← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 179 OF 201

Sashe 179

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haroon ne ya fada yana jifar su da harara.
kafin su furta Kalma sai ga Khala ta fito daga Cikin toilet din dakin, dakyar take taka kafarta koda idanunta su ka yi mata tazoli da Chief dake a rungume Da danish sai taji wani irin farin ciki ya lullu6e ta kamar ta zuba ruwa kasa ta sha.

Cikin rawar murya tace "Owais!

Danish cousin dinka ne, shine babyn Hateem na karshe da Sheikha mujeeda ta haifa masa, na fada masa komai game da iyayensa"
lokacin da yaji wannan maganar daga bakin Khala baisan sa'adda ya kara matse danish a kirjin shi ba, wani kuka ne ya balle masa, daga shi har danish din aka rasa mai lallashin wani a cikin su.
murmushin farin ciki Haroon Ya saki bayan ya gaishe da khala, Ya juya ya kalli dattijan da suka kura masu ido Yace"pls tun da kun kawo mu mun gansu, ku dan bamu wuri zamuyi magana ta sirri"
Har suna ha
a baki gurin cewa dama abun dayasa suka tsaya suna son suji idan nan zasu kwana, don su kawo masu wata katifar da kuma abunda zasu ci"
cike da kyankyami Haroon Yace"kasan su wanene mu kuwa?

Kana nufin a wannan kongon zamu zauna"?

Look bamu bukatar komai daga gare ku, mungode da taimakon da ku ka yi mana, Allah yasaka maku da Alkhairi, ga kuma kudi kun samu, don haka ku tafi, Idan mu ka gama tattaunawa, zamu bar maku gidan gonar ku.."
amsawa sukayi da toh sunata washe baki sufa yau ashar dinsu kakarsu ta yanke saka.

Har suka bar dakin Chief bai raba jikinshi daga na Danish ba, sun ki sakin juna..

Da murmushi akan fuskar Haroon Yace"finally Chief ya ha
u da cousin brother dinsa da ya rasa, dan uwansa mai kama da shi, me jarumta irin tashi."
Cike da farin Cik
i khala tace"tana tayasu murnar sake ha
uwa da juna, suyi kuka son ran su, suji
umun junansu, babu abun da zai sake raba su in sha Allah"
kalamai masu dadi da karfafa gwiwa ta shiga gaggaya masu.

Lokacin da suka raba jikinsu daga na juna wata irin zuface ta wanke fuskokinsu da jikinsu, ga wani zafi da jikin nasu ya dau ka, Idanun su cikin na juna, yayin da hawaye ke cigaba da shararowa kan kuncin kowannansu.

Cikin shesshekar murya Chief yace"am really sorry danish!

Nayi zaton kun mutu, wallahi Bansan kune kuke kirana ba, da tun ranar farko nazo na tafi daku, bansan kana araye ba, Danish kana araina dakai nake kwana dakai nake tashi, saboda yadda na damu dakai har mafarkin ka nakeyi, Danish ashe da rabon zamu sake ganin Juna? ....."
Nan take ya labarta masa komai daya faru, Hankalin Danish Ya kwanta da jin cewa Daddyn Unaisah da salsabeel dinsa suna araye sai dai baiji dadin nasarar da basuyi ba akan Elders..

"Ku fa
a mana tayaya akai kuka ku6uta daga Kurkukun kaddara..." Haroon ne ya tambaya.

"Owais Ni baka ganni ba"?

Khala ce ta fada mikewa yayi tare da duban ta..

"Ina sane dake, kema kina araina tun ranar dana fara ganinki da kuma maganar da kika fada akaina, kamar kin sanni!

Pls ki fada min wacece ke?

Kamar na sanki, Inaso na sani!"
"Owais baka gane ni ba har yanzu?

Ka dubeni dakyau, duk da nasan tsufa ya boye ainihin kamannina.." kura mata idanun shi yayi sosai"wadda kike min kama da ita, ta mutu yanzu bata araye,"
Murmushin takaici tayi"owais, zan fada maka abun da kake son ji akaina, ba yanzu ba, saboda a halin yanzu Daga ni har Danish muna bukatar kulawar likitoci saboda ba lafiya gare mu ba..."
nan take ta fayyace masu komai daya faru bayan Elder Ya ritsa da ita.

Hankalin su Ya tashi matuka sun kuma tausaya mata, sun jima suna fira a tsakanin su.

A ranar suka bar gidan gonar, Commender Haroon ne yayi masu booking Hotel Rooms din da zasu zauna, da taimakon adamu da ya shige masu agaba shi da yasan takan Birnin nasu..

Saida khala ta yi jinya a asibiti, na tsawon kwana biyu docs suna yi mata treatment na konuwar da kanta ya yi, Chief bai mi
a danish Asibiti ba saboda baya son ma wani ya gan shi, yasan yadda yake da jan hankali mutane zasu iya daukar hoton shi a boye wanda yin hakan zai iya jaza mashi matsala, tun da idan har Elders suka san suna araye, zasu nemi hanyar da zasu salwantar da rayuwarsu ne, sai dai ya dauki hayar Likitan da zai duba shi a boye, Cikin kwana ki biyu ya dan ji saukin jikin shi.

