← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 201

Sashe 23

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da budar bakin Unaisah sai cewa tayi"Anya, kamar nawa ne ni kadai, amma kada ki damu zamu dinga sanyawa atare, ai abuna naki ne"
mood din fuskarta kamar bataji dadi ba, in a cool voice tace"a'a ni bazanyi amfani da su ba, naki ne saboda ke ya siye su, kada ki damu..."
ta fada tare da saukowa daga kan gadon, ruko hannun ta Unaisah tayi"meya faru ne naga kamar bakya farin ciki"?

Murmushi ta kakalo kan fuskarta"don't mind your self, Am ok, inaso zan je dakin Aunty Ummi"
tana
arasa maganar ta juya ta fuce daga
akin, Unaisah bata kawo komai aranta ba, ta maida kayan cikin akwatin kafin ta datse shi tare da ruko handle dinsa, ta sauko ta fito daga dakin ta nufi dakin Aunty Ummi.

UMMIN AMERICA
Fitowa tayi daga Toilet jikinta sanye da bathrobe, wayar ta dake akan gado sai ringing takeyi, da zarar kiran ya katse wani ke shigowa.

Hararar wayar tayi bata da niyar daukarta.

Sai da ta gama shirya kanta cikin Jallabiya, kafin ta dauki wayar tare da yin picking ta kara a kunne.

Kakkausar muryarsa ce ta ratsa kunnanta " Ummi, why haven't you been answering my calls for two days?

I've even sent you
messages, but you didn't respond."
Batasan ya akai ta tsanci kanta da jin haushin shi ba.

"Bana jin dadi ne, wayar ma ban san inda na jefa ta ba, sai yau na dauko ta"
"Okay, ya jikin naki"
"Da sauki"
"Inason ganin ki, zanzo da anjima.."
bai
are maganar ba ta katse shi da cewa"Sorry, basai ka zo ba, ka bari idan na samu time zanzo gidan ka"
muryarsa da mamaki yace"Ummi kin canza min, wani abu ya faru ne"?

"A'a ba abunda ya faru, kawai bana so kazo nan dinne,"
"Okay.." ya na fa
a yai rejecting call
nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, har zata aje wayar saiga kiran dr shureim ya shigo wayar, tun shekaran jiya da suka zo yake ta kiran ta, sau daya ta taba picking tana jin muryar shi ta katse kiran amma tayi saving contact dinsa.

A kalla tana da missed calls dinsa kusan dari da hamsin, daga shekaran jiya izuwa yau, ga messages da ya ta turo mata na ban hakuri da rarrashin ta akan rashin da su ka yi na yar su.

Wi-pi din wayar ta kunna kafin ta shiga whatsapp, ta bude chat din shi, A hankali ta zauna daga gefen gadon ta soma karanta last message da ya tura mata.
_Aisha ba zaki yafe ma yayanki ba?

Pls bani baki tausayi, tsawon shekara sha takwas ina dakon soyayyarki a cikin zuciyata, dan Allah ki taimaki bawan Allahn nan, gani da
on barata agare ki, ko bacci bana iyayi saboda tunanin ki, nasan da babynmu tana araye watakil inci albarkacin ta, saboda kina son ta, amma baki son mu sake samun wata atare?

Kiyi tunani Aisha ni kadai ne zan iya baki irin ta_
A hankali ta furta"nasani ya shureim, kai kadai ne zaka iya bani irin ta, tabbas ina so na sake haihuwar mai kama da ita, but I can't marry you!

I've already told you I won't marry the man who raped me, I can forgive you, but I can't marry you, even though I still love you amma meyasa kayi mini haka?
jefar da wayar tayi kan gado kafin ta kifa kanta jikin pillow, kuka take ji sai dai hawayen sun
i zubowa, sai dai takama yin kukan zuci.

"Aunty Ummi" cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Unaisah, Da sauri ta shanye damuwarta ta mike zaune tana kallon Unaisah dake shigowa ciki hannunta ruke da akwatin ta.

"Ina Batool din?

Tace min zatazo gurin ki, "
"Batool bata shigo nan ba, akwatin wanene wannan"?

Ta fada tana nuna akwatin hannun ta
"Kayan da Chief ya siya minne"
ta fada tana murmushi, Ummi tace"Masha Allah, amma na taya ki murna, gaskiya Chief yana ji dake.."
ta fada yayin da take bu
e akwatin data kar6a a hannun ta, tayi mamakin kayan masu kyau da tsada.
______________________________
bayan ya kammala motsa jikin shi, ya fito daga Gym room din ya nufo dakin sa, hannun shi ruke da bottle water me sanyi, ya rataya farin towal akan shoulder dinsa, kwata kwata babu riga a jikin shi sai Boxer short dinsa, gaba daya jikin shi gumi yake fitarwa..

Harya bude murfin robar zai kai baki da niyar yasha ruwan, wayarsa ta doka alert, dan dakatawa yayi ya nufi wayar dake akan couch, ya danna unclock button, bai jira yaga wanene zai shigo ba ya juya baya ya kanga bottle din abakinsa ya fara shan ruwa.
can cikin kunnansa yajiyo takun tafiyar mutun, abun ya daure kansa aransa ya ayyana wanene ya shigo masa daki batare da sallama ba?

A sukwane ya juyo don yaga wani isasshen ne, da dan mamaki akan face din sa ya ke kallon ta, tayi tsaye idanunta na kallon floor, kamar mara gaskiya sai wasa takeyi da yatsun hannunta..
*~_____________________________////////////////////
*Daga Alkalamin Boss Bature
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*
_ *The Unexpected Guest *_
~___________________________________
Da ace wani ne ya shigo masa daki haka zai tuhumesa ne amma da yake yasan wacece ita, da irin rayuwar da tayi sai bai damu ba.

