← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 201

Sashe 35

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da bacci ya fara cin karfin su, Ummi da Batool har sun fara gyangya
i, Unaisah dai ba alamun bacci atattare da ita, ta kasa ta tsare sai Chief ya dawo.

"Ummi ku tashi kuje ku kwanta, dare yayi sosai" Taj ne ya fada yana duban su..

Sun langwa6e kansu jikin Sofa, girgiza kai Ummi ta yi, "Bana tunanin zan iya runtsawa in har Chief bai dawo ba, wlh na damu Boss, ace ko waya baya picking?"
Ta fa
a fuskarta a yamutse.

Da damuwa akan fuskarshi ya ce, "Ku yi hakuri kuje ku kwanta, in sha Allah ba abun da zai faru da shi, bafa wata uwa duniya ya tafi ba, yana agidan grandpa dinsa dake a cikin estate din nan, may be yan uwansa ne suka ru
e shi, amma nasan in sha Allah da asuba zai dawo nan din.."
"Amma in har lafiya, meyasa munata kiran sa baya picking? bayan shi da kan shi yace mu shirya idan ya dawo zamuyi celebration a gida.."
"At least in ma bazai dawo ba, yakamata ya kira a waya ya fa
a mana.."
"Ummi, kuyi masa uziri, Allah kadai yasan me ya tsayar da shi, a sanina da Chief bai cika mantuwa ba, mutunne mai son cika alkawari, sai dai bansan meyasa bai dawo ba, kuma bansan abinda ya hana shi kiran mu ba, amma mu yi hakuri mu jira zuwa gobe.."
Ummi ta ce, "Ni ba rashin dawowar shi bane ya
aga min hankalina, kawai muna so muji in yana lafiya sai hankalin mu ya kwanta.."
Dakyar Taj ya samu ya lallashe su har suka hakura da jiran na shi kowa ya nufi bedroom dinsa don ya kwanta.
~______________________________~
ELDERS
Duhu ne ya mamaye ko'ina, ba zaka iya ganin komai dake a kewayen wurin ba.

Yayin da yake a tsaye cikin shiga ta doguwar riga ba
a ta sauka har
asan kafafunsa dake a sanye cikin bakaken takalma na fata, Ya lullu6e sumar kansa da hular rigar tasa, baka iya ganin komai na jikinsa in ba
wayar idanunsa ba, hatta fuskarsa a lullu6e take da ba
in takunkumi, yayin da ya ru
e sandar sa a hannun shi na dama.

Tun daga yanayin tsayuwarsa zaka fahimci babu
oshin lafiya atare da shi, akwai rauni da karayar zuciya atattare da shi..

Unexpected hasken wutar candles dake a kewayen wurin ya soma kunna kansa, hakan ya bani damar ganin sauran bil'adaman dake a cikin katafaren
akin, har saida na firgita da ganin wasu irin dogayen mutane masu
irar
arfi a jikin su, gaba dayansu suna a zaune kan armchairs din dake a kewaye da shi.

Shigar jikinsu bata da bambanci da tashi, bakaken dogayen riguna ne a jikinsu, sun rufe kansu da hulunan rigunan, kowannansu yana a ruke da sandar shi ta alfarma, gaba daya sun sadda kansu
asa.

Hankalinsu ya dugunzuma ainun, basu ta6a shiga mawuyacin hali na farga irin wannan ranar ba, tun da Elder ya fada musu abun da ya faru da shi hankulansu sun tashi matu
a, wlh sun ka
u da jin asirin Elder ya tonu, dole su razana saboda basu taba tsammanin asirin shi zai tonu cikin sau
i ba, shi da yake shugaban su, ina ga su na
asa da shi.

