← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 201

Sashe 87

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya shureim!..." ba dan Benazir ce ta kirasa ba da ba abun da zai hana Yaki waiwayonta..

Juyowa yayi fuskarsa da fara'a ya ke duban ta, sanye take da kayan bacci riga da wando maroon tayi rolling headscarf, sai da ta matso kusa da shi Ya lura da wayar dake a hannunta, Fuskarta duk a yamutse.

Car key din hannunsa Ta kalla"ya shureim Ina za ka je da daren nan?

Ka duba lokaci kuwa?

Murmushi ya yi"Ki taya ni Murna Ukhtyna, Aisha ta kira ni yanzun nan awaya, tace tana son ganina, Inzo gidan dg"
aru
e ta furta"Aisha kuma?

Ya shureim yaushe aisha ta sauko daga kan dokin zuciyar da ta hau da har zata kira ka?

Ka kuwa duba kaga ita dince ta kira ka dagaske?

"Bakuwar Number ce amma Tabbas Aisha ne, Ni naji muryarta.."
"Muga number din" ta fada tare da mika masa hannu bayan Ya bata wayar ta dubi contact din nan take ta gane Number Taj ce.

"Yanzu Can zan tafi, tana jira na"
"Yaya shureim dagaske Aisha ce, number data kiraka da ita, ta Daddyn Unaisah ne amma meyasa take son ganinka a irin wannan lokacin?

Ta fa
a da rudu akan fuskarta.

"Kada ki tsayar Dani Benazir, ki bani kawai in tafi.." ya fada yana mika mata hannu..

Tana kokarin mika masa wayar, suka tsinkayi Muryar Mami a cikin kunnuwan su..

"Su wanene nan"?

Ta fada tana nufo su, atare suka dube ta, Damuwace ta bayyana akan fuskar Shureim har saida Ya harari Benazir ganin taja masa har mami tagansu yasan ba lallai tabar shi Ya fita ba.
arasowa tayi daga gaban su ta tsaya"meya ke faruwane?

Ina kuma zuwa?

Ta fada tana nuna key din hannun dr shureim..

Kamar marasa gaskiya sukayi shiru suna kallon kallon atsakanin su..

Hakan Yasa ta fahimci da akwai wani abu dake faruwa kuma basa son sanar da ita..

Har ta bu
e baki zata kuma yin magana phone ringing din Dr shureim Ya katse mata hanzarin ta, ganin number da Aisha ta kira ne yasa shi saurin yin picking..

"Ya shureim ka taimaka min ka zo, naji komai daya faru, bayin kanka ba ne, akwai abun da nakeso in fada maka dan Allah kazo, magana ce mai muhimmanci"
Waro idanu waje su ka yi gaba
ayan su sun ru
e sosai, daga mamin har Benazir din sunji komai, basu karasa jin
arashen zancen ba kiran ya katse..

Arude Mami Ta kar6e wayar shureim tadinga kiran layin ba'a dagawa, kallon su tayi cikin rudani tace"ku fadamin wacece wannan
in?

Meyasa take neman ka?

Akan me take yin magana? nasan kun sani, kada ku 6oye min ku fada mun kawai in ba haka ba zan sa6a maku.."
Ta karashe maganar kamar zata doke su..

Ran mami Ya 6aci jin sunyi shiru basu Bata amsa yasa ta daka masu tsawa"wai don ubanku ba zaku bani amsar tambayar da nayi maku ba?

