← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 201

Sashe 60

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har tsawon mintuna ashirin cuf babu wanda ya furta kalma daga cikin su saboda matsananciyar damuwar da suka shiga, kwata kwata meeting din yau bai yi musu dadi ba, saboda jin abun da basu taba zata ba, basu ji dadin maganganun da suka fa
a akan kakansa ba, wannan ne karo na biyu da suka ga raunin Chief, ranar da Danish ya fa
a rijiya da kuma yau, wlh sun tausaya masa sosai, sun ma ga kokarinsa da ya iya jurewa in wani ne tuni zuciyarsa zata buga ya mutu ko ya halaka kansa saboda ba
in ciki..
ewa Commender ya yi ya nufe shi tare da ru
o hannunsa ya juyo da shi, hankalinsu ya tashi da ganin siraran hawayen dake zarya kan kuncin sa.
_Zaunar da shi kan kujera Commender ya yi, tare da zaro Hanky ya share mashi
wallar shi, mikewa sauran suka yi gaba
aya suka kewaye sa duk da raunin da suka yi hakan bai hana su
arfafa zuciyarsu gurin lallashin shi da bashi baki akan
addarar data same su, babu wanda bai tofa albarkacin bakinsa ba gurin kwantar masa da hankali, su ka ce ya yi hakuri ya jure rada
in da ya ke ji, sun san abun da ciwo, dole zai shiga mawuyacin hali amma ya yi hakuri, kada ya ji komai su masu fahimtar shi ne, tabbas su kansu sun karaya sun kuma razana da jin cewa kakansa ne, amma ya zasu yi babu wanda ya isa ya canza abun da Allah ya riga ya kaddara faruwarsa, wlh saboda tausayin da ya basu da suna da halin da zasu cire mashi damuwar shi da ba abun da zai hana su yi hakan kodan su sau
a mashi radadin da yake ji, amma ba zasu bar shi ba, zasu kasance a tare da shi, No matter what, shi Chief dinsu ne na har abada, su sun yarda da shi fiye da yadda suka yarda da kansu, don haka kada ya ji komai, laifin kakansa ba zai taba shafarsa da ahlinsa ba, zasu tsaya masu tsayin daka don ganin basu tozarta a idon duniya ba, bashi kadai zai yi fadan ba, ya sani yana da su zasu taya shi yin fighting
in duk wani wanda yayi yunkurin cin zarafin ahlinsa ta hanyar amfani da abun da kakansa ya aikata!

Bayan haka basu san rauninsa, yana
aga masu hankali, abun da suke so da shi ya yi
arin cire damuwar da ke aransa, saboda zata iya haifar masa da rauni wanda kuma hakan faduwa ne a gare su, sun san Chief
insu jarumin namiji ne, mai dakakkar zuciya, kuma mai tawakkali, basu so ya canza daga yadda ya ke a da, ya sawa ransa cewa zai iya, ya manta da cewa kakansa ne Elder, ta haka ne zai kore damuwarsa har su samu su
arasa aikin su."_
Maganganu masu da
i da
arfafa gwiwa suka gaggaya masa har saida
ya ji karfi a jikin shi, sun faranta ranshi, kuma dama abun da ya kamata kenan idan mutun ya shiga wani hali a tausaya masa, a ja shi a jiki, bawai a dinga cuzguna masa ba saboda wata
addara ta same shi, wasu har da
i suke ji su dinga bullying
inka don su ba
anta maka rai, su ja depression ya kama mutun daga haka har ya lahanta kan shi, wa'iyazubilla..

Tun suna share mashi
wallar da ke gangarowa kan kuncinsa har ta kai ga sun fara tsokanar shi, baisan sa'adda ya fara sakin murmushi ba, saboda dadin da ya ji har godiya ya yi musu, su ka ce kada ya damu hakkinsu ne su bashi kulawa, yanzu tunda sun fahimci ba ya jin dadi yana bukatar ya ga likita saboda lafiyarsa, don haka zasu
aga meeting din, zuwa lokacin da zai ji sau
Ya ce masu bai
i shawarar su ba, amma bazai yiwu a
age meeting ba, akwai muhimman abubuwan da yakamata su tattauna akai idan ba haka ba zasu iya fuskantar matsala, hankalinsu ya tashi da jin hakan, suka ce tun da haka ne, zasu tafi hutun awa uku saboda sun damu da lafiyarsa suna so ya huta...

A cikin yan mintuna suka kira Isod docs suka bincika lafiyarsa anan cikin medical room
in su, bayan sun tabbatar da ciwon dake damunsa ya garga
e su akan kada su fa
a musu sakamakon saboda baya son kowa ya sani...

Lokacin da suka koma zaman meeting din, ba laifi sun ga ya
an saki jikinshi da walwala akan fuskarsa, A tsanake ya fayyace musu komai da ya faru bayan zuwan Khala..

Sun yi matukar mamakin jin cewa kakarsa ce, kuma Obie ne ya yi
aryar mutuwarta ya kai ta kurkukun kaddara, duk ba wannan ba, abun da ya basu haushi da takaici abun da Pravin ya aikata, ashe shima
Elder ne na gidan kurkukun kaddara, lallai Obie Family sun ha
a giggan
an ta'adda acikin su.

Bayan sun taya shi murnar ganin grandma
insa, da jimamin abun da ya faru da familyn sa Commender James ya ce,
"Yanzu ta ya za'ai mu iya gano sauran Elders?

