← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 201

Sashe 72

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk wannan abun dake faru su mami dake a falon basu son komai ba, saboda sun yi nesa da su basu iya jiyo sautin komai..

Kwatsam suna zazzaune a saman sofas na falo, suka soma jiyo kukan Mahboob kamar ana zare ransa, Hankali atashe suka zabura tare da mikewa kafin su motsa sai ga shi ya watso da gudu hawaye jaga jaga da fuskar shi yana karasowa bai iya furta kalma ba Ya yanke jiki ya fa
i asume, har suna hada baki gurin ambaton sunan shi basu kaiga karasawa gare shi ba, kwatsam saiga agents sun biyo bayan shi, biyu daga cikinsu sun dauko gawar Ana asaman wani buhu, wa'iyazubillah tsabar tashin hankali kasa motsi sukayi, saboda al'ajabin daya rikirkita su, har agents din suka ajiye gawar a tsakiyar su basu motsa ba.

Anila bata san sa'adda ta saki Junaid ya fadi kasa yana kuka, zubewa tayi kan gwiwowinta akan gawar ana da hannu ta dinga kakka6e kasar dake akan fuskarta har saida ta goge ta sosai ainihin kamannin fuskarta ya fito.

Cikin shesshekar kuka ta dubi agents din"A.. a ina kuk..

Ka samu gawarta"?

Agent zahra yace"a wani dakin sirri dake a jikin dakinsa wanda kofarsa bayan wardrobe dinsa take.."
fashewa tayi da kuka, Zahra tuni ta jima da sumewa, ummi ma nan take ta yanke jiki ta fa
Anila ta dubi abie daya kame atsaye shida mami tana kuka tace"yanzu kun gasgata abunda na fada maku ko?

Gayanan kun gani da idonku, Ana ba sharri tayi masa ba, bayan ya gama lalata rayuwarta shine Ya kasheta Ya binne don kada asirinshi Ya tonu.."
baba Mai gadi daya gama rudewa yama ra
a ina zai sa kansa.

Agent zahra ya fayyace masu komai da suka gani adakin Dan Iya.

Yace sun dauki bayanan da suke so Saura su kama shi, kuma suna neman goyan bayansu In har ya taka kafarsa a cikin gidan su yi hanzarin sanar da su sannan zasu tafi da gawar ana don su karasa binciken su akanta, idan suka gama zasu yi mata jana'iza, bayan haka sun kulle dakin dan iya dana Ana, kada wanda yayi kuskuren bude shi.

Kafin su tafi da ita Anila da abie da Mami suka zuzzukunna agaban gawar suka dinga yi mata addu'o'i.

Abie yace Idan zasu yi jana'izar su sanar da shi yanaso ya halarta suka amsa mashi da toh.

Bayan tafiyar su, Abie Ya dauko ruwa Ya yayyafa ma wadanda suka suma, koda suka farfado cike da damuwa suke tambayar mafarki sukayi ko gaske ne abun da su ka gani?

Abie ya fa
a masu abunda sojoji su ka ce, ya kuma ce suyi hakuri su rungumi kaddara, dan iya bai kyauta ma kanshi ba Ya ha'ince su Ya karya masu zuciya, bai ta6a zaton zai iya aikata rashin imanin na ba, ummi tana kuka tace Allah ya isa tsakaninta da shi, in sha Allah sai yaga sakayyar cin amanarsu da yayi da kuma abunda yayi ma Ana, anan har Ta labarta masu lokacin da take zuwa gyara masa badroom dinsa duk in taci karo da makudan kudi Sai yace mata bana shi bane, kudin Campaign ne da yan siyasa ke bashi, a karshe dayaga tacika sanya mashi ido saiya hana ta shiga dakin Kwata kwata, yace ta daina zuwar masa daki, a duk lokacin daya bukace ta zai shigo nata dakin, akan wannan maganar har fada sukayi batare da sanin kowa ba, kuma tun daya buga mata warning bata kara shiga dakinsa ba in bashi ya kirata ba, har yanzu abun yana
ona mata rai amma bata taba fa
a ma kowa ba sai yau da Asirin shi ya tonu.

Akalamina bazai iya misalta tashin hankalin da suka shiga ba, sunyi kuka tamkar ba gobe, Zahra da mahboob Har saida zazza6i ya lullu6e su bayin Allah, basu ji ba basu gani ba Ubansu Yaja masu.

Sai da takaiga Mami da Abie ne suke lallashin su su kansu karfin haline kawai sukeyi saboda matsanancin halin da suke a ciki.

Ahaka basu Ji komai ba, dan wannan introduction ne na abunda ya ke aikatawa.

Kamar masu zaman makoki, haka sukai ta alhini, baci ba sha kamar masu azumi..

Batare da sanin su ba, baba mai gadi ya tattara yanashi yanashi ya gudu daga gidan, saboda tsoron kada laifin ubangidan sa Ya shafe shi.

Wuraren Karfe
aya da rabi na rana, saiga Isod soldiers din sunzo gidan, gaba daya suka kewaye gidan bisa Umarnin Dg, sune zasu cigaba da gadin gidan har zuwa lokacin da zasu kama
an Iya
~_______________________________
Dr Jidenna
Yana a zaune kan Kujerar Officers dinsa ya
aura
afa daya kan
aya, as usual asanye yake da Ankara riga da wando, ya daura lapcoat fara akai, ga karkatacciyar hular nan tasa ta inyamurai daya kifawa kansa kamar kujera yar tsugunno, wuyansa yana a rataye da statescope, a tsanake Ya ke yin Operating Laptop dinsa dake akan desk din gaban shi, sanyin A.c na ratsa shi, Hankalin shi kwance bai da wata damuwa, yana aiki yana shan coffee din sa dake a cikin cup din gabansa.

