← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 201

Sashe 149

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abun ka ga rainon turai, da ta ji ya kwanta mata arai nan take ta kar6i tayin soyayyar shi, tun kafin a tashi daga walimar suka ke6e a garden su biyu suka sha soyayyar su, har bayan da suka koma gidajen su basu rabu da juna ba, chatting suka ci gaba da yi, tun daga wannan ranar ne sha
uwa mai
arfi ta shiga tsakanin su, sai da ta kai ga Mahboob ne ke zuwa gidansu ya
auke ta ya kaita school idan an tada su ya je ya
auko ta, Hajiya Sarah tasan da komai, kuma ta ji da
in kulawar da yake ba Zeenatu, saboda shi yasa yanzu bata zama da damuwa a ranta.

Daga bisani Zayn Ya auri Zahra bayan kammaluwar bikin su, Anan gidan sa na cikin Imam Estate suke da zama, yayin da Zaid ya ke jiran Sajeeda ta kammala karatu kamar yadda ta nemi alfarma a gurinsa na cewa ya bari ta gama karatu sai su yi aure, Shi ma Mahboob Zeenatu ya ke jira ta kammala karatu kafin su yi aure.
___________________________________
Taj bai manta da alkawarin da yayi akan Zai raka Danejo takai ziyara gurin yan uwanta fulanin Daji, bayan da suka samu kwanciyar hankali, a rana
aya suka shirya da shi da Unaisah da mommyn ta, tare da Danejo da kuma rakiyar Isod Soldiers wanda Owais ne ya Umarce su da su basu kariya saboda yaji Daji ne in da zasu je, bayan sun isa Dajin danejo bata manta da inda rigarsu take ba, ita ta jagorance su can cikin dajin har inda rigar ta ke, Ba zato ba tsammani Yan uwanta suka ganta tare da mijin ta da iyalinsa, tsantsar Al'ajabi ne ya kama su, nan take suka fashe da kukan farin ciki, itama ta kama kukan murnar ganin yan uwanta, bayin Allah basu ta6a tsammanin za su sa ke ha
uwa da Danejo ba, tun bayan da suka ba Taj amanarta ya tafi da ita, damuwa da zullumin awani hali take a ciki ya cika zukatansu, basu ta6a mantawa da ita ba, a lokacin har sun fidda rai da ita, duk in su ka tuna da ita sai sun yi danasanin
aukar
ar su marainiya su ka ba bare, amma zuwan da Taj ya yi da Danejo Ya faranta ran su, sunyi farin ciki mara misaltuwa, sun
ara jin kaunarsa ganin yadda ya ruke amanar
ar su, sun kuma yi mamakin ganin Angel,
ar yarinyar da suka sani tun tana da shekara sha
aya sai gata sun ganta ta girma ta zama budurwa, itama Unaisah tayi farin cikin ganin su, musamman Hasiya Yar uwar Danejo.

Benazir ta yi masu godiya sosai akan taimakon da Sukayi ma Yar ta Unaisah, gaba daya sunji dadin karramawar da sukayi masu, sati
aya sukayi A rugar, Lokacin da zasu dawo Taj Ya ro
i alfarmar da su biyo su su dawo birni cikin mutane da zama, har ya yi masu al
awarin zai taimaka masu da muhallin da zasu zauna, da farko sun nuna
in amincewar su saboda sun saba da rayuwar daji tun kaka da kakanni, amma da Danejo ta lallashe su ta kuma basu labarin rayuwar birni da kuma ababen more rayuwa sai suka amince da zasu biyo su, dama kuma suna cikin matsin talauci tun bayan da su ka rasa shanayensu da 6arayi su ka sace.