Abun da ya daure musu kai ta yadda har sihirin shi ya
i tasiri a lokacin da khala take tona mishi asiri, bayan haka sun yi mamakin tabya akai ta rayu bayan Elder ya tabbatar musu da mutuwar ta
alla Elders din dake a dakin sun kai su goma sha
aya, gaba daya sun tattara nutsuwarsu sun mayar da hankulansu akan Elder da ke kora musu jawabi cikin harshen su na matsafa..
a yau na ji kunyar da ban ta6a jin taba a rayuwata, nasan da zuwan wannan ranar amma ban ta6a zaton zata yi silar da zan ji danasani atare da ni ba, hankalina ya tashi, zuciyata ta karaya, fargaba da tsoro sun mamaye zuciyata, bawai don asirina ya tonu ba, sai don halin da na jefa rayuwar ya'yana da suka aminta da ni, nine silar
aukakarsu, nine
ashin bayansu kuma jigo sannan jagora na rayuwar su, kuma nine abu mafi soyuwa agare su, kamar yadda nima na
auke su dangina, bugun zuciyata, sune nake gani in ji dadi a raina, sune farin cikina kuma jin dadin rayuwana, amma a yau da asirina ya tonu a gaban idanunsu, na muzanta na ji kunyar da banta6a jin ta ba a rayuwana, na karaya da ganin yadda suke kukan bakin ciki saboda zaluncin dana aikata ma ya'yan su da kuma ha'intar su da na yi a matsayina na uba a gare su, na cuce su na cuci kaina, na kuma cuci ya'yan su dana sadaukar......."
Tun da Elder ya fara maganar sauran Elders din suka kafe shi da idanunsu da suka cika da tsantsar al'ajabi da rudanin maganarsa, gani suke kamar mafarki ne ba gaske ba, jin maganganun da suke fitowa daga bakin shi, asanin su da Elder mutunne mai taurin zuciya, bai ta6a karaya ba, kuma bai ta6a danasanin abunda ya ke aikatawa ba sai yau?

Abun ya
aure musu kai tamau har sun fara kokwanton anya Elder din su ne?

Ko dai musayarsa aka yi musu?

Taya ya karaya cikin sauki ya ajiye makaman ya
insa?" Gaba daya sun ru
e matu
"Harshe na bazai iya misalta muku irin kuncin da na ji a cikin zuciyata ba, naji bakin ciki da takaici mara misaltuwa, na ji radadin da yafi na
unar wuta zafi acikin zuciyata, nayi fatan ace na mutu kafin zuwan wannan ba
ar ranar"
Ya fa
a cikin raunanniyar muryarsa, a hankali ya dafe saitin zuciyar shi da tafin hannunsa.

Kafin ya
aura da cewa, "Jikana dana fi kauna yau da kansa ya sha
i wuyan rigata kamar zai doke ni, mutuncina ya zube a idanunsu, na yi musu mummunan tabon da har bayan ransu bazai ta6a goguwa ba, na yi zaton tsafina da dukiyata zasu sama min komai na duniyar nan, ban ta6a zaton akwai ranar da tsafina bazai amfane ni ba, a yau na raina karfin sirihina saboda na gane cewa shima tsafin ba gaskiya bane yaudarar kaine, akwai wanda yake da iko da masu tsafin da shi kanshi tsafin wanda idan ya so cikin da
a zai kar6e sihirin daga gare mu, kamar yadda dangina suka mutu a fagen fama, lokacin da ma
iya suka kawo mana farmakin bazata, mu tsafi gare mu sukuma basu da wannan tsafin amma a haka suka ci galaba akan dangina suka kashe kowa baifi mu shida muka rage ba a lokacin, In har tsafi bazai hana matsafi fuskantar mummunar kaddara ba, kuma bazai hana matsafi mutuwa ba, me hakan ke nufi....."?

Ya karashe maganar cikin raunanniyar murya yana duban Elders din dake sauraron shi ..

"Bamu gane abunda kake nufi ba Elder!

Kalaman ka suna nema su rikita tunaninmu, mun rasa gane ina ka dosa! maganganunka sun jefa mu a ru
ani..." Jan le6e ne ya yi maganar..

