← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 201

Sashe 19

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ashe dama duk kyautatawar da ka yi mana ba don Allah bane, sai don saboda wata mummunar manufa taka, baiwar Allah Aisha saida ta nuna batason zama agidan da ka kama mana haya a kasar germany saboda hankalinta bai kwanta da shi ba, sannan ta nuna rashin jin dadin ta akan zaryar da kake yi cikin gidan duk weekend sai ka zo ka kwana ga kudi da kake kashe mana, ni da kaina na kare ka agurinta na nuna mata cewa kada ta damu Uncle dina mutunne mai son yin alheri kuma dukiyar ka ta halal ce kasuwanci kake yi, sai daga baya na gano komai, arzikin da kake ta
ama da shi ba ta hanyar halal ka tara shi ba, mu ka raina ma wayau da sunan kasuwanci kake yi, bayan haka ina zargin kana a
ungiyar asiri ta yan shan jini, kuma kaine ka ha
a Aisha da mahaifinta, wato ka yi amfani da damar da kake da ita, a lokacin da kake zuwa ka kwana a gidanmu, sai ka bari dare ya yi sai ka saci hanya batare da sanin mu ba ka ke shiga
akin Aisha, ka dauketa video da hotuna, wama ya sani ko asiri kake yi mata shiyasa har batasan kana yi mata hakan ba, wallahi ka ci amanar yardar da na yi maka! kuma na rantse da wanda raina yake a hannunshi in har baka dawo mana da babynmu ba saina fallasa asirin ka...."
Tun kafin in
arasa maganar, Uncle Musa ya doka min tsawa yana huci kamar mayunwacin zaki, saboda tsabar fusata da bacin rai jikin shi ya dinga fitar da gumi, abun da ya daure mashi kai ya kuma
aga hankalinsa shine ta yaya akai duk nasan abunda yake
ullawa?" Sam ya kasa magana sai huci yake fitarwa, Idanunsa sun ka
a jawur.

Ganin baida niyar yin magana yasa naci gaba da cewa, "Kuma kaine ka shiga tsakanin Yaya Shureim da Aisha, ka yi masa asiri kasa yayi mata fya
e ba'a cikin hayyacin sa ba, komai dake faruwa kana bin diddiginsu kana samun information a gurin yan le
en asirin ka, Hatta Mahaifinmu baka
yalesa ba, kana amfani da sihiri gurin juya shi don yabi ra'ayin ka, bayan haka kaine ka turama Daddy videos din Aisha daka dauka tare da kai sai ka 6oye fuskarka don karsu gane kaine kabar fuskar Aisha saboda tsabar mugunta da zalunci irin naka! kuma kai ne shaidanin da ya tunzura mahaifinmu akan karya kuskura ya yarda Shureim ya auri Aisha in ba haka ba zai rasa kujerar da yake nema kuma mutane zasu juya mashi baya saboda abun kunyar da Shureim ya akaita, munafukin Allah kaita fa
a masa kauli da ba'adi har saida ka shiga tsakanin daddy da Ya Shureim...".

Ban kai ga
arasa maganar ba ya katse ni ta hanyar bugun table din gabansa da hannunsa, Jikinshi har wani jijjiga yake yi saboda bacin rai.

"Benazir!

Bana so ki jefa rayuwarki a cikin hadari!

Ina mai gargadin ki, Tun wuri ki yi gaggawar janye zargin da kike yi mini, tun kafin ki yi danasani" Na yi tsalle na dire na ce, "Wlh Uncle bazan janye ba, saboda ni akan gaskiyata nake, ba zargin ka ni ke yi ba, tabbaci gare ni, kai baka yi mamakin tayaya akai nasan sirrinka ba uhum?

Na fa
a ina kallon cikin idanunshi, wlh a lokacin ya razana dani ba kadan ba, amma da yake shu'umin mutunne sai ya dake ya tirje akan cewa ba gaskiya nake fada ba,
azafi nake yi masa.
raina a 6ace na juya zan bar falon ban ma jira ya karasa maganar shi ba, har na kusa fucewa Ya dakatar dani ta hanyar kiran sunana na tsaya ina jiran jin me zai ce.

"Ki fada mini komai kike so a duniyar nan zan yi maki shi, amma maganar zaki tona min asiri bata taso ba, Ki yi watsi da maganar nan, nifa Uncle dinki ne, In kika tona mini asiri kamar kin tona ma family din mu ne, ki dawo mu sasanta tsakanin mu" A hankali na juyo na fuskance shi.

"Baka so zaman lafiya ba Uncle, ai wlh in har kana son sasanci to ka dawo mana da babynmu, ni kuma nayi maka alkawarin babu wanda zaiji maganar nan!

Ni ita kadai nake so bandamu da abunda kake aikatawa ba, wannan tsakanin ka da Allah ne, duk wanda ya yi da kyau ya sani, kuma dai akwai mutuwa akwai hisabi kowa zai girbi abunda ya shuka ne..." Dafe kanshi ya yi da tafin hannunsa kamar mai fama da ciwon kai,
"Meyasa kin fiye taurin kai da kafiya ne?

Yakamata ki iya bakinki Benazir!

Har yanzu bakisan wanene ni ba!

Sabo da kaza bai hana in yankata!