So kuke ku haukatani ne..." cikin rawar murya Benazir ta ce"aisha ce mami, kiyi hakuri mun boye maki, amma Aisha ce, tana agidan Dg, Kuma Yarinyar nan Azeezaty, bakowa bace face Unaisah
ata Angel, mahaifinta kuma shine Taj mijina...."
wani faduwar gaba Mami taji, sai zare idanu takeyi saboda al'ajabi..
e Hannunta Benazir tayi"mami zanyi maki bayanin komai, mu ma bada son ranmu muka 6oye maki ba, Dg ne yayi mana warning akan karmu sanar da kowa game da su saboda Rayuwarsu tana acikin hadari, bazai yiwu a yanzu in fayyace maki komai ba, amma dan Allah mami kuzo mu tafi can gidan, zaifi mu hadu mu duka kowa yaji komai dake faruwa, Saboda Inaji araina Akwai wani abu dake faruwa shiyasa Aisha takira shureim ta nemi da ya je, kuma dama suna bincike akan case din daya shafe mu da kuma shi Taj din..."
Cike da zumu
i Mami Tace toh, bari in
auko hijabi
Cikin sauri Ta nufi daki, tana shiga ta taras da Alhaji Ubaid Yana kokarin fitowa daga toilet, koda ya tambayi daga ina take?

Tace mashi Ya biyota kawai su tafi, akwai wani babban al'amari"
Badajimawa ba, sai gasu sun fito tare da Alhaji Ubaid din, sai tambayarta yake ina za su je cikin daren nan? tace mashi Yabi su kawai in sunje zai gani, da yaga Benazir da shureim Hankalinsa Sai ya kara tashi, bai dai tambaye su ba, yabi bayan su Suka fito daga Falon, Cikin sauri suka nufi Parking space, gaba dayansu a motar Dr shureim suka zauna, Hajiya Layla da Alhaji Ubaid suna a backseat, Benazir tana a front seats tare da Dr shureim.

Key ya yi ma motar, tare dayin riverse Ya nufi Gate, sam Sun manta da Security Officers, aikuwa suna hango motarsu suka Tunkareta gadan gadan..

Hajiya layla tace karya kuskura ya tsayar da motar zasu 6ata masu lokaci
arshe su hanasu fita, tun da gate din a bu
e yake da alama wasu ne suka fita aka bude ba a kaiga rufewa ba ya fuce da su kawai.

Alhaji ubaid yace kada ay haka su bi komai a sannu.

Dr shureim dayafi su zumudi ya kure speed din Motar, Gadan gadan Ya nufi Security Officers din kiris Ya rage Yabi takansu da mota Hakan yasa suka dare tare da bashi hanya, Ya ba motarshi Wuta Ya kara gaba.

Wasu daga Cikin Security Officers din Har bin Motar shi su ka yi sai dai tuni sunyi musu nisa.

Sai da ya tabbatar da sun 6ace masu sannan Ya rage gudun Motar.

Wayar Benazir ce ta soma ruri cikin sauri Ta duba Mai kira ganin Anila yasa ta yi picking tare da kara wayar a kunne
Tana niyar yi mata sallama kukan Anila Ya katse ta,
Arude Ta furta"Anila?

Meya faru?

Meyasa kike kuka"?

Maganar da tayi ne ta karkato da hankulan su Hajiya layla ga kallon su.
da wata irin raunanniyar Murya ta furta"Benazir, Muna cikin tashin hankali, Uncle Ya kashe ta, mun ga gawarta, yanzu haka da na ke yi maki magana gidan mu a kewaye ya ke da sojoji"
Dafe kirji Benazir tayi"Inna Lillahi wa'inna ilaihirraji"un..."
"Menene?

Meya faru?

Benazir meke damun ta ne?

Me ta fada maki"?

Su mami ne Suke ta tambayarta Cikin rudu..

"Bani kadai bace Anila, Ina atare da su mami, Yanzu haka Muna akan hanyar zuwa gidan Dg, Aisha ce ta kira ya shureim tana kuka ta bukaci tana son ganin shi ina tunanin wani abu yana faruwa acan, in ba damuwa mu ha
e acan.."
Ta amsa mata da toh
Bayan tayi rejecting Call din ta dubi Dr shureim da ke kallon ta kafin ta mayar da dubanta ga su mami da ke abaya.