"Ka gafarce ni Elder, amma na yi mamakin yadda kayi saurin karaya saboda kawai asirinka ya tonu a gaban ya'yanka?

Kada ka bamu kunya mana, Faduwa ba taka bace Elder!

Ba'asan Elder da rauni ba, kuma ba'a san su da saurin karaya ba, a sanin mu da kai jarumin namiji ne, wanda ba'a halicci zuciyarsa da imani ko tausayi ba, kaine kake
arfafa mana gwiwa akan karmu kuskura mu bari zuciyar mu tayi raunin da zamu ji tausayin wani ko mu karaya.." A cewar Jan Ido...

Da kakkausar murya Jan Wuya ya ce, "Ni kuma baka ta6a bani kunya irin na yau ba Elder!

Ina hankalinka da tunaninka suke?

Ina dakakkar zuciyar ka take?

Ina izzarka da zaluncinka suke!

Kaine fa dodon dake tsoratar da wasu Yau kuma kaida kanka ka tsorata saboda asirin ka ya tonu a gaban ya'yanka uhum?"
Ya fada rai a 6ace, "kada ka bari son ya'ya ya rufe maka ido har ka yi abin da zaka yi danasani Elder!

Idan ma kana tunanin ajiye kambun zalunci ka ne to ka daina!

Saboda ka riga da ka makaro Elder!

Tubanka bazai kar6u ba Elder saboda tarin
umbun zunuban da ka aikata, Koda ka shiryu hukuma da al'ummar duniya bazasu kyale ka ba, mutuncin nan naka da
imarka zasu ruguje za'a cigaba da tsangwamarka kaida ahalinka har sai ba
in ciki ya yi silar barin ku duniya, ka tuna kana da ma
iya kaida ya'yan ka, me kake tunanin zai biyo baya idan suka ji abunda ka aikata?

Zasu yi amfani da wannan damar ne gurin cuzguna muku!"
Ya fa
a da kakkausar murya hadi da dun
ule yatsunsa,
"Kuma idan hukuma ta dam
e ka sai ka yi danasanin zuwanka duniya saboda azabtarwar da zasu yi maka, bayan haka idan mutuncin ka ya zube, zaka tashi daga dattijon arziki ka koma
antacce, mugu, kuma tantirin
an ta'adda a idon jama'a, za'a cigaba da aibata ka ne..."
Ya fa
a yana sakin dariyar sha
iyanci da alama shi ko a jikin shi bai damu da halin da Elder ya ke a ciki ba, shiru Elder ya yi bai tanka masa ba, hakan ya bashi damar cigaba da yin maganarsa, "Yanzu ya rage naka Elder, ka zauna kayi tunani kafin ka yanke shawara, har yanzu muna da damar da zamu farfa
o da gidan kurkukun
addara, ka kashe kowa naka da ya san sirrinka, mu cika sharu
an allon tsafin mu, a ganina ba dole saida Iyalanka zaka cigaba da rayuwa ba, kabar kowa naka, mu canza she
a...."
"Aminina, ni ina ganin mu
auki shawarar Jan Wuya, ita ka
ai ce mafitar dake gare mu, Ba zan so
aya daga cikin abunda ya fa
a ya faru da mu ba, ina jiye mana tsoron kalubalen da zamu fuskanta, ni bazan baka shawarar ka kashe ya'yanka ba, amma mu yi nesa da duniyar mutane, inda babu wani mahalukin da ya isa ya tunkare mu koda ba zamu cigaba da yin tsafin ba.." Jan Harshe ne ya yi maganar cikin tausasa murya...

"Har yanzu baku fahimce ni ba, Na lura wasu daga cikin ku basu damu da halin da nake a ciki ba..." ya fa
a yana jan numfashi gami da furzar da shi..
Chapter 35 · 0% Book details