Ganin sun murmure Yasa Chief Ya fara tunanin Komawa da su Nigeria, koda ya tuntu6i Haroon da maganar komawar su bai goyi bayan su koma tare da su ba, saboda rayuwarsu tana a cikin ha
ari, In har Elders suka san suna araye sai sun nemi hanyar da zasu kashe su saboda sune silar da aka kai musu farmaki, kuma yadda suka ci amanar su ba zasu ta6a
yale su ba, dole su dauki fansa akan shi
wara su nisanta su daga Nigeria har zuwa lokacin da zasu kawo
arshen Elders.

Maganar Haroon ta ankarar da shi kuskuren da ya ke kokarin yi dama yana zargin akwai sa hannun nashi a ciki!

In har ya koma da danish cikin yan uwansa Elders zasu iya sani tun da yasan suna da yan le
en asiri.
basu gama yanke shawarar inda zasu boye su ba, Chief Ya ce ma Haroon zai nemi shawarar khala ya ji ra'ayinta.

Bayan daya samu Khala a dakin ta, ya fada mata abun da suka tattauna da Haroon cike da damuwa tace sunyi tunani mai kyau tabbas idan Elders suka san suna araye zasu kashe su ne!

Amma tana neman alfarma agurinsa, Ya taimaka Ya ha
a Danish da Iyayen sa!

Tana son ya cika burinsa, rayuwa ba tabbas batason ya mutu bai gan su ba"!

Shi kanshi baida burin daya wuce danish Ya ha
u da iyayen sa, sai dai baya jin zai iya ha
a shi da mahaifinsa tun da har yanzu bai kai ga gano su wanene ke da sanya hannu a kurkukun kaddara cikin Uncles din sa ba, wannan dalilin ne yasa shi yanke shawarar zai hada shi da mommyn shi amma fa ba zai hada shi da daddynsa ba har sai zuwa lokacin da suka kammala bincike.
kwata kwata Khala bata nuna mashi tasan wanene Elder ba, ba irin magiyar da baiyi mata ba akan ta fa
a masa wadanda ta sani a cikin Elders !

Kuma yana son yasan tayaya akai tasan Danish cousin dinsa ne dan uncle Hateem! amma ta
i ta sanar da shi, daya matsa lamba tace in har yana son yaji amsoshin tambayoyin shi toh ya koma da ita Nigeria ya kuma hada kowa na family dinsa a estate dinsu, ita kuma tayi masa alkawarin a wannan lokacin ne zata fayyace mashi wacece ita sannan kuma zata tona wani sirri na family din su agaban kowa"!
maganarta ta
aure mashi kai, Ya rude ba kadan ba, amma bai musa mata ba,
Abun daya sa khala ta
i ta sanar da shi ta za6i ya koma da ita Nigeria ya kuma tara kowa na family dinsa, badan komai ba sai don tana son ta cika burinta na ganin ta tonawa Elder asirin agaban Ahlin sa.

Masu karatu kunji dalilin dayasa Owais Ya roki alfarmar yana son ayi family meeting a ranar birthday dinsa, saboda bazai iya jira har sai date din family meeting yazo ba, kuma yana son kowa na family dinsu ya halarta duk don ya cika sharuddan Khala!

Hakan na nufin dama can Owais Ya san da zuwan Khala.
___________________________
Bayan daya fa
a ma Haroon yadda su ka yi da Khala, shima ya goyi bayan ya hada Danish da mommynsa a boye, tun da ba'a Nigeria ta ke da zama ba, ita kuma khala ya bashi shawarar in sun koma Nigeria da ita su boye ta a guest house din sa kafin zuwan ranar da zai kaita estate din su, Chief yaji dadin shawarar Haroon.

Su uku suka san da wannan maganar, batare da 6ata lokaci ba, Dg Ya kira Sheikha Mujeedat awaya bayan sun gaisa ya fada mata cewa game da binciken da ya ke yi akan Danish, Ya gano cewa dagaske babynta ne da ta haifa babu rai shekara ashirin da suka wuce, yana tunanin akwai wadanda suka kulla makirci gurin raba su da shi.."
Bai
are maganar ba, ta katse shi da cewa dama ita tajima da ji aranta jininta ne, saboda kaunar da Hateem ke yi masa da kuma kamanninsa da Hateem! shiyasa ta yi dna test din nan, amma tana so tasan su wanene suka rabata da shi?

Meyasa su ka yi hakan?

Laifin me tayi masu da har yasa suka rabata da yaronta tsawon shekara ashirin, bata san yana araye ba, daga haihuwarsa ko
umin jikinta bai ji ba, ba'a bari ta gan shi ba aka rabata da shi, akayi mata
aryar ya mutu! ita kawai so take ta san su wanene su ka yi mata aika aikar nan"!
cikin lallashi chief yace tayi hakuri, ta kwantar da hankalin ta, Sun kusa kammala bincike akan wadanda suke zargin sun raba ta da shi, Yanzu haka da ya ke yi mata magana yana a tare da Omair dinta, sun riga sun fa
a masa cewa itace mommynsa, kuma tun da yaji hakan ya matsa lamba akan su ha
a shi da mamansa, ta taimaka in zai yiwu yana son ta ha
u da shi, amma baya son kowa ya sani! saboda rayuwar yaron tana a cikin ha
ari, miyagun da suka rabashi da su suna nan suna farautar rayuwarsa, ya zamana komai cikin sirri zasuyi shi.
kusan ru
ewa tayi saboda farin cikin jin cewa zai hada ta da dan ta.

Cike da zumudi tace karya damu, in sha Allah zata kula da komai, ba zata bari kowa ya sani ba, yanzu ya fada mata da yaushe zai turo shi canada"?
Chapter 179 · 0% Book details