← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 187 OF 201

Sashe 187

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar Omair ya ga tarin masoyan sa, mutane suka dinga daukar hotuna da shi, wasu ma video su ke yi, a karshe taro Ya tashi lafiya, kowa ya tafi da farin cikin ganin Omair.

Bayan kammaluwar Partyn, daga bisani Hateem ya tafi Da mutanansa Private resident dinsa na dubai, A Falo suka zauna cikin muryar lallashi suka fara zayyana masa dalilin daya kawosu Dubai, su ka
ara da cewa Ya taimaka ya dawo kan mulkinsa, canada tana bukatar shi, su basu gaji da shi ba, suna son shi, suna son mulkin sa, ya janye maganar murabus dinsa, kar ya damu su ba zasu ta6a ala
anta shi da laifin babansa ba, sun yarda da shi, sun san bashi da sa hannu, mutane suna ta
orafi akan murabus dinsa Ya taimaka kar ya karya zuciyar wa
anda suka aminta da shi.

Kalaman su sun so suyi tasiri a cikin zuciyarshi sai dai bayajin zai iya komawa ga mulkinsa.

Yace yaji dadin nuna damuwa akan shi da su ka yi, shima Yana son su Yana jin inama zai iya cigaba da ru
e canada sai dai kash zuciyarsa ta yi raunin da ba zai iya ba, ayanzu yafison Ya koma kasarsa cikin Yan uwansa don ya ci gaba da rayuwa da su.

Kamar zasu sanya mashi kuka, ba irin magiyar da basuyi mashi ba amma ya kafe akan bakansa, a karshe sukace zasu tafi masaukinsu amma ba zasu bar dubai ba, har sai sun yi nasarar shawo kan shi tukunna.

Bayan sunyi sallama da shi, Ya koma Ruler's resident Ya kira Mujeedat awaya, bayan ta same shi a part din ta, Suka zauna cike da damuwa ya fayyace mata komai da suka tattauna da bakinsa na canada.

Ta numfasa tace ita kanta bazata goyi bayan murabus dinsa ba, tuntuni taso tayi masa magana bata samu damar yi ba amma bataji dadin murabus din da yayi ba a live video din daya saki, meyasa zai sare saboda laifin da bashi ya aikata ba? mutanan canada suna son shi, kada Ya karya musu zuciya, tun da har su basu nemi Ya sauka daga kan mulkinsa ba why shi zai aje"?

Yace mata ta fahimce shi, ba zai iya ba, yayi rauni, mulkin ya fita aransa, dama siyasa ba ra'ayinsa bace, baban su ne Ya cusa masu ita, Yanzu kuma yaji ta fita aranshi, bayason komai daya shafi siyasa yafison Ya rayu tare da yan uwansa a Nigeria, tun da babu abun daya nema ya rasa, kuma abun da yafi damunshi lokacin da zai ba Omair, Idan har ya koma kan mulkinsa tayaya Omair zai samu kulawar sa?

Yana son ko da yaushe ya kasance a tare da shi.

Kalaman sa sun karya mata zuciya, ta fahimce shi sosai, ta kuma fahimci dalilin dayasa mulkin ya
ara fita ran shi, amma tace yayi hakuri ya koma inyaso nan gaba ka
an Sai Ya aje mulkin amma yanzu idan yayi murabus babu gaira ba dalili ga abun daya faru da mahaifinsa mutane zasu zargi wani abu.

Dakyar ta samu ta shawo kan shi har ya ce zaiyi shawara da Yan uwansa yaji ta bakin su.

Wata
aya su ka yi A Dubai
ashin kulawar dangin Mujeedat, daga bisani bayan daya gama yin shawara da yan uwansa gaba daya suka goyi bayan ya janye murabus din da ya yi har suka fa
a masa game da abun daya faru bayan zuwan dangin iyayensu mata, yayi farin ciki mara misaltuwa, ya kuma
ara jin karfin gwiwa a tare da shi, su ka ce koda zaiyi murabus din kada yayi saurin yanke hukunci Ya bari sai nan gaba zuwa lokacin da
ura ta lafa idan yaji baida ra'ayin ya cigaba sai ya yi murabus
in, suma sun nuna basu son mukamansu amma danginsu iyayensu mata sun nuna rashin goyan bayan su su yi hakan sun kuma
arfafa masu gwiwar su cigaba.
haka kuwa akayi bayan ya gama yanke shawara da su, batare da 6ata lokaci ba su ka koma babban birnin Canada.
~________________________________Ottawa, Ontario, Canada~
A ranar da suka isa, Bayan da jirginsu yayi landing A airport, Yan jarida da Yan kasa suka cika makil domin tarbo sa sai farin ciki sukeyi da murnar dawowar Hateem da dansa Omair, dakyar Secuty details nasa suka yi masu
awanya har suka shiga cikin motocin escorts din da su ka zo
aukar su.

A washe garin ranar da suka koma Canada, har party governor general Yasa aka shiryama Hateem da Iyalinsa saboda murnar dawowarsa da kuma tayasa murnar ganin
ansa Omair.
manyan
usoshin gwamnati da shahararrun
an jarida ne suka hallara domin tayasu murna.

Danish dai Yasha ruwan mamakin Ganin yadda Al'umma suke Girmama iyayen sa, shi kanshi dayake ba
o a family din nasa girmamasa su ke yi..

Anan ma Ya samu wasu
arin kyaututtukan na ban mamaki har baisan ma inda zai sanya kanshi ba saboda ru
ewar da ya yi duk da azahirin gaskiya Omair bai damu da abun duniya ba, hasalima ba kowani kyale kyale ke burgesa ba, amma idan aka basa kyauta yana jin dadi sosai saboda akwai wadanda ya ke da burin ya bama kyaututtukan.

