani Sajeed ya dubi Chief Owais da hawaye akan fuskarsa ya ce shi baisan tayaya zai gode masa ba, yau ya shammace shi, ya yi mashi surprise din da bai ta6a zato ba, da farko ya yi zaton hukunta shi zai yi, ashe yar uwarsa zai nuna masa, ya ce, " Chief kai wani irin mutunne mai kyakkyawar zuciya?

Na yi imanin zuciyarka ta daban ce, samun irin ka zai yi wuya a duniyar nan.

Ka kyautata mana a rayuwa, ka yi mana abun da baza mu ta6a mantawa da kai ba, Allah ne kadai zai iya biyan ka..."
Yayin da Sajeed ke furta masa kalmomin nan murmushi ne dauke akan fuskarsa.

Itama Gabriella ta yi masa godiya, ya ce su godewa Allah, saboda shine ya kaddara zai zama silar taimakon su.
Chapter 113 · 0% Book details