← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 201

Sashe 102

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jan Gashi ya ce, "Musa ne ya yi mana cinne, maci amana, ya yaudare mu, ya zama dole mu 6ace ......"
A lokaci
aya suka buga sandunansu
asa da niyyar su 6ace, sai dai me, babu abun da ya sauya suna nan a inda suke, a ru
e suka kalli sandunan nasu, cikin zafin nama suka
ara buga su da
arfi, still basu bace ba, firgici da karayar zuciya ce ta same su, sam sun gaza yarda da abun da ke shirin faruwa da su, cikin
imuwa suka ci gaba da bubbuga sandunansu
asa kamar mahaukata duk sun bi sun ru
Sojojin dake a kewaye da su sun yi tsaye suna kallon su, kamar masu kallon wasan
wayo.

"Idan kun gama buga wasan naku, muna jiran ku." A cewar Chief Owais.

Ba su yi aune ba, kwatsam!

Wani ba
in hayaki ya soma kur
owa ta cikin
ofofin hancinsu akan idanun su, wata irin razana suka yi ganin Evils din jikinsu suna fita wanda hakan na nufin sihirin su ya bar jikin su yanzu saura
arfin da Allah Ya halicce su da shi, Tashin hankalin da ba'a saka ma shi rana!

Rikicewa suka yi, sun rasa gane wanene ya yi masu wannan aika aikar?

"Arrest them!" Chief ne ya fa
a, da sandunan hannayensu suka soma kokarin kaima sojoji bugu, aikuwa suka rufe su da bugu saida suka raunata kowace ga6a ta jikinsu, suka yi masu bugun mutuwa, suka wanke jikinsu da jini, daga wanda ya rasa hakoransa sai wanda ya rasa idonsa
aya, duk saida suka rarrabasu da kayan jikinsu ya rage daga su sai gajerun wanduna, jikin nasu ma babu kyan gani duk gashi cunkushe wasu
azamai da su, gaba
ayan su farar fata ne, basu ta6a muzanta da shiga tashin hankali ba irin na yau, kafin sojoji su tafi da su,
aya daga cikin su ya fakaici idanunsu ya yi saurin zare bindiga daga
ugun soja batare da sojan ya ankara ba, ya harbe ma
oshin shi nan take ya fa
i a mace,
aya kuma Zuciyarsa ce ta buga da bakin ciki nan take ya fa
i shima a mace, sun
wammace su kashe kansu akan a tafi da su saboda sunsan ba zasu yi masu da kyau ba, a tunaninsu mutuwa ce mafita a gare su, basu san cewa sun
ara jefa kansu cikin musiba bane don har
wara su ji kunyar duniya.

Sojojin basu ji dadin wadanda suka mutu ba, saboda ba su son su mutu batare da sun fallasa ma duniya abun da suka aikata ba, sun fi so su ji kunyar duniya, su kuma gir6i abun da suka shuka.

Ukun da suka rage basu a cikin hayyacin su shiyasa basu iya ta6uka komai ba, dama da igiyoyinsu suka zo, aikuwa suka
aure su kamar dabbobi, shidda daga cikin sojojin suka fuce da su daga kurkukun ta ainihin babbar
ofar fita daga kurkukun
addara wadda a
alla tayi shekaru sama da ashirin batare da an bu
e ta ba sai yau da dubunsu ta cika!

Ko tayaya akai hakan ya faru?

Nima na ru
e amma bari dai mubi al
alamin Boss !

Shin Ina Jan Wuya ne
Ransa fari fat, ya
a6e kwalbar zuciyar a
irjin shi, shine a gaba gaba, Dr Mark yana a gefen shi, Jan ido da Jan le6e suna a biye da bayansu kamar bindi, sai zumbula uban sauri suke yi don su
arasa ga temple of evils.

Inda mazaunin dodon tsafin su ya ke, tsabar yadda suke sauri kamar zasu tashi sama..

Lokacin da suka kusa
arasawa daga inda suke suna iya hango Temple of Evils da ke a kewaye da wasu samudawan Evil Giants, dogaye ne masu fadin kirji, tun da uwata ta haife ni ban ta6a ganin mutane masu irin
wanjin su ba, kallon su ka
ai zai iya sa gaban mutun ya fadi, ga mutum mai tsoro har suma zai iya yi idan ya gansu saboda firgitarwar da ke gare su, zai yi wuya in mutane ne ba zallar evils ba, hatta sautin takunsu kamar na dawakan ya
i, gaba
ayansu a sanye suke da jajayen dogayen riguna masu huluna, baka iya ganin komai nasu daidai da idanuwansu sai dai su su ganka, wadannan Evils din daban suke ko a gidan Kurkukun
addara, sune masu tsaron temple dinsu wato mazaunin dodon tsafin su.

Suna da
arfin iko, basu san wani abu wai shi tausayi ko imani ba, saboda babu wannan a cikin zuciyar su, kuma suna da sharu
ansu, kafin ka tunkare su ka tabbatar babu tsarki a tare da kai!

Ba'a ambaton sunan Allah gurinsu ko wani abu da ya shafi addini!

Suna da girman kai da izza, basu magana sai dai suyi kwatance da hannayensu, suna dariya amma basu kuka, ba su
aukar raini, kuma ba a yi masu
arya, uwa uba ba su son maci amana, ba su yarda da kowa in ba Elder Obinna ba da aminin sa Jan Harshe, su ka
ai ne suke basu umarni su bi batare da an samu matsala ba, amma bayansu babu wani mahalukin da ya isa ya kawo masu wargi batare da sun azabtar da shi ba.

