← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 201

Sashe 55

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Abun da yasa nake zargin pravin, Idan ba zaku manta ba aranar dinner din Hateem, Pravin ya yi wani abu da ya ja hankulan mutanan dake agurin, a bainar jama'a ya dam
i hannun Hajjaty ya tursasa mata akan tabar hall din, tun anan na sanya masu alamar tambaya..."
Da yayi wannan maganar nan take suka tunano lokacin da abun ya faru babu wanda bai zargi akwai boyayyiyar alaka a tsakaninsu ba, a lokacin har mataki suka ce zasu
auka akan shi, amma daga bisani suka yi watsi da maganar.

Sir mubarak ya
aura da cewa, "May be sun da
e suna kulla makirci a bayan idon mu, bayan haka komi ya faru da Saratu baba ne ya ja mata, lokacin da ta zo da shi daga
asar India ta nuna shi take so ta aura gaba
ayan mu babu wanda ya amince saboda bai kwanta mana a rai ba, saida muka musa akan mu bamu yarda Saratu ta auri bare wanda ba jinsin mu ba, mutumin da ko asali baida shi, ba mu san kowa nashi ba in ba ita
ar uwar ta shi ba da ya zo da ita daga baya, amma Saratu ta
i sauraron mu saboda baba ya goya mata bayan ta auri za6in ranta" ya fa
a ransa a matu
ar 6ace.

"Bayan haka ina zargin baba shine ya janyo pravin cikin harkar tsafinsa, watakil sunyi yarjejeniyar zai bashi auranta idan ya amince zai yi masa abun da yake so shi kuma da ya ke dama kwa
ayin dukiyar Saratu ce ta ru
e sa shiyasa ya biyo ta don ya kwashi rabon shi, shine ya amince zai masa biyayya..."
Maganar Sir Mubarak ta
aga hankulansu saboda suma sun hasaso abun da ya ke zargin.

Hateem ya ce, "In kuwa hakane Baba ya zalunci Saratu, ni dama na yi mamakin yadda ya yi saurin amince ma auranta da shi, saboda kwata kwata ba ajinta bane, a matsayinsa na mutun mai girmama darajarsa da
imarsa amma ya rufe ido ya nace akan abar Saratu ta auri za6in ta, abun ya tsaya min araina, a lokacin har kwatanta masa muka yi ya rufa mana asiri kada ya zubar mana da mutuncinmu Saratu ta fi karfin Pravin, ba sa'an aurenta bane, mutane zasu yi mana surutu amma duk bai duba wannan ba, thats mean dama can da wata a
asa a tsakanin su..."
Chief Owais dake sauraronsu zuciyarshi ta zo wuya saboda tsabar 6acin rai da tsanar hali irin na grandpa dinsa da kuma haushin Pravin.

Jikinsu Ziyad ya yi sanyi lakwas, jin abun suke kamar a mafarki saboda al'ajabi.

"Lokacin da momma ta fara tona masu asiri, munafukin batare da sanin mu ba ya zame jiki ya fuce daga falon, ina tunanin a lokacin da zai gudu Auta ta gan shi, shine ta bishi don ta tuhume shi akan abunda momma ta fa
a, watakil ta riske shi a
akin hajjaty suna kokarin guduwa shine su ka yi mata haka don kada ta tona masu asirin abun da suke kokarin yi..."
Da ru
u akan fuskokin su suke kallon shi, gaba daya sun yarda da maganar shi.

"Mayaudaran banza, na dade banga mugun miji irin pravin ba, tsawon shekara da shekaru yana auran Saratu ashe bada zuciya
aya yake tare da ita ba, ni takaici na
a'yan dake atsakanin su, ya za su ji idan su ka ji mugun halin uban su?

Da kuma abun da ya aikata, dama ya lafiyar gwiwa!

Suma ba hankaline ya ishe su ba, uban nasu ya 6ata su, badan mun tsaya masu tsayin daka ba akan tarbiyarsu, da Allah kadai yasan lalacewar da zasu yi...." Senate Lateef ne ya fa
a cikin fushi.

"Kuma wallahi na rantse da wanda raina yake a hannunsa,
aya daga cikinsu ba zai sha ba, ko da zasu gudu daga
asar nan ne su tafi birnin sin saina sa an kamo min su an dawo dasu nan, dole su gir6i abun da suka shuka..."
Ya fa
a tare da kai hannu ya daki hand sofa.

"Dole Saratu ta shiga mawuyacin hali, nafi jin tausayinta, ba ta yi dacen uba ba, ba kuma ta yi dacen miji ba.." a cewar Deen
"Owais, su wanene sauran Elders din?" Ajiyar zuciya ya
an sauke tare da duban daddyn nasa, "Elders goma sha biyu ne, shidda suna jagorantar kurkukun
addara, sauran shiddan ba a
asar nan suke da zama ba, mutun hu
u da momma ta fada su ka
ai muka sani a cikin su, amma akwai mutun biyu da muke zargin suma elders ne, anan Abuja suke da zama, nan bada jimawa ba zamu kammala bincike akan su, na tambayi baba amma ya ki ya sanar da ni..."
ya fa
a cikin raunannan murya.

Har suna ha
a baki gurin furta, "ka yi magana da baba?

Yaushe?"
Numfasawa yayi kafin ya zayyana masu komai da suka tattauna tare da baba Obie.

