← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 201

Sashe 89

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan nafi kowa sanin wacece
ata, Aisha, bazan iya misalta maki mawuyacin halin da na shiga ba bayan dana neme ki na rasa, na yi kukan da ban ta6a
insa ba arayuwata, na tsani kaina, na
untata rayuwata, na ji rayuwar duniyar ma ta sire mini, mutuwa nakes o kawai na yi, Aisha gidan mahaukata ne kawai ban je ba, amma na yi haukan rashin ki, har kulle kaina na yi tsawon kwanaki ba asan inda nake ba ba ci ba sha, na yi rashin lafiyar data yi silar kwantar da ni asibiti, na yi jinya kamar bazan rayu ba, bansan wa ke akaina ba, saida ta kai ga sunanki ka
ai nake fada a cikin sambatuna, Aisha yanzu haka da nake maki magana ina da ciwon zuciya, Allah ne bai
addara zan mutu ba, shiyasa na kawo har wannan lokacin a raye..."
Shesshekar kukan Benazir da Anila ne ya cika kunnuwan kowan nan su.

"Aisha ban manta dake ba, da ke nake kwana da ke na ke tashi araina, addu'ar da nake maki kullum a cikin sallata ban daina ba, kamar yadda ki ke sa ran zan neme ki nima haka nayi ta sa ran wata rana zaki dawo ki neme ni, amma baki ta6a tunanin kiyi hakan ba, shiyasa zuciyata ta karaya na yi tunanin ko kin mutu ne ko kuwa abun da na yi maki ne yasa baki ta6a nema ba..." Ya
an dakata yana mayar da numfashi.

"Bani da kwanciyar hankali saboda zullumi da fargaban a wani hali kike a ciki, kullum saina kira layinki amma ban ta6a samun shi a kunne ba, kuma ban fidda rai ba, kullum addu'ata idan kina a raye keda jinjirarki Allah ya kare mun ku a duk inda ku ke, Ya zama gatan ku, Ya kuma ha
a ni da ku, idan kuma baku a raye Allah Ya jikanku da rahamarsa, ban ta6a gajiyawa ba da neman ku, saboda ku na sha zuwa aikin hajji don in yi maku addu'a..."
Kasa karasa maganar ya yi saboda raunin da zuciyarshi ta yi, baiwar Allah ta yi kuka kamar ranta zai fita, bata taba tunanin ya damu da ita har hakan ba, ta yi zaton yana sane ya yi watsi da ita shiyasa bata ta6a tunanin ta dawo gida ba tun da bai neme ta ba, ta yi zaton har yanzu fushi ya ke yi da ita.

Tallabo fuskarta ya yi da tafukan sa, idanunsu da ke tsiyayar da kwalla suka ha
u cikin na juna.

"Aisha, saboda ke na ajiye aikina na rabu da kowa nawa, a karshe ma da na yi jiran shiru baki dawo ba, sai na bar
asar ba tare da sanin kowa ba."
Numfasawa ya yi tare da girgiza kansa cike da danasani ya daura da cewa, "A ranar dana fara ganin ki a gidan nan, wani irin farin ciki mara misaltuwa na ji, kamar anyi min albishir da gidan aljanna, saboda na ji da
in ganinki da ranki da lafiyarki, duk da na shiga tashin hankali saboda sauyin da na gani a tare dake, daga yanayin shigarki, na gane kin canza hali, har saida na yi kokwanton anya Aisha nane?"
Amma saboda jinina dake yawo a jikinki yasa ban musa ba, a lokacin dalilin da yasa ban yi ma ki magana ba, saboda ina jin kunyarki, kema kuma sai kika nuna kamar baki taba sanina ba, shiyasa jikina ya yi sanyi, amma bayan na koma gida saboda farin ciki ban iya runtsawa ba, kwana na yi ina nafilfili don nuna godiyata ga Allah da ya bayyanar min da ke, har so nake Chief ya gayyace ni don in zo gidan nan saboda kawai zumudin in ganki..

"
komai saida Imam ya fayyace mata na daga halin da ya shiga bayan rabuwar shi da ita.

Bai
are maganar ba, Ya saki fuskarta da ya tallabe, ya tattare
asan jallabiyar Jikin shi da niyar ya zu
unna kan gwiwowinsa don ya nemi yafiyar ta.

Lura da hakan yasa ta yi saurin
ame shi tana rokonshi akan kada ya zu
unna mata, ya bari, kada ya yi, idan ma akwai wanda ya cancanta ya nemi yafiyar wani atsakanin su toh ita yakamata ta nemi yafiyar sa, yana kuka ya ce mata ta barshi ya zukunna, idan har baiyi hakan ba bazai ta6a yafe ma kansa ba, koda ta yafe masa, saboda ya dade yana yi ma kanshi kallon mugun Uba, mara imani, saboda rashin adalcin da bai yi mata ba.

Ta fashe da wani sabon kukan ta ce, "Baba babu yafiya atsakanin mu, abun da ya faru bayin kanka bane, haka zalika abun da ya faru tsakanina da yaya Shureim bayin kan shi bane, a yau na ji komai baba.

Na ji abun da ya
aga hankalina ya kuma karya zuciyata, Baba ashe dama makirci ne aka kulla min saboda a
auki fansa akanka?"
Kaitsaye maganar ta ratsa kunnuwansu, a ru
e suke kallonta.

Muryarsa na rawa ya furta, "Bangane me kike nufi ba? ki yi min bayani yadda zan fahimta!"
Gajiya ta yi da tsayuwa, hakan yasa ta zauna shima ya zauna yana fuskantarta, yayin da sauran mutanan dake a falon suke atsaitsaye babu alamun gajiya a tare da su.