Wlh zan iya salwantar da rayuwarki, kuma idan na kashe ki na kas
he banza."
A lokacin gabana ya fa
i na kuma sha jinin jikina amma ban bari ya gane hakan ba, saima na yi dariya na ce, "Idan ma kana tunanin kashe ni shine mafita agare ka, to ka daina, saboda hujjojin dana fada maka ina da su, bani kadai ke da su ba, Nima ina da mutanene da nake yin aiki tare da su, idan yau ka kashe ni, wlh zasu fallasa asirin ka ne duniya tasan me ka ke aikata, ka ga kuwa baka da wata mafita da ya wuce ka bini ta lalama"
Maganar da na yi ta
aga hankalinsa matu
a, Zuciyarshi ta hasala kamar ya rufe ni da bugu haka yake ji.

Har na
aga kafa zan fuce na sake tsinkayar muryarsa a cikin kunne na, "Ko don saboda abun da ke a cikin ki, Yakamata ki yi takatsantsan idan ba haka ba, zaki jefa rayuwarsa a cikin ha
ari ne..."
Wani irin faduwar gaba na ji, saboda a lokacin bansan ina
auke da juna biyu ba, cikin sauri na dafe cikina tare da zare idanuna akan fuskar shi, gaba daya na bi na ru
e, Murmushin mugunta ya sakar mun saboda ya gano lago na..

"Benazir, nafi karfin ki nesa ba kusa ba, wlh baki isa ki ja dani ba,
aramar yar iska mai kwana da wando, saboda baki da hankali ki rasa wa zaki tuhuma sai ni?

Kinsan wanene ni kuwa??

Ki fara sanin wanene ni kafin ki yi ja in ja dani, Sannan zan
ara tuna maki, kina da miji, kina da juna biyu, kina da iyaye, kuma kina da ya ya mafi soyuwa a gare ki, Ina fata Kin fahimci abunda nake nufi???"
Yana karasa maganar ya juya ya nufi up batare da ya sake waiwaye na ba, har saida ya 6ace ma ganina kafin na kawar da idanuna daga barin kallon sa.

Har na dawo gida ban daina tariyo maganarsa a cikin kunnena ba, Saboda hankalina ya tashi sosai, Lamarin Uncle Musa ya fara bani tsoro, na riga da na gane mugun mutunne shi, mara imani, kuma tantirin shaidani nasan zai iya aiwatar da komai don ya rufawa kansa asiri..

Bayan sati biyu na je ganin likita batare da saninka ba, bayan doc yayi mini gwaje-gwaje sakamakon ya nuna ina dauke da ciki na sati biyu, nan fa hankalina ya
ara tashi kwata kwata ban yi farin ciki da cikin ba a lokacin saboda zai zama rauni na, kuma ina jin tsoron in haife shi saboda fargaban kada Uncle Musa ya salwantar da rayuwarsa, Ko ya
auke sa kamar yadda ya dauke
iyar Ya Shureim, wannan dalilinne yasa nayita yunkurin in zubar da cikin Angel, wlh Allah shine shaidata badan bana son shi ba, Kawai a lokacin muna yawan samun sabani da kai saboda bani da kwanciyar hankali, Damuwa tayi mini katutu, kullum cikin zullumi da fargaba nake yi saboda nasan Uncle Musa bazai
yale ni ba, kamar yadda ya fada dole ya dauki mataki akaina, kuskuren da na yi shine
in sanar da kai, Na
i fa
ama kowa nabar abun a matsayin sirri, saboda gudun kada na fa
a ya koma mashi karshe inja ma kaina da kuma dangina don har lokacin ban saduda na kyaleshi kan fito da yarinyar Yaya Shureim ba, ka ji dalilin da yasa a duk lokacin daka kamani ina yunkurin zubar da cikinta ka tuhume ni dalili, sai ince maka bana son ya'ya, kuma bana son cikin saboda zai bata mini shape
in jikina, Amma a zahirin gaskiya bada son raina ni ke yin hakan ba, gaba daya rayuwar aurena da kai wani abun sai daga baya na gane bayin kaina bane, nasan bana jin magana, amma wlh Taj na so mu yi zaman lafiya sai dai na kasa faranta maka, saima cuzguna makan da nake yi hakanan bakai mini komai ba, kawai sai inji haushin ka, da tsanarka acikin Zuciyata, hatta mai aikin gidanmu Janet na ji na tsane ta, laifin da bai kai ya kawo ba idan ta yi mini bana
yale ta, saina azabtar da ita...."
Kasa
arasa maganar ta yi saboda kukan da ya
wace mata, Ha
a Zuciyar Taj ta karaya, tsantsar mamaki da al'jabi sun ruke zuciyar shi tamau, duk da sanyin A.c din dake a dakin hakan bai hana shi fitar da zufa ba, jikin shi har tsuma yake yi, wani irin tausayin Benazir ne ya kama shi ya yi danasanin zarginta da ya dinga yi, ashe bayin kanta bane, makircine aka shirya mata.

Numfasawa ta yi, cikin shesshekar kuka ta ci gaba da cewa, "Bayan wani lokaci, ban
ara jin
uriyar Uncle musa ba, har lokacin da cikin Unaisah Ya cika wata tara cuf, nima kuma ban
ara tuntubarsa ba ko in yi tunanin sanar da wani game da sirrin, a tunanina saboda bana son in jefa rayuwar ahalina Cikin hadari ne, a daren ranar da na
uda ta kama ni, da ni da kai muna a kwance kan gadonmu mun yi nisa a cikin baccinmu, kwatsam ba zato ba tsammani, na fara jin na
uda na taso mun, a firgice na farka daga baccin hannayena daddafe da cikina, ina ta faman cizon le6e saboda radadin da nake ji a jikina.
Chapter 19 · 0% Book details