← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 196 OF 201

Sashe 196

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Unexpected Ta hango shi A dining room ta cikin glass Yana a zaune kan dining mat ya tattara hankalinsa akan wayarsa da ya ke pressing, Nannauyar zuciyar ta sauke, Ta nufi Dining room din, ta tsaya daga bakin kofar tana
are mashi kallo mai cike da shaukin shi, pyjamas din jikinshi sunyi mashi kyau sosai sun kara fito da hasken fatarshi fara sol.

Ya nutsu abunsa, bai lura da zuwanta ba, dadin kallonshi ta ke ji cike da
okinsa kamar ta ha
iye shi ta ke ji, Aranta ta ayyana wai yanzu nan mijinta ne Uban ya'yanta nan gaba?

Wonders shall neva end, Allah ya za6e ta a cikin dubunnan mata ita
aya Ya mallaka mata shi!

Ya Allah, kamshin Jikintane Ya ziyarci hancinsa, nan take ransa Ya bashi tana a tare da shi, a hankali Ya
ago da sleepy eyes dinsa Ya dube ta da su, gaba
ayansu akwai gajiya da bacci acikin idanun su ga yunwar da suke fama da ita wuni guda baci ba sha.

"Ke nake jira, Kizo muyi dinner nasan kina jin yunwa"
ya fa
a yana nuna mata kayan abincin dake shake akan mat din, nufo shi tayi kamar wadda aka zarewa Laka, daga bayan shi ta tsaya tana kallon dinner din, arabian dishes ne a cikin Silver platters and Coffer, aroma dinsu ne Ya fara dakar hancinta ta fara hadiyar yawu, tana leken abincin, Ganin bata da niyar zama ta tsaya bayan shi, yasa shi yi mata gyaran murya, dakyar ta motsa ta zagaya zata zauna daga karshen Dinner mat din, Tana satar kallonshi suka hada idanunsu cikin na Juna, girgiza mata kai yayi"kinyi min nisa, ba haka nakeso mu dinga cin abinci ba..

" dan zare ido tayi, tare da jinjina kai, ta dawo zata zauna tana facing nasa, still ya girgiza mata kai, Ta rasa gane me yake nufi, ganin ta toge yasa shi mika mata hannu"zonan"!

Yadda ya kirata kamar
aramar yarinya, ya zatayi tun da karkashinshi take, Wuka da nama suna a hannunsa, sai yadda ya ga dama..

Matsawa tayi daga gaban shi, harta yunkura zata zauna agefen shi, Ya janyo hannunta gaba
aya ta rubzo saman laps dinsa,daidaita zamansa yayi yadda zataji dadin zama, kuma yana kallon face dinta.

Wani shock taji kamar electric current Ya ta6ata.

Saboda kunyar shi yasa ta rufe idanunta.

Kallon fuskarta yayi kamar zaiyi murmushi, har cikin ranshi da
i ya ke ji na kasantuwar su ma'aurata, yana mai mamakin kunyarsa da ta ke ji bai dauka angel dinshi zataji kunyarshi irin haka ba.

"Haka nakeso mu dinga zama idan zamuci abinci" can kasan makoshi ta furta"toh"
"Tayaya zamu iya ciyar da junan mu bayan kin rufe idanunki"?
dakyar ta
an bude su batare data dube shi ba.

A hankali ya dauko tea put me dauke da gahwa (Arabic coffee) Ya tsiyaya masu a cikin Silver cups, Ya ruko cup daya ya mi
a mata, hannunta na kerma ta kar6a ta kanga abaki, kamshin tea din ne Ya ratsa hancinta har batasan sa'adda ta kur6e shi duka ba, tana so ta dan ja aji kar yaga hadamarta amma takasa, sau uku yana
ara mata coffee tana shanyewa, yayin da shi ko rabin cup dinsa baiyi ba, ta
osa su fara cin abinci yunwa ta ke ji kamar kamar me.

