← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 201

Sashe 136

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tukunna a hankali ya
an dinga satar kallon fuskokin su
aya bayan daya tun daga kan ya'yan shi ya fara, har izuwa kan jikokinsa, akan fuskar kowan nan su ya karancin halin da suke a ciki, bai taba jin kunyar kansa irin na yau ba, jikinsa yadinga kerma kamar mazari, kukan saratu Ya cika kunnansa akan idon shi yaga Sir mubarak da Sharafudeen sun nufi daki da ita, tana ta kiran sunan shi tana fada masa ya 6ace kada ya bari su tafi da shi, a karshe ma hada zagi tadinga hada masa baba tana cewa ya 6ace, wallahi in ka bari suka tafi dakai Allah ya isa ban ya fe maka ba.

Bai
ara tabbatar da raunin mace da tausayinta ba sai yau, Duk irin abun da yayi wa saratu ya aura mata mijin da shi yasan ba son ta ya ke yi ba, Ya kuma gur6ata shi, amma ahaka take nema ta cece shi saboda bata son ataba lafiyarsa.

A daki suka sanya saratu, tare da twins din ta, suka umarce su da su zauna tare da ita, gudun kada ta lahanta kanta, daga bisani su ka kulle dakin, ta yadda ba zata iya fitowa ba.

Tadinga bubbuga kofar, twins suna rurruketa tana bangaje su, su fadi ahaka zasu mike su cigaba da ru
e ta.

Babu wanda ya
ara furta kalma, tun bayan da suka ambaci sunan shi.

Ko handcuff agents din basu sanya ma shi ba, saboda nauyin yin hakan agaban Dg sukeji.

Lokacin da ya ke tafiya agents din na biye da shi, yayin da yake kallon kowa dake a kewaye da shi, karaf idanunsa suka sauka akan Jazz dake ta kuka kamar ransa zai fita, mommynsa turai ta rungume kansa a kirjinta, ita ta hana ya motsa da ba abun da zai hana yayi irin haukan da saratu ta yi, saboda kaunar da ya ke ma baba Obie, bakomai ne ya fado masa aranshi ba face maganganun da suka ta6a shi da baba Obie.
_baba, Bana jin da
in yadda wasu suke guduna saboda rashin asalina, meyasa sauran mutane ba kamar kai da daddy mubarak suke ba_
_Na tsani kaina baba, Rashin asalina Yana neman Yaja min na rasa abunda nakeso, kowa ya bu
i baki sai yace ni
an mai aikine bani da asali, Har shege ake kirana baba_
_Kamar yadda nasaba fadamaka,Yau ma zan maimaita maka, Ni dai inason family
inka, Ina alfahari daku, nayi fatan ace nima ina
aya daga cikin jikokin ka sai dai Allah bai nufa_
A cikin ransa yake tariyo komai yayin da yake kallon Jazz, at same time jazz daya ga irin kallon da baba obie yake masa shima saiya tuna da ranar da sukayi maganar..
_ Toh toh ya isa ka yi shiru, Bana son Kana sanya damuwa aranka, Kukan Ya isa haka, kowani
an adam da ka gani a duniyar nan da irin tashi
addarar, babu wanda Allah baya jarabta, inaso ka rungumi wannan amatsayin
addararka, Kada ka ta6a bari wani Yasa ka canza tunaninka, Allah Shi yake son ganin rayuwarka haka, Kuma shine zai nema maka mafita"
_Jazz baka
auke ni kamar yadda na dauke ka ba, ko da yake ba laifinka bane, laifin wadanda suke yi maka gorine, sune sukasa kake jin kanka bare afamily dina, amma inaso kasani, baba obie baya yi maka kallon bare, inasonka jazz kamar yadda nakeson jikokina, Kamar yadda kake fatan ka zama daya daga zuri'ata nima haka nake fatan ka kasance_
Fashe wa ya kuma yi da wani kukan Aransa ya shiga furta inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un!

Baba meyasa ka kasance azzalumi? baba me yaja maka?

Meyasa ka sauya daga yadda nasanka?

Ka karya zuciyata baba..."
Aransa yayi maganar, adaidai lokacin baba obie ya
auke idanunsa da daga kan Jazz, ya dan girgiza kan shi, hawaye na sauka kan kuncinsa..

Sau
aya ya ha
a idanunsa dana Momma ya yi saurin kawar da su gefe cike da jin kunyar ta data kamashi, itama ta zubda kwalla kamar ruwan hawayen ta za su
are.

Bayan da suka fito gaba
ayan su, Chief Owais ya bu
e mashi backseat na Motar shi..

Bai kaiga shiga ba, Sai ga Mota ta kunno kai cikin estate din kaitsaye ta nufo gurinsu da matsakaicin gudu tana gab da zata karaso gudunta ya ragu slowly tayi parking a gefen su.

Gaba
aya suka
ura idanunsu akan Motar suna jiran ganin wanene zai fito.

Amininsa ne Jan kunne Ya fito daga motar, fuskarsa jaga jaga da hawaye, kayan jikinsa sun yi squeezing kamar mahaukaci, ko takalma babu a kafarsa.

Tsantsar tashin hankali da damuwa ne akan fuskarsa.

Sunyi mamakin ganin shi, bayan yasan neman shi akeyi don a kama shi, Owais ne ka
ai yasan da maganar zuwan shi, saboda tuntuni baba Obie ya fa
a masa ya ce zai mika wuya saboda baba Obie kuma ya cika alkawarinsa ya kawo kan shi, don a hukunta su a tare..