Gaba
aya basu ji dadin
in fa
a masan da bai yi ba, duk da sun riga da sun san halin uban nasu, duk da mugun halinsa yana da amana da kuma rukon alkawari, tun da har ya
i sanar da shi to kuwa bazai ta6a fa
a ba.

Kwantar masa da hankali su ka yi, su ka ce kada ya damu tun da har ya ce ya nemi taimakon Allah, toh ya dage da addu'a suma zasu taya shi da addu'a, kada ya kuskura ya bari maganar baban ta sagar ma shi da gwiwa, in sha Allah babu abun da zai gagare shi, su basu ma so ya nemi taimakon sa ba, da ya yi shawara da su da ba zasu bari ba, saboda haushin shi da suke ji, kuma suna so ya sani a yanzu binciken bana hukumarsu bane ka
ai suma sun shiga ciki, zasu taya shi fa
an har zuwa lokacin da zasu kawo
arshen su, sannan komai ake ciki ya sanar da su, zasu taimaka mashi da iyakar iyawarsu, su kuma wadanda momma ta fadi sunayen su a cikin elders din za su yi kokarin kama su don ba zasu bari a ci gaba da aikata fasadi a doron kasa ba...."
Maganganunsu sun karfafa zuciyar Chief, musamman da suka bashi shawarwarin da zasu amfane shi akan binciken shi, sun bashi goyan bayansu dari bisa dari, prime minister ya ce zai
ara mashi da Canadian Police, Sir mubarak ma ya ce zai bada gudummuwar sojoji, kwata kwata basu yi magana akan inmates ba, ba don basu damu da su ba, sai don sun fi so su fara kawo karshen elders amma abun yana aran su, suna son suga duka inmates watakil su samu sauran yaransu da ke a raye
Har maganar Jan kunne suka yi sir Mubarak ya ce, "Abun haushi abun takaici wai aure! haba ni dama abun na daure min kai, amintarsu ta jima tana burgeni, basu taba samun sabani ba, basu gajiya da ziyartar juna, musamman shi jan kunnan, ashe akwai wata a
asa, wama yasan me suke aikatawa idan suka shige
aki, bamu taba kawo komai a ranmu ba, saboda yardar da mu ka yi da su, munafuki shiyasa ya
i ajiye iyali ashe yasan me ya taka, wato uban namu ne iyalinsa ko..."
Maganar shi ta so basu dariya ba don halin da suke a ciki ba.

Lokacin da marece ya kunno kai, gaba daya suka shirya tafiya Villa, Chief ne kadai bai bi su ba saboda ya damu da ya dawo gidansa, a cikin motocin security details din Sharafuddeen su ka tafi, ba zan iya misalta maku haduwar presidential resident ba, abun sai wanda ya gani.

Daya bayan daya motocin suka shiga cikin Villa, da matsakaicin gudu suka nufi presidencial medical center, a gaban hospital din suka yi parking, a hanzarce security officers din dake tsaron asibitin suka yi hanzarin karasowa tare da bu
e masu cardoors din, suna fitowa suka fara sara masu..

Cikin sauri suka shiga cikin katafaren asibitin duk inda suka gifta jiki na 6ari hospital staff suke gaishe da su with respect kamar zasu durkusa kasa, wasu daga cikin staffs din ne suka yi masu jagora zuwa Private room din da aka kwantar da Momma, suna shiga ciki idanunsu suka sauka akanta tana a kwance saman medical bed sanye da patient uniform, wuyan hannunta na dama asanye yake da canula, da alama tayi nisa a cikin baccinta, hankalinsu ba karamin kwanciya ya yi ba ganin yadda take bacci cikin kwanciyar hankali, daga gani tana samun kyakkyawar kulawa.

Docs din dake kula da ita ne suka shigo dakin jin zuwan Mr president da yan uwansa bayan sun gaisa da su, suka fara kora masu jawabi game da cigaban da suke samu akan lafiyarta, bayan sun gama sauraronsu suka yi masu godiya bisa ga kokarinsu, kafin su bar dakin momma saida suka je har gaban gadonta suka kura mata ido kamar za su ha
iye ta musamman Hateem da Sharafuddeen wani irin kaunar mahaifiyarsu ne ya
ara shigarsu ba dan basu son su katse mata baccinta ba da ba abun da zai hana su tada ta, a hankali suka ruko hannayenta kowan nan su ya manna mata kiss, hatta su Sir mubarak saida suka sumbaci hannunta, kafin daga bisani suka bar dakin nata.

Docs su ka yi masu jagora zuwa private room din da aka kwantar da hajiya Saratu suna shiga ciki suka taras da su twins a zazzaune kan kujerun dake agaban gadon, jiya izuwa yau har yar rama suka yi, idanunsu sun kumbura sunyi jajur daga gani sun sha kuka, suna jin takun tafiyarsu suka mike da sauri suka nufe su, cikin sauri suka rungumesu, wani sabon kukan suka kuma fashewa da shi, lallashin su suka dinga yi, cikin shesshekar kuka Zaid ya ke tambayarsu ina dadynsu?

Me yasa bai zo ya duba halin da mommynsu take a ciki ba?

Ko har yanzu bai dawo gidan bane?

Tun jiya suke kiran wayarsa a kashe.." Zayn dake ta cizon le6ensa saboda zuciya cikin bacin rai ya ce, "Uncles ku fada mana meke faruwa ne? and Where's Hajjaty?

Did she return home or run away?
Chapter 55 · 0% Book details