Wayarsa ce tayi ringing, saida ya mula ya sha iska tukunna yayi picking tare da karawa a kunnansa..

"Dr.adam ya akai?

Ina aiki ka katse ni, ba nace nayi cancelling meeting din da zamuyi ba.."
bai
are maganar ba, muryar dr.

Adam ta katse shi"sir ba wannan ba, akwai matsala, Idan kana a office kayi gaggawar guduwa idan ba haka ba, ka mutu..." cikin rudu yace"bansan zancan banza Adam!

In gudu sai kace wani 6arawo?

Ka manta da wa kake magana?

Md ne fa, ka duba layin da ka kira ko kayi mistake ne..." katse shi dr Adam yayi cikin rawar murya yace"kutmar Uban md din! don ubanka ka gudu nace!

Asirin mu ya tonu, sun san komai, sun san cewa da sa hannunmu ake sadaukar da jariran su In har ka bari suka ritsa dakai ka mutu, Ni ma ganin nan zan gudu in bar
asar"
Tuntsirewa yayi da dariya"bana son shirme da shiririta, yanzu ba lokacin yin tsokana bane"
Dr adam yace"ba tsokanarka ka na keyi ba, dagaske nake maka, ka gudu yanzun nan ko ka kwana a
abarin ka"
"Ka fahimce ni, rayuwar mu tana a cikin ha
ari, yanzu haka da nakeyi maka magana, gidan dan iya, a kewaye ya ke da Sojoji ni ma kaina ya
aure na rasa gane tayaya akai hakan ta faru?

Taya suka san komai..."
"Bari na kira obinnan muji, Ni nasan labarin nan ba gaskiya bane, waya isa ma ya tona asirin dattijon arzi
i balle har a kama shi, bayan suke rike da kasar da iznin su ake komai..." katse kiran yayi ya dannawa Layin baba Obie kira, tana shiga ba'ayi picking ba, kira ya dinyi baya picking..

"Kai ko ka daga mana!

Nasan a bakin ka ne zanji gaskiyar zance"
Knocking Kofa Yaji daga waje, rai a6ace yace"pls bana bukatar ganin kowa, na ce na fasa meeting din.." bai kaiga
arasa maganar ba, suka banka
o kofar, da karfi, a zuciye ya dubi mai shigowa da niyar ya tsawatar ma su, A fadace yai pointing din su, da indext finger dinsa, cak ya tsaya kamar andasa mashi aya, ya shiga zare jajayen idanun shi kamar na mujiya, cikin shi ya duri ruwa duk yabi yasha jinin jikin shi..

Isod Agents ne suka shigo su hu
u sanye da black suits
aya daga Cikin su ne Ya nuna masa Id Card dinsa"sunana Agent Jabeer Osman daga hukumar Isod, muna gayyatarka zuwa headquarter din mu, ka biyo mu mu tafi salin alin, batare da kayi kuskuren da zaisa wani ya gane meke faruwa ba, Idan kuma kace za ka yi mana gaddama..." bai
are maganar ba, ya
age masa gira tare da kai hannu ya shafa bindigar dake soke a qugunsa, tsantsar tsoro ne da tashin hankali akan fuskar dr jidenna, jikinsa ya kama kerma kamar mazari, zufa ta wanke goshinshi, sai faman sharceta yakeyi da yatsunsa,
Agent Jabeer ya kara da cewa"bayan haka, Iyalinka suna a karkashin kulawar sojojin mu, kasan me zai biyu baya idan ka bijire ma na"
Agent din dake a gefen Jabeer da hannu ya nuna masa kofa"this way please" cikin rawar jiki ya bi su suka sanya shi a tsakiyar su, gaba daya hospital staffs din babu wanda yasan meke faruwa, sun ga dai Md jidenna a tsakiyar bakinsa masu bakaken suit sai washe bakiyi yake yi suna fira, wasu daga cikin visitors har gaishe da shi su ke yi yana amsa masu dakyar dakyar.

Shi ka
ai yasan musibar da ya ke a ciki, marassa Ta cika da fitsari..
_______________________________
Horn din Mota ne Ya karade kunnuwan mai gadin wani katafaren gida, mikewa yayi daga kan bencin da yake a zaune, cikin sauri ya karasa tare da zuge gate din gidan, ta shigo da motarta a parking space ta ajiye, da sauri mai gadin gidan Ya nufi motar, Ya bu
e mata Car door, fitowa tayi daga ciki, babbar macace jawur, daga ganinta inyamura ce yar gayu da ita, sanye da lace, tayi rolling mayafi akanta..

"Sannu da dawowa Hajiya, ya gajiyar aiki" sama sama ta amsa mashi, kafin ta nufi gidan, tun a falo ta fara cin karo da high heels
afa biyu, ga handbags saman sofa"
Nan take ta fahimci tayi ba
i, Girgiza kai tayi cike da bakin ciki ta nufi bedroom din mijin nata, nishi da gurnani ta dinga jiyowa.

Acikin kunnanta, ko knocking batayi ba, ta ture kofar ta shige, a kwance ta same su turmi da tabarya, shi daya mata biyu akan shi..

Wa'iyazubulla, kwata kwata basu san ta shigo ba, saboda sun fita hayyacin su, Ba yau ta saba kama shi da karuwai a cikin gidan su ba, idan ta ce zata tanka sai ya rufeta da fada hada bugu.
Chapter 72 · 0% Book details