← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 201

Sashe 44

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tunani na damuwarka tawa ce, bai kamata ka boye min ba, Pls ka fadamin zan taimaka maka mu shawo kan matsalar..."
numfashi Yaja tare da furzar da shi, ganin taki tafiya yasa shi daka mata tsawar da ta tsoratar da ita
t you dare make me repeat what I said!

Get out of my room before I do something bad.
gyada kai tayi, idanun ta cike tab da kwalla ta soma ja da baya tana cigaba da kallon bayansa, ta lura ko kallon ta baison yi, abu kamar aikin asiri in a short time ya canza musu.

A hankali ta juya takai hannu zata bu
ofar, sai kuma ta fasa saboda zuciyarta dake azalzalarta akan kada ta tafi, ta tsaya taji meke damun sa.

Sakin handle din kofar tayi da tunanin tayi ko karta aikata abunda zuciyarta ke saqa mata, ga tunanin nasihar dadynta amma bata jin zata iya barin shi a halin da yake ciki, juyawa tayi slowly ta nufe shi tana karasawa batay wata wata ba, ta fa
a kan bayansa, she slowly wrapped her arms around his waist, ta daura tafukanta a saman shafaffen cikinsa, lokaci
aya ya tsinci kanshi awani irin yanayi mai wuyar fassaruwa, har baisan sa'adda Ya saki sirinjin hannun sa ba, wata irin kasala ta haifar masa, lumshe idanun shi yayi a hankali yana jin bugun zuciyarta da hucin numfashinta on his neck.

Yatsunsa taji akan hannunta yana kokarin banbareta don ya rabata daga jikin shi, cikin sauri ta furta"na roke ka, dan Allah, dan soyayyar da kake yiwa manzon Allah SAW kada ka kore ni, ka barni atare dakai, inaso naji meke damunka, ko ban sama maka mafita ba, zan tayaka addu'a Allah ya yaye maka damuwarka, baka taba barin mu cikin damuwa ba, taya kake tunanin ni zan iya barin ka a mayuwacin hali irin wannan"?

Kalamanta sun sanyaya zuciyarshi, sai dai baya jin zai iya fada mata abunda ke damunsa, baisan ya zasu dauki abun ba idan suka ji cewa kakansa ne Elder mamallakin gidan kurkukun kaddara, mutumin daya azabtar da rayuwarsu, Ya Ilahi, Ji yake kamar kowa zai juya masa bayane..
wata irin kara mai tattare da bakin Ciki Ya fasa, tuni shatun jijiyoyin goshinsa dana wuyansa suka fito ru
u ru
u saman fatarsa, tun da ya yi tsawar gaban ta ya fa
i rass hankalin ta ya
ara ta shi duk tabi ta ru
Nauyin jikin shi daya sakar mata ne yasa ta gaza jurewa saboda yafi karfinta nesa ba kusa ba, aikuwa gaba daya suka fa
a saman bedmattress dinsa.
a rubda ciki ya fa
a yayin da take akwance saman bayansa, sam sun kasa motsawa har na tsawon mintuna, dakyar ta yi kokarin raba jikin ta daga na shi, da wata irin kasala ta mike zaune tare da zuba mashi idanunta da suka cicciko da kwalla.

Duk da batasan meke damunsa ba, amma hankalinta ya tashi ta kuma ji tsantsar tausayin sa acikin zuciyar ta, jikinta harya fara daukar
umi saboda zafin jikin shi da ta goga silar ha
uwar da fatarsu tayi.
ya kasa jure radadin da yake ji ne, baiso ya bayyana rauninsa a fili ba, duk yadda yaso ya danne damuwarsa ya kasa bawan Allah.

Cikin shesshekar kuka ta dinga tambayar shi meke damunshi har ta ha
ura ta yi shiru saboda ya
i furta kalma, daidaita nutsuwarta tayi cikin sanyin murya ta fara zuba mashi kira'ar alqur'ani mai tsuma zuciya, lokaci
aya ya fara jin tamkar ana wanke damuwar da ke acikin zuciyarsa, bacci ne ya ziyar ce shi a hankali ya fara lumshe idanun..
bata kaiga dire ayar data janyo ba, kwatsam ta fara jin gyangya
in bacci har bata san lokacin da ta sulale gefen sa ta kwanta ba, Kafin wani lokaci, wani wahalallan Bacci yayi awon gaba da su, ikon Allah kenan bai kaiga yin sedative injection din da ya so yayi ba, sai gashi silar karatun qur'anin da Unaisah tayi masa yasa shi yin bacci...
sai da suka shafe tsawon awanni bakwai suna yin baccin, tun karfe
aya da rabi na dare, har karfe bakwai na safe basu farka ba kamar wadanda suka sha sleeping pills.

Tun da garin Allah ya waye Batool taga babu Unaisah a dakin, har toilet ta duba bata ganta ba, hankali atashe ta nufi dakin aunty ummi don ta dubo ko taje can, tana zuwa taga babu unaisah nan ta fada ma Aunty ummi bata ganta adaki ba, hankalinsu atashe suka fito neman ta, sako da lungu na gidan sun duba basu ganta ba, kuma basu kawo ma ransu tana adakin Chief ba, har dakin Taj suka shiga a lokacin yana a zaune kan darduma Yana jan cazbaha bayan sun gaishe da shi, Ummi ta tambaye shi Unaisah batazo nan ba, yace musu ko gifcin ta bai gani ba amma kada su damu yasan duk inda taje ba zata wuce cikin gidan ba, ya fada tare da dauko wayarsa ya danna mata kira tana ta ringing ba'ay picking ba..
__________________________________
A hankali ya soma kokarin bude idanunsa da sukayi mashi nauyi ga wata kasala data baibaiye jikin shi, jin hucin numfashin mutun a gefen shi kasa kasa cikin natsuwa ya ke fita, yasa shi saurin karasa bude idanun nasa.
tamkar wanda ya yi loosing memory dinsa, ya
an razana da ganin mace a kwance saman gadon shi tana bacci, kuma suna fuskantar juna, kitson kanta yabi da kwallo, dan mayafin da ta yafa ma kanta tuni ya bar jikin ta, kwakwalwarsa ce ke kokarin tariyo masa abun daya faru!

