← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 201

Sashe 43

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anya ba tuban muzuru su ka yi ba? saboda nayi mamaki wallahi, Mutanan da suka gaji sihiri suka san dadin shi zaiyi wuya su tuba ta cikin sau
arashe maganar yayin da yake mi
a ma matashiyar dake a gafensa hannu cikin sauri ta tsiyaya masa whisky a glass ta mi
a masa ya kar6a tare da kaiwa baki yana kur6a.

"Bakin ciki ne da hassada don kada mu samu cigaba, Watakil kuma saboda suna jin fargaban mu farfado da ran kurkukun kaddara, ko kuma suna jin tsoron mu ci amanar su..."
acewar jan le6e, wata yar iskar dariya suka sanya..

A hankali jan wuya ya kur6i whisky din dake a hannunsa kafin yace"yakamata mu san abunyi, ni hankalina bai kwanta da alkawarin da Elder ya
aukar mana ba na cewa bazai tona mana asiri ba, yadda ya mutu akan kaunar jikan nan nashi kuna tunanin ba zai iya fada masa komai ba idan ya matsa masa? kuma ina kokwanto dakyar in ba makirar tsohuwar nan tasan ni ba, Kada sai mun saki jiki su fallasa mu..." maganarsa ta dan daga hankalin Sauran Elders din..

Jan Le6e yace"bana tunanin Elder zai iya cin amanar mu, mun riga da munsan halin shi mutunne mai rukon amana, ko da zasu azabtar da shi, bazai fa
i sunayen mu ba,...."
bai
are maganar ba, Jan wuya yace"hmmm dan adam ba abun yarda bane, ni ban yarda da kowa ba, kawai mu nema ma kanmu mafita..." bai kare maganar ba, jan ido yace"me kake nufi"?

Wani makirin murmushin gefen fuska ya saki tare da kallon su, sai da Ya zuki tabar hannunsa kafin yace"ku yi amfani da brain dinku mana, idan har muna so mu zauna lafiya batare da fargabar wani abu ba, to fa dole sai mun kawar da Obie family, saboda sun san komai game da kurkukun kaddara da kuma sirrinmu, tun kafin labarin ya fita duniya ta sani, muyi gaggawar tura masu Evil giants under cover of night, su kashe su duka batare da sanin kowa ba, and no one will suspect a thing, kunga daga nan zamu ci gaba da cin karen mu babu babbaka...."
har ya
are maganar tashi elders din basu tanka mashi ba, kamar shawarar tashi ba ta kwanta masu arai ba..

Jan le6e yace"wannan shawarar daka bamu bamai 6ullewa bace, ko kamanta gargadin da jan harshe yayi mana"?
ya tambaya yana kallonsa bai jira amsar shi ba ya dasa da cewa"Idan ka manta bari na tuna maka, Har yanzu Elder shi ke a ruke da masarrafinmu, idan muka kuskura muka ce zamu ci amanar shi wallahi zai yi mana tsiya ne! elder zai iya rufa mana asiri amma abu dayane zaisa ya tona mana asiri ya kuma
wace sirihin jikinmu shine idan muka ci amanarsa, Saboda shi baya yafewa wanda ya ci amanarsa, Kuma kai kana tunanin Evil giants zasu Iya farmakar Ahlin Obie bayan Elder Yana araye..."?

Ya jefa masa tambayar, nan da nan annurin fuskarsa ya
auke
uff..

Jan ido yace"kayi tunani mai kyau Jan le6e, ba zamu iya cin galaba akan ahlin Obie ba har sai bayan ransa.."
Shiru su ka yi na
an wani lokaci, young ladies din da ke a kewaye da su sun yi zururu da idanun su, ga gajiyar da suka farayi da tsayuwa ba halin su ce zasu zukunna..

"Abun da ya kamata mu maida hankali akai yanzu, shi ne Mu nemo Jan kunne duk inda ya shiga acikin garin nan, saboda shine mai rauni a cikin mu, Idan mukayi kuskuren da Jami'an isod suka riga mu kama shi zai tona mana asiri ne da zarar sun fara azabtar da shi saboda ba shi da juriya ko ka
an...."
acewar jan le6e, kusan atare suke mike daga kishingiden da suke sam sun manta da batun wani jan kunne dama bawani mahimmanci suke bashi ba, saboda Obie yasa suke tarayya da shi...

"jan kunne baida amfani agurinmu, ko da mun kama shi sai dai mu kashe shi, tun da asirin shi ya riga daya tonu..." jan wuya ne ya fa
a da kakkausar muryarsa.

Jan ido yace"wayarsa a kashe take, wata
il ya jefar da ita wani gurin don kada jami'ae su bi diddiginsa, duk da sakarcin shi wani lokacin yana da wayau, amma hakan bashi zai hana mu
yale shi ba, dole mu kashe shi..." ya karashe maganar tare da kur6ar giyar dake a hannun sa...

"Ranar da muka yi zaman tattaunawa a mafarki, shi kadai ne bai halarta ba, zai iya yiwuwa ya gudu yabar kasar ne.." ya fa
a yana kur6ar whisky dinsa..

"ba zai yi mana saukin kamawa ba, saboda karfin sihirinsa
ayane da namu"!

Jan le6e ne ya fada rai a6ace..

Jan wuya yace"kubar komai a hannuna, zan nemo shi da kaina, Kuma zan kashe shi..." tuntsirewa sukayi da dariya hahahaha...

"Ya batun dawo da ran gidan kurkukun
addara?