Taj da Benazir sunji dadin amincewar su saboda suna son su saka masu da halaccin da su ka yi wa Unaisah, bayan da suka baro rigar, kaitsaye suka nufi Jihar Joss, already Ya gyara gidansa na Joss da niyar duk in zasu kawo ziyara sai su sauka anan, Gaba daya Ya mallaka ma Dangin Danejo gidan, da ya ke basu da yawa ya ishe su har ya yi masu yawa, Unaisah ta basu kyautar Kaso mafi tsoka a cikin kudin da kotu ta raba masu na Elders, yayin da Benazir ta
ara masu da kyautar Ku
in da zasuja jarin sana'a, ga kuma kudin da Owais ya bada abasu kimanin miliyan goma.
suka dinga yin kukan farin ciki suna yi masu godiya, kafin tafiyar Taj da iyalinsa sai da suka rakasu kasuwa suka yi siyayyar dabbobin da zasu kiwata, a bayan gidan suka hada garken Dabbobin su, inda zasu cigaba da kiwon su, ga kuma sana'ar siyar da fura da nono da za su farayi, Taj ne Ya ha
a su da abokinsa Muhsin bayan daya nemi taimakonsa Akan ya dinga taimaka masu har su samu wayewa tun da shi anan joss ya ke da zama tare da family dinsa, Muhsin yaji dadin alfarmar da Taj ya nema agurinsa saboda shima yana Neman hanyar da zai saka mashi alkhairin da yayi masa.
bayan Taj da iyalinsa sun koma Abuja, Muhsin da danginsa ne suka cigaba da kula da dangin Danejo, suna taimaka masu ta fannin wayar masu da kai game da rayuwar birni da kuma mu'amala da jama'a, sun kuma taimaka masu gurin neman ilmin addini dana zamani.
*FLASH BACK
bari mu koma baya muji shin wanene Mahaifin Prisoner Chinonso wanda muka fi sani da Majnoon, Unaisah ce ta gano wanda ya sadaukar da shi saboda ta
wallafa rai akan son sanin wani mugunne ya sadaukar da
aramin yaro mai ta6in hankali har yayi silar mutuwar shi? saboda bata manta da shi ba, yana aranta, har Yau har gobe bata daina yi masu addu'a ba shi da Unaizah, da sauran yan uwansu prisoners wadanda suka rigamu gidan gaskiya, tun kafin ayi shari'ar Elders, ta ta6a jin labarin kundin rijistar fursinoni a gurin Owais shi ne ya fada mata yadda suka samu kundin ya kuma fayyace mata abun daya
unsa, ko da taji haka nan ta ro
e shi daya taimaka Ya dubo mata wanene ya sadaukar da Majnoon dinsu a cikin littafin rijistar fursinoni, bai tambayeta dalili ba, bayan daya kawo mata littafin, a gaban ta Ya bu
e shafin prisoners din da aka sadaukar Na sashen su a kurkukun, suna tsaka da dubawa nan take suka gano sunan Chinonso, da wanda Ya sadaukar dashi, bakowa bane face aminin baba Obie, Jan kunne, Chinonso yana daya daga cikin ya'yan sa daya sadaukar a gidan kurkukun kaddara, gaba daya ma ya'yan da yake sadaukarwa bata hanyar aure yake samun su ba, Majority dinsu tsohuwa zafreen ce ta ke haifa mashi su, a tare suke sadaukar da jinin su gidan kurkukun, Unaisah batayi mamakin jin sunan wadanda suka sadaukar da shi ba saboda tasan Tsohuwa Zafreen takuma san kafurar zuciyarta, daga bisani tayima Chief Owais godiya daya taimaka mata gurin gano abun da ta ke nema
__________
TURAI_____,
Shin wacece Harriet (khadija) Mahifiyar Dr Jazz ?

Menene asalin su?

Me kuma yasa ta baro
asarta England da danta tazo Nigeria?

Tayaya kuma akai ta samu aikatau a obie estate?

Harriet Baturiya ce ta usili, Yar asalin London ce babban birnin kasar England , ta taso a hannun Mari
inta, kawunta kanin mahaifin ta, wanda tun bayan rasuwar iyayenta ya
auke ta ya dawo da ita gidan shi, Yana da mata daya tare da
ansa Abraham wanda ya haifa tare da mariganya matar shi ta farko, kawunta ne ya rike ta tun daga
uriciya har ta girma ta zama budurwa, bayan data mallaki hankalinta, ta kammala karatunta, ya ha
a ta aure da
an su, wanda sun da
e suna son Juna tun da kuruciya, bayan data samu cikin shi wata tara cuf ta haifi danta mai suna Eric wanda muka fi sani da Jazz, daddynsa Yana mutuwar son shi kamar ranshi, arayuwar Turai bata da matsalar daya wuce Matar Uncle dinta wato step mother din mijin ta Beatrice, Beatrice bata da mutunci ko ka
an, ta
aura mata karan tsana tun lokacin da Mijinta Ya kawota gidan, bata son ta, bata kula da ita, kullum cikin
yarar ta ta ke yi, idan ya kasance su biyu ne a gida har wankin bango take sanyata, ta dinga yi mata barazana akan zata kashe ta.
haka lokacin da Uncle dinta ya hadata aure da dan uwanta, Beatrice ta nuna
in amincewarta, saboda bata son idan Abraham Ya mutu ta gaji dukiyar shi, shiyasa tun farko taso ta hada shi aure da diyar kanwarta, amma ya bijire akan baison ta turai yake so, bada son ranta ba Abraham Ya auri harriet sai don saboda Ubansa Ya matsa akan saiya hada Yar dan uwansa da dansa aure saboda baya son bare Ya aureta, kuma ya fahimci son juna su ke yi, bayan auransu Ta
ara tsanar turai babban bakin cikinta, Arzi
in Abraham da yake yana da dukiyar daya gada agurin mommynsa, tasan muddin Ya mutu turai ce zata gaje shi tare da danta, ita kuma batason hakan ya faru, gani take kamar ma Turai badan Allah ta aure shi ba, sai don saboda dukiyar shi, gaba daya ta hana rayuwarta sukuni, gashi ta kasa fa
ama kowa game da
untatawar da ta ke yi mata da ya ke a gida daya suke rayuwa kowa da part din sa, ta hana ta sukuni agidan Mijinta, karshe ma ta fara shiga tsakaninta da mijinta, ta dinga kulla mata makirci duk don ta rabasu amma Allah bai nufa ba, saboda daddyn Jazz yana yi mata son da baya ganin laifinta akan komai, a wata rana Allah yayiwa Uncle dinta rasuwa sunji mutuwarshi, musamman ita daya zama gatanta, hankalinta Ya tashi saboda tasan Beatrice ba zata raga mata ba tun da mai goya mata baya baya araye yanzu zata samu damar rabata da mijinta, ko ta kashe ta kamar yadda ta saba fadin itace zatayi ajalin ta.
Chapter 149 · 0% Book details