"Anila ce, ta fada min wani abu ya faru agidansu, bana iya jin me take cewa kamar kuka takeyi, Amma nace mata mu hadu a gidan Dj nasan zata zo"
Cike da fargaba suka amsa mata da toh kowa da abunda ya ke sa
awa A cikin ran su..

Lokacin da motar su ta haura kan Titin Obie Estate, Cikin sauri Benazir ta kira layin taj, bayan yayi picking ta fada mashi game da zuwan su, tace ya taimaka yayi masu hanyar da zasu shigo cikin sauki, ya ce mata kada su biyo ta gate din gaba, su shigo ta gate din baya na estate din, zai sanar da securies din.
sallama su ka yi da shi, bayan ta fada ma dr shureim abun da ya ce, Ta yi shiru zuciyarta cike fal da fargaba, Muryar Taj da taji ta daga hankalinta kamar baya a cikin nutsuwar shi.
ta gate din baya suka shiga Estate din basu sha wahala ba, saboda already Taj Ya sanar da securities din game da zuwansu..

A parking Space dr shurem ya yi Parking din Motarsa.

Bayan sun fito, Hajiya layla ta dinga jinjina kanta, ganin haduwar tamfatsetsan Gidan dg, tayi zaton daga gidan Alhaji musa an gama Gini mai kyau a Abuja sai yau da Allah Ya kawota gidan Chief.

Shi Kanshi Alhaji Ubaid Ya jinjinama haduwar Villa din..
dr shureim ne ya fara yin gaba jikinsa sai tsuma yakeyi saboda zumu
i, da sauri suka Bi bayan shi.

Basu kaiga
arasawa ga Kofar Ba, Horn din mota Ya katse masu hanzarin su, sunyi tunanin su Anila ne Hakan Yasa suka dakata tare da juyawa suna kallon Motar da ke shigowa da matsakaicin gudu ta nufo Entry Hall sai da takusa
arasowa inda suke suka ga gudun nata Ya ragu slowly ta yi Parking daga gefen su.

Gaba
aya suka kura idanu suna jiran ganin wanene zai fito daga cikin Motar.

Lokacin daya bude cardoor din Ya zuro kofarsa basu gane wanene ba amma daya karasa fitowa gaba daya suka Zare idanun su, Har suna hada baki gurin furta"Sheikh Imam Malik..."
kwata kwata baisan da zamansu ba, Har saida suka ambaci sunanshi tukunna ya lura da su.

A hankali ya
aura idanunshi akan fuskokinsu, Mutanan da har abada bazai ta6a mantawa da irin Butulcin da su ka yi masa ba, Tsantsar mamaki ne akan fuskokin kowan nan su daga shi har su din sun kasa motsawa.

Tun Lokacin da suka samu sa6ani Yau kimanin shekara goma sha takwas da zumuncin su Ya yanke basu kara haduwa ba kuma babu wanda ya nemi wani, sai yau da su ka yi ha
uwar bazata cikin ikon Allah agidan dg.

Wani irin nauyin shi da kunyarshi ne Ya lullu6e su,
Hajiya layla ji tayi kamar ta ha
a kasa ta binne kanta saboda kunyar Imam malik, duk tasha jinin jikinta, Saboda Kunya yasa ta dinga kare fuskarta da kasan hijab din ta.

Alhaji Ubaid kuwa Kasa jure hada idanunsa yayi dana sheikh Imam, wani irin kwarjini yayi masu.

A hankali Yake binsu da kallo mai wuyar fassaruwa..

Kamar yadda suke mamakin ganin shi haka shima Yake mamakin ganin su, komai daya faru arayuwar su suka soma tunanowa kamar a yanzu yake faruwa, ba zai ta6a mantawa da rashin mutuncin da sukayi mashi ba, ganin su da ya yi sai ya zamana kamar sun fama raunin dake a acikin zuciyarsa ne.

Kallon kallo su ke jefawa junan su, dr shureim da Benazir sun yi zuru da idanu kamar wadanda suka ma sarki Karya fadawa suka turke su.
Chapter 87 · 0% Book details