Kada ku manta Har yanzu muna da sauran dama fa, idan har muka cika sharu
an da ake bu
ata zamu jefi tsuntsu biyu ne da dutse
aya, na farko zamu iya canza location din gidan kurkukun
addara, abu na biyu in har mukayi nasarar cika sharuddan karfin sihirinmu zai
aru, ta yadda ko Elder bazai Iya ja da mu ba, ..." wani irin annurin farin cikine Ya cika su, jin abun da Jan le6e ya fada, Jan ido yace"tayaya hakan zai yiwu"?

Shu'umun murmushi jan le6e yayi"kada ku manta, tun kafin ku san Elder na riga ku sanin shi, atare mukayi yawan duniyancin mu, duk wani sirrin shi na sani, wannan maganar dana fa
a naganta ne a rubuce cikin tarik sijnil
adar wanda mahaifin Elder ne ya rubuta littafin da al
alamin shi tun da dadewa..."
wata irin shewa suka sanya har saida suka tsorata matasan yan matan dake yi masu hidima.

"Amma fa wanda ya riga cike sharuddan a cikin mu, shine zai maye gurbin Elder, shi kuma Elder zai rasa karfin sihirin sa ta yadda bazai iya sarrafa evils din jikin mu ba"
Wannan maganar da jan le6e ya fa
a ta faranta ran Jan wuya, sai faman sakin shu'umun murmushi yakeyi aransa harya fara tunanin yadda zai riga su aiwatarwa saboda ya samu karfin ikon Elder, tsabar hadamarsa yafi so yafi kowan nan su karfin sihiri, ta hakane kadai zai iya mayar da su karkashin ikon shi, don ya cigaba da juyasu son ran shi
UNAISA ANGEL
A cikin kunnanta ta jiyo sautin dirar Mota a gidan, baiwar Allah a lokaci bacci ne ke kokarin
aukarta, tana a kudundune cikin duvet dinta ta kasa runtsawa saboda tunaninsa, ranta ne ya bata shi ne ya shigo gidan..

Jikinta na 6ari ta sauko daga kan gadon, Batool tana akwance gefe daya tayi nisa a baccinta, ta kudundune kanta cikin duvet din ta, Night gown ce a jikin ta Ja, Mayafi ta dauka ta yafa ma kanta, ko takalma bata saka ba, garin saurin ta fita daga dakin har tuntube tayi amma hakan bai dame ta ba, burinta kawai ta je ta dubo in shi ne.

Tana fitowa daga dakinsu ta nufi main falo unexpected Ta hango shi yayin da yake tafiya akan stairs, aranta ta ayyana dama yana fita a irin wannan lokacin idan sunyi bacci?
tayi kewarsa cikin kwanakin nan daya juya masu baya, daga yanayin yadda yake tafiya ta fahimci babu kuzari atare da shi kamar wanda yasha
waya, Cikin sauri tabi bayanshi sai dai kafin ta karasa tuni Ya shige bedroom dinsa, tana isowa bakin kofar room din tayi knocking shiru babu alamun zai bude mata, cigaba da bubbuga kofar tayi tana ambaton sunan shi tare da yi mashi magiya akan ya bude mata kofar.
abun daya
aga hankalinta sautin nishin da ya ke saki har cikin kunnanta take jin shi, ganin baida niyar bude mata kuma bai bata iznin shiga ba, hakan yasa batai wata wata ba, ta fara kokarin danna code din kofar da ya ke ya taba nuna mata tun farkon da suka fara shakuwa da junan su, abun daya sa bata taba gigin yi mashi katsadan din ta shiga batare da izninsa ba, saboda ba muharraminta bane, kuma bai dace ta fada masa daki batare da izninsa ba, batasan awani yanayi zata taras da shi ba.

Nishin da taji yanayi ne yasa ta razana har bata san sa'adda ta saka code din kofar ta bude ta, a fujajen ta dira kafafunta cikin dakin, wani irin burki taci, lokacin da idanunta suka hango mata shi, har ya cire kayan jikin shi, yana daga tsaye gaban gadonsa ya bata baya, boxer short ne kadai a jikin shi, Ya ru
e Syringe mai dauke da ruwan allura a cikin shi, yana kokarin caka ta a upper arm din sa..

"My hubby...." dakatawa yayi jin muryarta a cikin kunnan shi, kwata kwata baisan da zamanta adakin ba, hatta knocking din da ta dinga yi baiji ba saboda hankalin sa baya a tare da shi, kawai so yake yayi ma kansa allurar ko ya samu sassaucin radadin da zuciyar sa ke yi masa, kwana biyu rabon da yayi bacci saboda pressure din daya daura wa kansa na gano su wanene Elders, bai da wani kwanciyar hankali idan har ba gano su yayi ba.

A hankali take tafiya tana tunkarar shi, daga bayan shi ta tsaya tana duban gefen fuskarsa daya jike sharkaf da gumi..

"Me ke damun ka?

Meyasa ka juya mana baya?

Ka hana zuciyata sukuni, saboda kai ko bacci bana iyayi, na rasa gane kanka acikin kwanakin nan! ..." ta fada tana dan girgiza kanta idanunta sun cika da kwalla..

"Why would you inject yourself?

Aren't you well?

Ta fada araunace.
da wata irin kakkausar murya ya furta
I don't want to see anyone close to me!

Don't you dare take one step closer to me! ki fuce min daga daki..."
gabanta ne ya fa
i a rude take kallon bayansa, kamar ba daga bakinsa kalaman ke fitowa ba.

Ta razana sosai, Cikin rawar murya tace"Husband to be, yau ni kake kora daga dakin ka?

Me yake damunka ne?
Chapter 43 · 0% Book details