Cikin
anin lokaci rayuwar Omair ta sauya, musamman saboda ya samu gogewa ta bangaren ilmin addinin musulunci dana boko yasa Prime minister Ya
auki hayar private teachers din da zasu dinga zuwa har gida suna ilmantar da shi, bayan teachers din da Hateem Yasa suna koya masa karatu saida Gimbiya mujeedat ta dauki hayar therapist da Mentor saboda shi kawai, Albashi mai tsoka suke biyan su burinsu Omair Ya cika burinsa na samun ilmi, ya kuma manta da trauma din da ke damun shi.

Bayan haka sisters dinsa duk idan suka samu free time suna ilimantar da shi ta hanyar bashi lokacin su, su fita yawon sha
atawa da shi, haka mom dinsa da daddynsa basu gajiya da 6ata lokaci gurin faranta masa rai, gata yayi masa yawa, jin dadi ta ko'ina, Ya rasa gane waya fi son shi tsakanin iyayensa da sisters dinsa?

Kowa burinsa ya faranta masa rai, basu san 6acin ranshi, Ko jinjiri bai kaishi samun kulawa ba, ko sautin tarinsa ya sauya sai sun kira doc dinsa ya duba lafiyar sa.

Baida lokacin komai saina karatu, su kansu suna mamakin yadda yaba karatu muhimmanci fiye da komai in ka cire ibadarsa.

Baya gajiya da yin karatu, idan kana nemansa, Ka duba cikin bedroom dinsa a saman kujerar study table dinsa, idan baka same shi anan ba, to ka duba a home library, In nan ma baka gan shi ba ka duba garden, ko Classroom dinsa Inda teachers dinsa ke koya masa karatu.

Bawan Allah, kullum Yana a rungume da books yana karatu, sometimes da su ya ke kwana rungume a kirjin sa, yasa naci da dagiya, Ya sadaukar da
walwarsa ga karatu, ko bacci ya ke yi ya dinga sambatun karatun da akayi masa.

Abun dayafi basu al'ajabi game
da shi kaifin basirar da ke gashi da saurin hadda ce karatu, he was gifted and a genus, masu wuyar samu a duniya, su kansu malamansa Yabon shi su ke yi suna al'ajabin irin haza
ar sa.

Malamansa har fita sukeyi da shi Yawon bu
e ido badan komaiba sai don su wayar mashi da kan shi ya kuma
ara ilmi.

Iyayensa sun
aura burin duniya akan shi, son shi su ke yi da zuciya
aya, Komai nasa mai tsada ne, suturarsa, takalmansa, turarensa, abincin sa, basu wasa da komai na shi, musamman su ka ware masa bodyguards masu kula da shi.

Cikin shekara
aya kacal su ka yi nasarar goge masa trauma din Suka wanke masa
walwar sa da jin dadin rayuwa, Ya sauya gaba
aya, Ya zama wayayye mai tsantsar ilmi, ya goge ta fannin rubutu da karatu, haddar al'qur'ani dayafi bada himma akanta, Har yayi izuf talatin a cikin shekara
aya da watanni, tsabar wayewarsa ko magana yayi sai yaja hankalin mutun saboda komai nasa cikin qasaita da aji yakeyin sa, hatta salon tafiyarsa ta sauya, idan yayi dressing Ya fito outing gaba daya idanun mutane ke dawowa kansa.

Yan matan dake hauka kan soyayyar shi basu
irguwa.
shafukansa na social media miliyoyin mutanene ke following dinsa.

A cikin shekara ta biyu ne da iyayensa suka tabbatar Ya samu wayewa da gogewa ta fannin ilmi sanan suka fara tunanin sanya shi school, dama abun daya hana su sanya shi tun farko abu biyu ne!

Saboda basu san ya fara zuwa makaranta a matsayin jahili wanda baisan komai ba, saboda gudun kada students su dinga tsokanarsa, dama ga ba
in tabon da kakansa Yabar masa dole asamu wadanda zasuyi bullying din shi akan abun da kakansa ya yi, shiyasa sukaji shakkar su sanya shi amma yanzu sun samu
warin gwiwar kaisa school da zumar zasu baza guards dinsa har cikin Class din da zai zauna saboda tsaro.
malaman sa na gida ma sun goyi bayan su kaishi school saboda zaifi samun ilmin zamantakewa da mutane idan yana mu'amala da su, dama dole sai kana tare da mutane ka ke iya koyan zama da su.

Ko da suka tambaye shi me ya ke da burin ya zama nan gaba? yace baida burin daya wuce ya zama jami'in Isod saboda yana son aikin da zai taimaki rayukan Al'umma da kuma kawar da mugun iri a cikin su.

Sun yi farin ciki da jin hakan sosai, duk da za6in nasa bai kwanta aran su ba, saboda basu san yayi aikin da zai iya jefa rayuwarsa a ha
ari amma saboda jin kyakkyawar manufarsa yasa basu nuna
in amincewar su ba, bayan haka suna son abun daya ke so, dan kuma saboda Owais.

Bayan Prime minister ya kira Owais awaya ya fa
a masa abun da suka tattauna da Omair, Owais yayi farin ciki sosai da jin burin da ya ke da shi na zama jami'in isod, dama ya dade yana yi masa sha'awar ya zama Jami'in Isod, tun lokacin daya ga irin
arfin da Allah yayi masa Yasan cewa zai iya!

Nan ta ke ya shawarci prime minister da su sanya shi jami'a ya karanci cybersecurity, prime minister yace ya gode da shawarar da ya ba shi.
Chapter 187 · 0% Book details