Kana ganin grandma
inka zata iya samun sau
i nan kusa!" Girgiza kai ya yi, "Bakowa ta sani a cikin su ba, yanzu haka da ita da aunt
in nawa an kwantar da su asibiti basu san inda kansu yake ba, amma suna samun kulawar likita.."
"Me zai hana mu tuntubi shi Elde...Au, afwan sir grandpa nake so na ce,..." murmushi chief ya yi tare da kallon CI da ya yi maganar.

"Duk yadda ma ka fa
a daidai ne CI, already na yi masa magana akan ya fada mun sauran Elders din amma ya
i sanar da ni...." Nan ya labarta musu abun da suka tattauna tsakaninshi da baba Obie.

Kallon kallo suka jefawa junan su cike da tashin hankali, Agent Jabeer Osman ya ce, "Akwai sauran rina a kaba kenan, In har bamu yi gaggawar kamasu ba zasu iya mayar da hannun agogo baya, nasan iwar haka suna nan suna shirin kawo mana farmaki."
Gaba
aya sunyi amanna da maganarsa, Agent Zahra ya ce, "Ni damuwana ina zasu farmaka? ya tambaya yana duban su,
"Hankalina ya fi karkata akan fursinonin da muka baro a Csh."
Taj ya ce,"Asibitin yana da tsaro tunda na sojoji ne, amma fa kada mu dogara da hakan, mun riga da mun san su wanene Evil Giants, in har suka farmake mu da su, toh Allah ne ka
ai zai iya
watar mu, za su iya amfani da sihiri su kashe sojojin dake tsaron su, su kwashe yaran abunda ba a fata, amma menene mafita...?"
gaba
aya suka zurfafa tunaninsu kowa na tunanin abun da yakamata a yi.

"Kuskuren da muka yi tun farko shine barin makaman da grandma ta bamu, da mun sani mun taho da su, saboda da su ka
ai ne za'a iya ya
ar su.."
A cewar Captain..

Cike da takaici Canal ya daki gaban table dinsa yama rasa abun cewa..

Jackson ya ce,"Akwai gagarumar matsala, dole fa mu fara kai masu farmaki kafin su kawo mana idan ba haka ba, ba zasu yi mana da dadi ba, bamu san ina zasu farmaka ba!"
Lieutenant Thompson ya ce, "Ni dai a nawa ganin shawara
aya ce, Chief grandpa shine mafita, shi ka
aine makamin da muke da shi a yanzu, tun da ya ce zai mika wuya toh ya taimaka ya fa
a mana komai idan ba haka ba, ba zamu iya cin galaba a kansu ba, a kowani lokaci zasu iya kawo mana farmakin bazata..."
Girgiza kai Chief Owais ya yi, "mu yi hakuri mu nemi wata mafitar, saboda ba irin magiyar da ban yi masa ba amma ya
i fada mun, ya ce a dokar aikinsu wani baya tona asirin wani, alkawari ne suka
aukarwa junansu, kuma shi ba zai ci amanarsu ba, tun da har ya fadi hakan bai duba
aunar da yake yi mini ba, toh wlh ba zai ta6a bamu hadin kai ba, koda zamu azabtar da shi ne, amma a maganarsa ya ce in har aka kawo mana farmaki mu sanar da shi, amma wannan ba mafita bane, tayaya za a yi mu san za'a kawo mana farmakin?"
Da damuwa ya jefa musu tambayar, gaba daya sun shiga tashin hankali..

"Ni a ganina mu fara nemo wadanda grandma ta fadi sunayen su?

In ya so sai muci ubansu mu azabtar da su har sai sun fa
a mana su wanene sauran Elders din..." Taj ne ya fada yana huci zuciya ta kai wuya..!

General Noah ya ce, "No ba zamu iya kama su ba, har yanzu bamu da isassun hujjojin yin hakan!"
"Sir, muna da isassun hujjojin da zamu iya kama su..."
Gaba
aya suka maida hankali akan Taj da ya yi maganar har suna ha
a baki gurin tambayar wata hujja ce?

Bai jira Chief ya bashi umarnin ya fa
a ba, ya fara zayyana musu komai da ya faru tun daga kan labarin Ummi har izuwa labarin da Benazir ta bashi akan Alhaji Musa.

Lamarin ya
aure musu kai, basu gama shan mamaki ba, sai da Chief ya samu
warin giwar tunawa da wata hujjar da yake da ita, nan shima ya labarta musu komai da ya gano game da shi tun daga kan hotansa dake a cikin diary din Unaizah, ya
ara da cewa, "Har yanzu bai rabu da Ummi ba, bayan ya rabata da kowa nata ya maidata karuwarsa, shine ya tafi da ita America..." A rude U.s armies suke jefawa junansu kallo mai cike da tsantsar al'jabi, Ummi dai da suka sani tantiriyar karuwa yau sun ji asalin labarinta da kuma azzulumin da ya yi silar canza rayuwarta, gaba
aya basu ji da
in abun daya faru da ita ba, tausayinta ne tsantsa a kan fuskokinsu, ba su ka
ai ba hatta General Noah dana hannun daman Chief sun nuna tausayawar su a gare ta, labarinta ya taba zukatansu, kuma basu taba ganin mugun mutun irin Musa ba, labarin yarinyar da ya sa su zubda
walla ashe shine Ubanta, sun ma riga da sun yanke ma kansu shine JAN WUYA mutumin da suke nema ruwa a jallo..

Chief Owais bai dakata ba, ya
aura da basu labarin da Sheikh Imam ya ba shi ...
Chapter 60 · 0% Book details