← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 201

Sashe 77

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Please idan kinji dadin wakar da nayi maki, Ki fito mu fuskanci juna, Inason na ganki, wallahi har nayi missing
inki Batool dina, pls ki fito zan baki kyauta ta musamman, da zata faranta ranki"
shiru tayi bata tanka mata ba, kamar zata saka ihu, Bubbuga kafafunta tayi"wai me kikeso nayi maki ne wanda zaisa ki yafe min"
_"Ki
auke ni kamar yadda na
auke ki, shi ka
ai ne zai sa ni farin ciki"_
ta fada a cikin ran ta
"Ina ta maki magiya ki fito amma kin
iya, ai ko Allah muna masa laifi ya yafe mana balle mu yan adam, Kada Allah yasa ki yafe kinji ko, Ki ta zama a cikin toilet, madaddalar shai
anu.."
still bata tanka mata ba, yamitsa fuska tayi tare da hararar kofar toilet din, dabara ce ta fado mata, da gudu ta fuce daga dakin tana fadin"oyoyo Aunty Ummi, welcome back home, we really missed you, Muna ta jira ki dawo har munyi fushi.."
A zabure Batool ta mike jikinta na 6ari ta bude toilet door din, ta watso a guje ta nufi kofar tana lekowa taga wayam babu kowa nan take ta gane set up din Unaisah ne don ta fito, nan da nan walwalar fuskarta ta
auke duff, kamar bata taba dariya ba, tana niyar ta fucewa daga dakin harta daga kafa Unexpected taji an dam
i wuyan kafarta, atsorace ta zare idanun ta tare da kallon ta, ajiyar zuciya ta dauke ganin Unaisah..

"Am sorry Aunty Batool, Kaina bisa wuyana, na tuba bazan
ara ba, bansan ki da fushi ba, pls, ki tausayawa yar kanwarki Unaisah, Zan gyara kuskurena, nasan bana jin magana amma ki min uziri hada yarinta ke damuna.."
ta karasa maganar tare da kama kunnuwanta.

Batool dake kallon ta, kiris ya rage ta fashe da dariya, saboda ta bata nishadi musamman da ta kama kunnuwanta kamar zomanya, ta wani marairaice mata fuska.

"Bai kamata ki biyemin ba, kiyi fushi dani, kefa babba ce ni kuma
anwarki, idan nayi badai dai ba, nasiha yakamata kiyi min sai in gyara bawai kiyi fushi dani ba.."
idanunta cike tab da kwalla tayi maganar, ita kanta batool din wasu hawayen ne suka cika idanunta, ta rasa gane meyasa take jin Unaisah fiye da sauran yan uwanta da ta fara sani kafin ita.

Bazata iya jure fushi da ita ba, A hankali ta cire hannu ta mi
a mata, Jikin ta har kerma yakeyi gurin Zura hannunta a cikin na Batool, ta janyo ta, ta mike tsaye suka yi hugging din juna.

Lallashin juna sukayi tare da ba juna hakurin sabanin da suka samu.

"Zan fada maki abun ki ke son ji, daga yanzu babu boye boye atsakanina da ke, sirrina naki ne.."
ta fa
a yayin da suke raba jikinsu daga juna, cheeks dinsu sunyi ja saboda kukan da suka sha.

Ruko hannun Batool tayi suka zauna kan tattausan rug din dakinsu suna fuskantar juna, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin kunyar Batool, tayi mata
warjini ko dan yau tayi gaba da gaba da ita.

Lumshe idanunta tayi a hankali
In a cool voice tace"a duk lokacin da kika ganni ina kuka, to na tuna da shi ne, wallahi shine silar halin da nake shiga! nayi iyakar
arina dan ganin na daina tunaninsa sai dai nakasa, Ya mutu amma babu abun daya sauya na daga son da nake masa"!

Nan ta ke Batool ta gane wa take nufi.

"akwai wasu kalmomi daya furta min kafin su tafi kai farmaki sun tsaya min araina! da su nake kwana da su nake ta shi araina, nayi nayi in cire gur6ataccen tunaninsa da nake yi amma nakasa, zuciyata takasa mantawa da cewa shi fa yanzu mamaci ne ba rayayye ba, meyasa take tsananta min akan shi.."
wasu zafafan hawaye ne suka wanke fuskarta..

Ruko hannayenta Batool tayi a cikin nata, wani irin tausayin ta ne ya mamaye zuciyarta, tayi zaton Unaisah ta daina son shi tun da baya araye ashe har yanzu da son shi sosai a cikin zuciyarta.
shiru tayi tana tariyo kalaman daya fa
a mata a cikin brain dinta, a ranar da zasu tafi kai farmaki lokacin daya yi mata ra
a a cikin kunnanta..
_Unaisaah, my desire for you burns fiercely,Taking your virginity has become my utmost dream, For what feels like an eternity, I've been tormented by my longing for you, I've concealed it for your sake, but my craving for you only intensifies_
_I'm patient, Unaisah, not wanting to rush or harm you, I yearn to make love to you with your trust, your consent, I don't mean to pressure you, I simply can't wait to be with you_
_When I return, grant me my heart's desire, Unaisah.