"Me ke damun ki"?

Ya fada ganin kayan baccin jikinta sunyi squeezing, ga sumar kan nan nata a haukace ba gyara.

Sam ta kasa bashi amsa, wani irin shakkarshi take ji, batasan ma ta shigo dakin ba, saboda bata a hayyacin ta,
Nufo ta yayi jikinta na bari ta juya zata fuce, tana ruke handle din kofar taji ta adatse, wani irin faduwar gaba taji, ta dinga jan handle din amma taki bu
ewa kamar zata saka kuka.

Mamakine ya kama shi, ya rasa gane kan ta, aransa ya ayyana ko dai tana da tabin hankali?

If not why zata shigo dakinsa ba sallama kuma yayi magana tayi shiru, sannan ya nufo ta tana kokarin guduwa"?

Daga bayanta ya tsaya yana kallon yalwatacciyar suman kanta data cika bayanta.

"Fada min meke damun ki?

Baki da lafiya ne?

Ai ko ki akayi guri na?

Ko kinzo ne don ki gaishe dani'?

Cikin rawar murya tace"am sorry, bansan na shigo ba, ba wanda ya aiko ni, "
"Look, ni nasan ba hakanan ki ka zo ba, dole akwai abunda ya kawo ki daki na, just Calm down and tell me "
Batare data juyo ta dube shi ba tace"ka ba Unaisah akwati, ni baka bani ba kuma inaso"
Murmushin gefen fuska ya saki"Akwati biyu nace ta dauka, daya nata daya naki"
"Ai daya ne tazo da shi, kuma tace nata, ita kadai ka ba mawa"
juyawa yayi tare da kallon inda ya ajiye akwatinan daya ya gani.

"Oh, ina tunanin ta manta bata ji ni dakyau ba..." ya juya ya nufi akwatin ya janyo handle dinshi ya mika mata"ga naki kema" maimakon ta juyo ta kar6a sai ta mika mashi hannun ta ta baya don ya bata.

"It's improper ki juya mun baya ina magana, if you wanna me to give it to you, Turn around and face me"
sarai ya fahimci shakkar shi take ji, kuma tana da kunya.

Dakyar ta juyo ta fuskance shi idanunta na kallon floor.
dayasan haka zai ganta inya matso kusa dabai ce ta juyowa ba, saboda gaba daya shatun nipples dinsa sun fito sosai ta jikin rigar baccin ta, bata saka bra ba, da sauri ya kawar da idanunsa gefe
aya, Ya mika mata akwatin hannunta na kerma ta ru
e handle dinta cike da zumudi ta juya zata fuce ya dakatar da ita.

"Kar in kuskura in
ara ganin kina yawo babu mayafi akanki!

Ki dinga suturta jikinki dakyau"
gabanta na faduwa ta amsa mashi da toh, Ya raba ta gefenta Ya danna code din kofar ta bu
e da sauri ta fuce, tsayawa ya yi yana kallonta yayin da take jan akwatin ta nufi stairs, sai dadi take ji har zukunnawa tayi kan stairs ta shasshafa jikin akwatin batasan yana kallonta ba, sai da tagama kalle shi ta mike cike da zumudi ta karasa sauka down ta nufi dakinsu don taje ta gwado ma Unaisah itama ya bata suitcase.

Sakin kofar yayi ta yi locking kanta, har zai juya idanun shi suka sauka akan siraran gashin kanta da ya kakkaba a kan floor, wasu irin dogaye masu kananna
juyawa yayi ya nufi tissu box dinsa dake ajiye gaban mirror ya yago tissue
in ya dawo ya zukunna gaban gashin Ya daura tissue din Ya nanna
o su aciki, Kafin ya mike ya nufi drawer, ya bude Ya sanya Tissue din a ciki.
______________________________
Bayan Kammala Sallar Juma'a around
arfe biyu da yan mintuna, Hamshakan Motoci Suka fara tururuwar shigowa Obie Estate, bakowane a cikin su ba face yan uwa da Abokanan Chief Owais yan team dinsa na isod tare da U.s Armies.

Raba hanya motocin su kayi wasu suka nufi Gidan Baba Obie yayin da wasu suka nufi Gidan Chief Owais..
*CHIEF OWAIS
Yana atsaye Cikin Lift, ya dauki wankan tuxedo suit, anyi masu adon Gold Gem stone dark blue, sai kyalli su ke yi, kayan sunyi fitting dinsa, ga wannan hadadden ducktail hair style din da yayi ma sumarsa.
idanunsa na akan wrist watch dinsa kirar patek philippe wanda sai dan wane da wane suke sanyata.

Time yake kallo, Yana karasa saukowa down Lift din ta bu
e Ya fito Ya nufi Dining area Tun kan ya karasa fragrance dinsa Ya daki kofofin Hanci nan su kusan atare suka dago suna kallon shi, ya yin da su ke a zaune kan Dining Chairs suna cin lunch din su.
kasa ha
iye kingin abincin dake a bakunan su sukayi saboda rudewar da sukayi na ganinsa, Ya tafi da imanin su, Ba ummi ba ba taj ba har Unaisah da Batool sun shagala da kallon shi..

Har saida yayi masu gyaran murya tukunna suka gyara nutsuwar su..
Chapter 23 · 0% Book details