Silver platter ya bu
e mai
auke da Chicken machboos
(Abincin gulf ne, wanda aka yi da shinkafa da nama,)
tuni taji miyanta yatsinke, sam ta shafa'a ta tsoma hannu batare data sanya spoon ba, ta fara duma loma abaki tana ci, kasa ci yayi ya nutsu yana kallon ta gwanin ban sha'awa, tana tsaka da cizgar cinyar kaza ta
ware, da sauri Ya dauko glass of zamzam Ya mi
a mata, arazane ta dube shi bakinta dama dama da maiko,
aga mata gira yayi da sauri ta sunkuyar da kanta kasa cike da jin kunyarshi, ta bude baki ya kwafa mata bakin cup din tasha ruwan mai sanyi da dadi.

"Kin tuna ranar da yunwa ta farkar damu tsakar dare agidan kurkukun
addara, muna laluban kwandon abinci muka hada hannu atare muke ruke kwandon.."
batasan sa'adda ta fashe da dariya ba, Murmushi yayi idanunsa akan white teeth dinta, dimple dinta yafi komai tafiya da shi.

Ta shagala tana ta dariya har ta dan kwantar da kanta saman kirjin shi.

Dama da biyu ya tuna mata ranar, saboda yana son ta daina jin kunyar cin abinci agaban shi, yafi son ta saki jiki da shi suyi rayuwar farin ciki.

Tsagaitawa tayi da yin dariyar tana fadin"na Tuna ranar, idan bazan manta ba, dana hana ka har kayi zuciya ka ki ci ko"?

Ta fa
a tare da kallon shi kaitsaye idanunsu suka shiga cikin na juna, dage mata gira yai alamar eh, da sauri ta kawar da idanunta gefe
aya, cikin nisha
i suka cigaba da cin abincin, tun tuna jin kunyar shi harya fara bata abaki itama ta soma bashi, saida sukaci suka
oshi, a lokacin dare ya ritsa sosai, Suna kammala Cin abincin ya dauko mata pain reliever ya bata tasha saboda ta kara jin sau
in jikin ta.

Daga bisani ya sa6eta da hannayensa biyu Ya nufi Bedroom da ita, Asaman gado Ya shimfi
ar da ita kamar new born baby, tayi lamo tana bin shi da kallo,Addu'a yace suyi sannan, ya kashe hasken dakin, Ya Hau kan gadon daga bayanta, Ya Janyo duvet din Ya lullu6e masu rabin jikin su, kwata kwata bai matsa kusa da ita ba da akwai tazara a tsakanin su.

Ji tayi bazata iya jirewa ba gudun kada ta juya taga babu shi yasa tayi tunanin ta
an juya ta saci kallon shi, A hankali Ta dan juya ta dube shi, ya lumshe idanun shi kamar maiyin bacci.

Nutsuwa tayi tana kallon kyakkyawar fuskarsa yayin da take tuna komai daya faru a tsakanin su yau, kafin ta sauya a kalar tunanin nata zuwa kalmomin daya furta mata kafin tafiyarsu kai farmaki, taso ayau dinnan ta cika mashi burin shi amma tsoro ya hana ta, da dabara ta mirgina kamar irin cikin magagin bacci ta matsa kusa da shi, ta ha
e jikinta da nashi, da sauri ya tallabe bayanta da hannayen shi tare da cusa hancinshi tsakankanin wuyanta har wani sautin shakar kamshin ta yake fitarwa, a hankali itama ta cusa hannayenta a cikin sumar shi tana shafawa kamar tanayi mashi susa, tun sunayi cikin hankalinsu har bacci ya fara fisgar su cikin shau
in juna, in a short time bacci mai nauyi yayi awon gaba da su, yadda suka
ame juna kamar zasu dawwama a haka.

Tun
arfe 2 da rabi na dare suka fara sharar bacci, Har wuraren
arfe goma na safe ba su farka ba, Tsawon Awanni takwas Cuff.

Lokacin daya farka daga bacci, Unaisah ko motsawa batayi ba, tayi nisan kiwo a cikin baccin ta kamar matatta, ta haura kafarta daya asaman waist dinsa.