Fulfill my wish, And let's create a memory that will last a lifetime_
kifa kanta tayi saman kafa
ar Batool, cikin karyayyar murya ta furta"a lokacin daya furta mun kalaman nan, duk da bakomai na fahimta ba, amma naji wani bakon abu da ban ta6a jin shi ba a tare da ni..."
ta fada tana jan numfashi, gaba daya tausayinta ya kama Batool
_"Daga baya, na zauna nayita yin nazari akan kalamansa, na yi bincike ta hanyar wayana akan abun da ban fahimta ba, har saida na gano komai dayake nufi, i was shocked, Danish da baisan komai ba, tayaya ya samu ilmi kan abun da ni bansani ba, ko Aunty ummi bakomai take fayyace mana ba, saboda tana jin kunyar mu.
shafa bayanta Batool tayi da tafin ta"mutuwa tayi min yankan kauna, naso ace na cika mashi burin shi akaina, sai dai Allah baya barin wani dan wani yaji dadi, ina daurewa ne idan kewarshi ta addabe ni, bana bari kowa ya sani, saboda abu biyu, bana so na fama ciwon Zuciyata saboda inason na rayu ko dan na ga
arshen Elders, sannan bana so in
aga hankalin ku, gaba daya na hana kaina kallon hotunansa da vidoes din da nayi masa wasu ma batare da sanin shi ba, saboda yanayin da nake shiga idan ina kallon su, da ace idan na bishi zamu rayu a kabari daya ne da ba abun da zai hana in roki Allah ya dauki raina nima, amma bana fatan hakan saboda a duk lokacin da na farka yin nafilfili nayi masa addu'a inajin wani dadi a cikin zuciyata"_
Lallashinta Batool ta cigaba da yi gwanin ban tausayi, a yanzu ta fahimci wasu abubuwan tanayi ne saboda ta kawar da damuwar rashin Danish.

"Yanzu da na fa
a maki sirrina sai naji kamar an yaye min damuwana, musamman da kika kwantar min da hankali, pls amana ne atsakanin mu, daga ni sai ke, kema idan akwai abunda ke damunki ki fada min.."
murmushi suka sakar ma Juna.

"Kada ki damu, zan fada maki nima, amma ayanzu bani da wani sirri daya wuce in taimaka maki gurin ganin mun shawo kan matsalar da ke damun ki" ta fada tana shafa sumar kan ta.
sun jima suna tattaunawa, fira tayi dadi, har saida cook yayi knocking Ya sanar da su su fito su ci lunch din su tukunna suka tsagaita.

Phone box din ta dauko ta mika ma Batool, Wani uban tsallan farin ciki ta daka, hada yin sujudusshukr saboda dadin da taji, hakan ba karamin nishadi ya ba Unaisah ba, ganin ta sanyata farin ciki.

"Ki yi hakuri tuntuni Yakamata in baki ita, sai dai banyi hakan ba saboda Sajeed ya nuna yanaso yanzu da baya nan gayanan na baki, kiyi ma daddy magana ya siya maki sim"
tana faman washe baki tace thank you sis, you're special, kin faranta min rai
atare suka bu
e kwalin wayar, sabuwa gal da ita
irar Samsung galaxy,
"Nasan yau dakyar zaki Iya runtsawa" tana dariya tace "kamar kin sani"
"Kije ki sanya kaya, zan jira ki"
Ta fada tare da ruke mata wayar, da sauri ta nufi closet dinsu, shaf shaf ta zura gown a jikinta, ta dawo.

"muje muyi lunch daga nan sai mu kira yan uwan mu mu gaisa da su ko"
"Yeah" da farin ciki suka fito daga dakin.

A dining room suka taras da Cooks dake jera masu kayan lunch din su, bayan sun zauna kan kujera suna fuskantar Juna, a tsanake suka soma cin abincin su.

"Har yanzu shiru, aunty Ummi bata dawo ba, gidan duk ba dadi, babu Aunty Ummi, Chief tun safe bai dawo ba, daddy ma ya fita anguwa, sai mu kadai, nayi kewar su" Batool ce ta fada yayin da take tura Steak kebab abakinta tana taunawa.

"Idan muka kammala Cin abincin zan sake jaraba kiran su, Inji yaushe zasu dawo gida"
Unaisah ce ta fa
a tana tsoma hannunta cikin plate din gabanta dake a shake da farfesun ganda mai zafi da tafshi, daukowa tayi tare da turawa abaki tana taunar gandar.

"Kwanakin baya kin yi min alkwarin zaki bani labarin aunty Ummi, har yanzu ban manta ba, Inaso naji..."
dakatawa tayi da sharbar farfesun ta danyi shiru tana yanke shawara da zuciyarta, Chief ya hana ta fada amma kafin ya garga
eta akan kada ta fa
a ta riga tayi wa Batool al
awarin zata bata labari, kuma tasan in har bata fada mata ba, zataji ba dadi.

Dagowa tayi suka hada ido cikin na juna, ta kura mata idanun ta..

"Ki bari mu gama cin abincin mana"
Girgiza kai tayi"haka kullin kike kawo uzirin da zaisa ki manta, kawai ki fada min a yanzu.."
Saboda gudun 6acin ranta yasa tace "Okay, zan fada maki amma pls, amana, daga ni sai ke my sis" murmushi Batool ta saki taji dadin maganarta..

"In sha Allah.." a tsanake Unaisah ta fara labarta mata tiryan tiryan kamar yadda ta saurara a audio din da Chief ya kunna mata.
tunkan takai karashen labarin Idanun Batool suka cicciko tab da
walla cikin sanyin murya tace"sai yanzu na gane meyasa aunty ummi kuka rannan, nayi zaton ni Batool din take fadin ta rasa na mutu ashe bani bace, sunan babynta ce data rasu, na tausayawa aunty Ummi da uncle Shureim, labarinsu ya taba zuciya ta, ashe sheikh Imam ne mahaifinta amma meyasa ya yanke mata hukunci cikin fushi?

Ta fa
a fuskarta babu walwala..
Chapter 77 · 0% Book details