Gaba
aya haushin shi da tsanar shi su ke ji, gani suke kamar shine ya jefa mahaifinsu a halin da ya ke a ciki, Ko arzikin kallon mutunci bai samu agurin su ba, kwata kwata baya a cikin nutsuwar shi, kamar ya fara samun tabin hankali.
tun da ya fito bai nufi kowa ba sai baba Obie, Bai kaiga karasowa ba, Ya'yan baba Obie Suka kare ubansu cikin fushi suka daka mashi tsawa, su ka ce babu shi babu ubansu, tsakanin su sai dai hange daga nesa, amma ya gama kusantar inda mahaifin su ya ke.

Baba Obie Yana kallon aminin nasa da ke ta ambaton sunan shi yana ro
on su akan su bar shi ya gana da amininsa shi ka
aine zai iya kwantar masa da hankali.

Baba Obie yaso su barshi suyi magana amma suka ki basu dama.

Akan idon shi, agents suka sanya mashi handcuff a hannayenshi, suka tura shi cikin motar su.

Owais Yace ya shiga daga ciki, cikin sanyi jiki ya shiga ya zauna, ya rufe masa cardoor din.

Ta gilashin motar yake ta kallon ya'yansa da jikokinsa dake ta kuka kamar ransu zai fita.

Chief owais da kan shi yayi driving din baba Obie.

Duk suna atsaitsaye motocin suka fuce daga Obie estate, gaba da bayan su motocin sojoji ne dana yan sanda saboda su ba su tsaro..

Lokacin da ya ke yin driving dinsa yana satar kallonsa ta mirror, zuciyarsa ta karaya da ganin yadda baba Obie ke ta kuka hada magina a hancin sa.

Cikin shesshekar murya yaji yana fadin kaicona, na zalunce kaina, na zalunci ya'yana da jikokina, na zubda mutuncina, na kashe rayuwar ya'yana da kaina, na kashe rayuwata, bani da hankali, dabbane ni, bazan taba yafewa kaina ba
ya dinga zagin kansa yana aibata kansa.

Kasa magana Owais yayi saboda baida abun da zai iya furta masa, amma daya tuna taimakon da yayi masu sai yaji zai iya masa wani abu.

"Baba bani da abun da zan iyayi maka, ka riga da katabka babban kuskure, shawara
aya da zan baka shine, Ka tuba ka musulunta ka komama Allah kafin mutuwarka, ko dan ka samu sassauci" ya fa
a ne kawai don ya kwantar masa da hankali amma shi kanshi yasan ina!

"Owais, Allah ba zai ta6a kar6ar tubana ba, koda na kar6i musulunci, babu abun da zai sauya Owais, ayyukana gaba daya irin na yan wuta ne, tun a duniya owais nasan menene makoma ta, duk wanda ya aikata mai kyau ya sani owais, na aika zunubbai masu yawa munana, hakkin rayukan dake akaina basu kirguwa, ina jin kunyar mahaliccina, ina jin fargaban ranar da zan farka in ganni a cikin
abarina daga ni sai mugun halina Owais, wallahi na kasa kashe kaina ne saboda tsoron abun da zan taras a cikin
abarina, wallahi na zalunci kaina saboda neman duniyar da zamu mutu mu barta, gayanan naja ma kaina da ahlina.
maganganunsa sun jefa chief owais a hali na damuwa.

"Duk da haka baba, ka musulunta in har dagaske ka tuba, kuma ka ji tsoron ha
uwarka da Allah, bansan hukuncin da kotu zata yanke maku ba, amma nasan zaku yi zaman gidan yari, kaga in hasashe na ya tabbata zaku samu sauran lokacin da yarage maku a duniya, hakan na nufin kana da sauran damar da za kayi ta yin istigfari",
Girgiza kai yayi cikin kunci yace"owais, koda Allah zai yafe ma kowa zunubinsa banda irin mu, fir'auna ma daya nemi ya musulunta kasa karasa furta shahada yayi ruwa ya ha
e da shi, dafa hankalin mu mun sani muka take sani Owais.."
"Baba Ka fahimta, kai ba musulmi bane, atlease in ka musulunta da imani a zuciyarka ko yayane zaka iya samun sassauci.."
magiya owais yadinga yi masa yana driving a hankali saboda baison suyi saurin karasawa Headquarter din su, sarai baba Obie Ya lura da yadda ya ke yin driving din ya kuma fahimci dalilin dayasa ya ke yin hakan.

"Owais, zanyi tunani akan maganar ka.."
"Baba baka da lokaci daya wuce wannan!

Dama ce agareka, daga jibi zamu shiga kotu za'a yanke maku hukunci, ba lallai mu sake haduwa ba, musuluntar da zakayi ita zata bamu kwarin gwiwar yi maka addu'a ko bayan ba ranka.."
maganar Owais ta kayar masa da gaba.

Duk yadda yaso ya shawo kanshi abun ya gagara, ya fahimci yana son ya musulunta sai dai yana jin fargaban koya musulunta Allah bazai kar6i tubansa ba, kawai ya cire rai ne da komai.

Har suka
araso Headquarter din baba Obie bai kar6i tayin Owais ba.
da shi da amininsa agents suka tasa su agaba Owais Yana a ruke da hannun kakansa Ya kasa sakinsa yana ta nanata masa kalmatusshahada don ya kar6a amma ya
i ya furta abakin sa.

Gaba
aya Isod agents din dake a head quarter din da sojojin tun shigowar su, suka cire hulunansu tare da sadda kansu
asa, alama ce ta nuna girmamawa ga kakan dg.
Chapter 136 · 0% Book details