"Ke nake sauraro Aisha.." A
agare da son ji duk da yana fargaban abun da ya da
e yana zargi ya zamana gaskiya.

"Baba, zan fa
a maka, amma zan roke ka, dan Allah ka yi min alkawarin zaka jure komai da za ka ji daga gare ni, kuma duk abun da zan fa
a maka ya riga da ya wuce, kuma anyi ne don a cusa maka ba
in cikin da zai yi silar mutuwarka, sannan kuma a lalata martabarka da
imarka, in har ka tada hankalinka akan abun da za ka ji toh zai yi nasara ne, shiyasa bana so ka sanya damuwa a ranka, nasan za ka ji ra
in da yafi na
unar wuta zafi a cikin zuciyarka amma ina so ka tuna komai ya faru a rayuwar mu mukaddari ne daga Allah, ka
auki hakan a matsayin jarabawa da Allah ke yiwa bayinSa muminai, mu yi hakuri da cutarwar da aka yi mana, In sha Allah zamu ga ribar hakurin da muka yi, kuma Allah zai yi mana sakayya"
Cikin sanyin murya ta
arasa maganar tana kallon fuskar mahaifin nata dake kallonta da rinannun idanunsa.

Unexpectected ta ji ya furta, "Musa!"
kowa da ke a falon sai da gabansa ya fa
i da jin sunan da ya ambata.

Ba ta yi mamakin Jin ya canki sunan shi ba, dama tasan dole ya zo masa a rai tun da shine babban ma
iyinsa a duniyar nan.

"Ki fa
amin shine ko?

Shine ya shiga tsakanina da ke ko?" Cike da damuwa ya tambaya,
Fargaban amsa mash
i ta ke yi saboda zullum halin da zai shiga, tasan mahaifin nata da zuciya komai zai iya faruwa.
yar ta jinjina mashi kai cikin raunanniyar murya ta ce, "Shine baba, uncle Musa, ya da
e yana
ulla makirci atsakanin mu, ban ta6a ganin azzalumin mutun irinsa ba, ya karya mini zuciyata, ya ha'ince mu, wata shari'ar sai a lahira, amma ya cutar da rayuwar mu..."
kamar a mafarki suke sauraron maganar Aisha, gaba daya sun kasa tantance wani Musan take magana akan shi, Taj ne ka
ai ya san komai, sai kuma Benazir da Anila.

Sauran da ke a falon sun ru
e sosai, sun rasa gane inda ta dosa.

"Aisha kada ki ji komai, ki fadamin kawai, bazan karaya ba, nasan zai aikata saboda ya kullace ni a ranshi, dama ni saida na yi zargin dasa hannunsa a cikin abun da ya faru, kawai don bani da hujjar da zan tuhume sa ne.."
ya fa
a cikin karfin hali kamar zai iya jurewa.
arasa shiga cikin falon suka yi, saboda su samu damar jin komai, a saman sofas kowan nan su ya samu wuri ya zauna suka nutsu suna kallon Aisha da baba Imam, kwata kwata basu san da zaman su ba, saboda hankalinsu ba akansu yake ba, basu san ma sun shigo falon ba.

Numfasawa tayi cikin karyayyar murya ta soma zayyana masa komai da Uncle Musa ya fa
a mata, tiryan tiryan abu
aya da ta boye masa saboda gudun halin da zai shiga, shine karuwancin da ta yi a America da kuma haramtacciyar ala
arta da Musa tasan in ya ji wannan komai zai iya faruwa ita kuma ba ta so Musa yayi nasara akan mahaifinta, ta dai sakaya ta ce shi ya kaita America ya
auki nauyin komai nata saboda ya kawar da tunaninta akan dawowa gida.

Tunkan ta
arasa labarta mashi Hajiya Layla ta mi
e tsaye tana tafa hannayenta a ki
ime take zabga salati, Alhaji Ubaid dake a zaune sai jinjina kansa ya ke yi yama kasa furta komai saboda
uncin da zuciyarshi ta yi mashi, ina ga Dr shureim dake neman zaucewa saboda tashin hankalin da ya haifar masa da ra
i mara misaltuwa a zuciyarsa, bai ta6a zaton Uncle musa zai iya yi masa haka ba, saboda yasan shi ya cutar da rayuwarshi shiyasa ya dawo da shi gidan shi da zama, haka lokacin da ya ke neman taimako yaita kiransa baya shiga ashe blocking
insa ya yi, kowa dake falon sai da ya razana ba ka
an ba, Musa ya karya zuciyoyinsu, basu ta6a tunanin shine munafukin da ke
ulla musu makirci ba.

Saboda bacin rai da fusata yasa shekh Imam zubda gumi akan fuskarsa, ba a ta6a cin galaba akanshi ba sai wannan karon, Musa ya cuce shi, wani laifi ya yi masa da yasa shi yanke masa mummunan hukuncin nan?"
Kawai saboda ya hana shi auran Aisha?

Saboda ba
in zalunci da rashin imani ya shiga tsakaninta da shi, yayi mata kazafi bayan ya shiga tsakaninta da Shureim, abun da yafi bakanta ransa tsawon shekarun da ya raba shi da
arshi, ashe yana a tare da ita, saboda zalunci irin na shi, yanzu ya gane komai da ya faru da Aisha shi ya ja mata, tun da akan shi yake
aukar fansa, bata ji ba bata gani ba.
Chapter 89 · 0% Book details