Kuma idan zaka shekara kana zarya a gidan kurkukun
addara ba zaka ta6a ganinsu suna sintiri ba, basu wuce iyakarsu, aikin su a temple yake nan ka
ai zaka iya ganin su, bakowa ke iya ganin mazaunin dodon tsafi ba sai mai sihiri a jikin shi, ko lokacin da sojoji suka kawo farmaki sun shiga ko'ina amma idanunsu basu gane masu mazaunin dodo ba, idan masu karatu ba zasu manta ba, Unaisah tamu tagargajiya ta ta6a yi masu le
en asiri har suka yi mata wankan jini, itama a lokacin Allah ne ya nufa zata ga temple din da idanunta sai dai bata ga ainihin mazaunin dodon ba, da kuwa ta gama gani a duniya.

Yayin da suke tunkarar su,
Wani mayaudarin kallo Mark ya ke bin Musa da shi mai wuyar fassaruwa, batare da shi Musan ya lura ba, da alama akwai wata a
asa.

Jan ido da Jan le6e dai sai bin su suke yi kamar jela, kowannansu da muguwar manufarsa a rai.

Lokacin da suka
araso gaban
ofar Temple din, dakatawa suka yi da yin tafiya ganin yadda temple Evils din suka kare kofar shiga.

Cike da gadara Musa ya soma yi masu magana cikin harshen su na matsafa,
"Na cika sharu
an da aka bu
ata, na kashe Kaddarar Kurkuku, na kuma cire Zuciyar Kurkuku." Ya fa
a yana nuna masu kwalbar zuciyar cike da alfahari.

Sannan ya
aura da cewa, "Don haka ku bani hanya in wuce ciki, yanzu ni ne shugaban ku..."
arasa maganar cikin izza yana cika yana batsewa.

Da hannu,
aya daga cikinsu ya yi mashi kashedi mai nuni da garga
i.
yacewa ya yi da
ar iskar dariyarsa cike da izza ya ce, "Kada ku ce za ku yi min taurin kai, ni ne uban gidanku a yanzu, dole ku mi
a wuya ku yi mini biyayya sau da
afa, idan ba haka ba da zarar na hau karagar Elder zan shafe babinku, ku bani hanya in wuce..." Ya fa
a yana dariya.

A hankali Dr Mark ya soma ja da baya da baya, cikin takun san
a ya arta a guje batare da sanin su ba, ya rage saura su uku.

"Ba ku ji abun da ya ce bane?

Ku bamu hanya mu wuce, mu
arasa aiwatar da abun da ya kawo mu." Jan ido ne ya fa
a a tsawace...

"Anya kuwa ba a yi kuskuren wani abu ba?

Meyasa suka
i bamu hanya mu wuce?

Idan har da gaske sharu
an sun cika kamata ya yi tunkan mu
araso zasu dare su bamu hanya..."
Jan le6e ne ya fa
a zuciyarsa cike da kokwanto.

Cikin sauri ya dubi kwalbar zuciyar da Musa ya rungume a
irjinsa.

Nan take gabansa ya fa
i ganin wani abu.

Cike da tashin hankali ya ce, "Musa mun mutu!

Ka ja mana bala'e, wannan ba zuciyar yarinyar bace...!" Kai tsaye maganar Jan le6e ta dira a kunnanshi, kusan a tare Jan ido da jan wuya suka dubi zuciyar dake a cikin kwalbar nan take suka ga tayi duhu ba
irin sa6anin
azu da jini ne a jikin ta, tsantsar ru
ani ne da tashin hankali ya bayyana akan fuskokin su, wallahi an shammace shi, gaba
aya ya razana ya bi ya ru
e ya rasa gane meke shirin faruwa da shi?

Wanene ya ci amanarshi ya yaudare shi, tunawa da Mark yasa shi saurin furta sunan shi, "Mark!!

Mark..!!!" Gabansa ne ya fadi ganin babu Mark babu alamarsa nan take ya fahimci Mark ne ya ci amanar shi ya bashi zuciyar evil giant a matsayin zuciyar Batool!

Bai ta6a zaton hakan daga gare shi ba!

Mark Ya shammace shi.

Wata irin kururuwa ya fasa ta ba
in ciki, ya rufe idanunsa gam, baisan sa'adda ya saki Kwalbar ta fadi
asa ta fashe, sai huci ya ke yi yana gurnani kamar mayunwacin zaki..

Batare da sanin shi ba, Jan ido da jan le6e suka zame jiki da gudu suka bar gurin ya rage saura shi ka
ai, saida ya gama haukan nashi ya juyo ya ga babu su..

Cikin fusatacciyar murya ya ce,
"Ka tabka babban kuskure Mark!

Har ni zaka ci amanata!

Na rantse bazan
yale ka ba, sai na yi maka azaba, Mark ka gama yawo, dole in kashe ka!!!"
Sai sambatu ya ke yi kamar mahaukacin kare, yana
arin
aga
afarsa Temple Evils suka yi mashi
awanya, Tashin hankali! dara ta ci gida!

A dabarbarce ya furta, "Don ubanku ba zaku bani hanya in wuce ba eye!

Kar ku kuskura ku bari in bu
e idanuna in ganku a gabana!"
arashe maganar a tsiwace kamar zai doke su, ya runtse idanun shi yana fitar da numfashi mai huci, niyyar shi ya yi masu sihiri ya kashe su idan su kai masa gaddama.
Chapter 102 · 0% Book details