Nannauyar Ajiyar zuciya ya sauke, tunawa da komai daya faru tun farkon shigowarta, yayi mamakin baccin daya sha, wani iko na Allah kwata kwata babu inda keyi masa ciwo, saima wata lafiya dayaji a jikin shi, kamar ana dawo masa da kuzarinsa, yana ji aransa silar kira'ar qur'nin da Unaisah tayi mashi ne, kuma dama shi qur'ani waraka ne.

Slowly ya zame hannayensa daga kan gefen fuskarshi, Ya daura tafinsa saman lallausar sumar kanta da aka kitsa, A hankali Yake shafa gashin nata har na tsawon mintuna, kafin ya dan dago da face din tata, hakan ne ya bashi damar kallon fuskarta dakyau, wata irin nutsuwa ce ke shigar shi, yayi fatan ace bai farka daga baccin daya dauke shi ba, saboda kwanciyar hankalin daya samu..

Tunawa da sallar asubahi da bai yi bane yasa shi saurin mikewa ya sauka daga kan gadon, shaf shaf ya fada toilet yayi wanka kafin Ya dauro alwala, Ya fito waist dinsa daure da towel, Ya nufi walk in closet dinsa Ya shirya kansa cikin jallabiya, kafin ya nufi prayer corner dinsa after Ya gama sallar, yayi addu'o'i har da hawayensa, kafin daga bisani Ya mike Ya nufi gadon, a hankali ya kwanta yana fuskantarta, yaso ya tashe ta tayi sallah sai dai ya kasa yin hakan saboda bai son ya katse mata baccin ta, ya lura kamar ba ta samu isasshen bacci, ya fahimci hakanne saboda alamar daya gani saman kwarin idanunta da sukayi ja, kuma yasan shine silar shigarta halin da take a ciki, tsantsar tausayinta da kaunartane suka mamaye zuciyarsa ko gajiya da kallon ta ba ya yi, mutumin da saboda kamun kansa da gujewa abun da zai sabawa mahaliccinsa bai ta6a bari ya ke6anta kan shi da macen da ba muharramarsa ba, balle har su hada shimfida, amma yau saboda halin da yake a ciki ya kasa ankarar da kanshi kuskuren yin hakan saboda a buqace yake da son samun wanda zai kwantar masa da hankali..

Akan idonsa ta fara yamutsa pinkish lips dinta da suka bushe
amas.
ziraran eye lashes dinta sai kerma suke yi, Tunawa yayi da ranar farko daya fara ganin fuskarta lokacin data kira sa video call da kuruciyarta, a ranar kasa runtsawa yayi saboda tunanin yar tahalikar nan..

Da alama baccin nata ya
are,
ari take ta bude idanun ta da suka kumbura saboda kukan da ta sha, daura tafin hannunsa ya yi a saman gefen fuskarta, a
an firgice ta zare idanun ta.
kaitsaye suka shiga cikin nashi wani irin shock taji ganin Chief agabanta, ganin yadda ta ru
e ne yasa shi sakin tsadaddan murmushin nan na shi, baisan ya
ara jefa ta a rudu ba, duk tabi ta dabarbace sam takasa ci gaba da kallonshi, saboda yanayin data tsinci kan ta..

"Na samu bacci silar karatun alkurnin da ki ka yi min, I can't thank you enough baby..."
ya fa
a tare da dan shafa sajen gefen fuskarta da ya kwanta luff, shiru tayi tana jin yadda zuciyoyinsu ke bugawa saboda kusancin da suke da juna..
m so sorry, I made you cry, nima bada son raina ba, banso kika ga raunina ba, na kasa jure abunda ke damuna ne.." ya fada yana kare mata kallo.

In a cool voice tace"ba laifin ka bane, daga zuciyarka ne, I understand that something bad happened that put you in this difficult situation of worry, but I want you to know that I will never leave you in such a situation, It is my duty to calm you down, and I will help you find a solution after that, I will remind you, no matter what, kada ka bari hankalinka ya gushe, jarumtakar nan taka da nutsuwarka su nakeso na gani atare da kai, komai ya same mu arayuwa muyi hakuri mu mika lamuran mu ga Allah shine zai nema mana mafita".
har cikin ranshi yaji dadin kalamanta masu sanyaya zuciya, harya fara tunanin irin rayuwar farin cikin da zasuyi idan sukayi aure, zai more rayuwarsa saboda samun mace tagari kamar ta.

"Ka fada min meke damunka pls, amma idan sirrinka ne da bai kamata in sani ba, to kada ka sanar dani, kuma koda baka fadamin ba, nayi maka alkawarin zan tayaka da addu'a Allah yaye maka damuwarka ya kuma kawo maka mafita acikin lamuranka"
bai san sa'adda ya saki murmushi ba wanda har sai da fararen hakoransa suka bayyana, saboda dadin kalamin ta, ita kanta batasan ya akai ta samu kwarin gwiwar furta masa su ba, kamar ancire mata jin nauyin sa hada karin tausayinshi daya mamayeta.
Chapter 44 · 0% Book details