Abu na farko daya farayin tozali da shi sa'ilin daya bu
e idanun shi itace kyakkyawar fuskarta, Akan ta ya sauke eyes dinshi, yadda take fitar da numfashi kamar wata jinjira cikin natsuwa da kwanciyar hankali,murmushi ne ya subuce mashi Dan kadan kafin a hankali yayi kasa da idonshi ajikinta,yadda take numfashi a hankali haka kirjinta ke hawa da sauka ba karamin jan hankalin shi su ka yi ba, bakomai ya ke tunawa ba face time din da babu albarkatu a kirjinta, kamar na namiji saboda shafewar su, bai ta6a tunanin wannan ranar zatazo ba, kamar zaiyi murmushi ya dan ta6e red lips dinta.

Fuskarta Yabi da kallo tana bacci kamar jinjira.

Ya gaza yarda Ya mallaki Unaisah, Yanzu tashi ce ita, matar shi, uwar ya'yanshi masu zuwa, ta zama a karkashin ikon shi, Nauyin komai nata na akan shi, Allah ne kadai Yasan farin cikin da ya ke ji.
a cikin zuciyarshi ya karanta addu'ar tashi daga bacci, A tsanake Yake sake bin eye lashes dinta da kallo, a hankali Ya Daura yatsunsa asaman sumar kanta Yana dan shafa mata ita kamar jinjira, kwata kwata bai lura da lokaci ba, saboda shagalar da yayi gurin kallonta.

Kamar ance Ya dubi agogo, arude Ya zare eyes dinsa ganin karfe goma na safe, Bacci Ya shagalar da su har asuba ta wuce ba su yi Ibada ba.

Tunani ya somayi tayaya zai tayar da ita daga bacci batare daya takura mata ba!

Badan sallah ba da ba abun da zaisa ya farkar da ita.

Saitin kunnanta ya kai labbansa cikin muryar ra
a ya furta
"ya rouhi, Tashi muje muyi sallah, mun makara"
shiru bata farka ba.

Sau uku yanayi mata ra
a kamar wanda zai tayar da jinjira.

Yasan ta da nauyin bacci wani lokaci,balle jiya data jigata.

Qira'ar Alqur'ani ya soma yi mata cikin nutsatstsiyar muryarsa, Unexpected cikin bacci ta tsinkayi
ira'arsa mai dadin sauraro irin ta Larabawa.

Tana bu
e idanunta kaitsaye suka shiga cikin nashi, ta
ura mashi idanu tana kallon yadda ya ke motsa labbansa yana qira'a tayi mamaki sosai, jin surar da yake Karanta mata da kai batare daya duba al'qur'ani ba, Saida ya kai aya tukunna ya dakata yana lumshe idanun shi yace"barka da safiya ya malak albi, kin tashi lafiya" lumshe idanunta tayi tana jin ta awata duniyar nisha
Saida ta fara karanta addu'ar tashi daga bacci duk yana kallon ta daga bisani tace
"My man In har zaka dinga tada ni daga bacci irin haka zanfi kowa more tashi daga bacci, zanji dadi idan ka zama mutun na farko da zan fara yin tozali da shi a duk lokacin dana farka daga bacci.

Murmushi yayi wanda bai wuci fatar labbansa ba.

"Mun makara bamuyi sallah ba"
da sauri ta dubi agogo, zare idanu tayi, tare da yin saurin mi
ewa, Batai aune ba, Taji Ya cuccu6eta ya sauko da ita daga kan gadon, A saman kafadarshi Ya sa6e ta, Babu alamun Yana jin nauyinta, Ji ya ke kamar ya
auki jinjira, Toilet Ya shige da ita.

Bayan sunyi alwala, suka fito Coset room suka shige don su shirya kan su, jim ka
an suka fito cikin shigar larabawa hannunsu ruke cikin na juna suka nufi prayer room wanda komai na cikinsa na yin ibada ne.
Chapter 196 · 0% Book details