← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 174 OF 201

Sashe 174

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basu dira a ko'ina ba, sai cikin dakin Khala, kamar an wurgo su daga sama, suka fa
o kasa.
wannan jinin da su Chief owais suka gani malale a kasan dakin Khala, ba jinin kowa bane face jinin da Gabriellah ta amayar, da hannu khala ta dinga buga mata dunduna, ta dinga sakin aman jini har saida ta fitar da jinin da ta sha.
ewa khala tayi da sauri ta nufi daya daga cikin tulunan dakinta mai dauke da ruwa mai sanyi, ta kinkimo tulun ruwan da hannunta daya, yayin da dayan hannun ke a ruke da sandarta, ta dawo gaban Gabriella ta
warara mata ruwan a jikinta.
sai lokacin ta fara dawowa hayyacin ta, aje tulun kasa khala tayi, ta zukunna tare da kwalfar ruwa a tafin hannunta ta wanke mata fuskarta, ta kwafa mata bakin tulun abaki ta shiga kuskure bakin ta, duk wannan abun da khala tayi mata bata san wacece akanta ba, saida tasha ruwa sanyi ya ratsa makoshinta, tana dagowa da rinannun idanunta suka shiga cikin na khala, fashewa tayi da kuka tamkar ranta zai fita, cikin sauri khala ta rungumeta a kirjinta, ta shiga lallashinta, tasan ta da zuciya, cikin shesshekar kuka ta zayyana ma khala abun daya faru tsakanin ta da tsohuwa inno, tace mata tayi hakuri ta jure, ta manta da komai, yanzu ga taimako sun samu, sojoji sunzo har ma sun ku6utar da fursinonin kurkukun gaba daya, a lokacin wani ihun farin ciki ta saki, arude tace mata ina dan uwanta gabriel?

Shima sun fita da shi"?

Khala tace mata eh, sune ma na farko da aka tafi da su" ta fa
a mata hakanne don ta samu ta shawo kanta tabi su su tafi.

Cikin sauri Khala ta nufi bookshelves din dakinta ta zaro kundi biyu
aya na tarihin kurkukun
addara
ayan kuma littafin rijistar fursinoni ne ta rungumesu a hannunta ta nufi wata tsohuwar jakar fata dake makale jikin bango ta curota ta zazzage kayan cikinta, ta zura kundaddakin a ciki, Gabriella duk tana kallon ta bayan data gama ta mi
a mata Jakar tace ta ruke ta da kyau, suna da mahimmanci, Idan ta fita daga kurkukun ta bama sojojin, tace mata toh.

Batare da bata lokaci ba, Ta janyo hannunta, suka fito daga dakin, lokacin da suka karasa gaban sojojin dake tsaron tagogin rufin ta damka masu gabriela tace su tafi da ita, cike da tashin hankali tace ma khala tazo su tafi tare, khala tace a'a su fara tafiya zatazo daga baya, idan sojojin sun kammala ya
in zata biyo su, fashewa da kuka Gabriella tayi, ta sanya musu rigima akan bazata tafi ba in har khala ba zatazo su tafi atare ba, bata son ta tafi tabarta, gani take kamar zata mutu ne..
ganin zata 6ata musu lokaci yasa sojojin suka tasa
eyarta, tana ji tana gani suka rabata da khala, har ta fara bin igiyar bata daina waiwayen Khala ba, tana atsaye tana kallonta, fuskarta dauke da murmushi tace karta damu, tayi mata alkawarin indai da rai da lafiya zata zo inda su ke, sannan idan ta hadu da dan uwanta Gabriel ta gaishe mata da shi.
itama tana kuka tace ta kula mata da kanta, duk runtsi duk wuya karta bari ta mutu, tana son ta.." bayan Gabriela ta dura ta rufin, ta rarrafa ita kadai tana kuka tabi hanyar da zata 6ular da ita...

Saida sojojin dake tsaron gurin su ka ce ma khala tabi ta su tafi tace masu a'a, bazata iya tafiya batare da ta ga karshen fadan ba, saboda akwai burin da take da shi, tana son taga nasarar su akan idanunta, in har ta tafi zullumi da fargaban a wani hali suke a ciki bazai bari ta zauna lafiya ba.."
badan sun so ba suka
yale ta.

Idanun ta cike tab da kwalla, ta juya ta nufi hanyar komawa dakinta, zuciyarta a cike fal da kewar Gabriella, tana son yarinyar ta shaku da ita, tana son su sake haduwa sai dai tana ji aranta da wuya ta rayu, bayan irin 6arnar da tayiwa Elder bayan ta shiga dakin kasa zama tayi saboda zullumin awani hali su Danish suke a ciki..

Ta yi zurfi a tunaninta kwatsam tajiyo takun tafiyar mutun abayanta, juyowar da za tayi keda wuya idanunta suka sauka akan Elder Obinna daya fa
o a fujajen jikinshi sai tsuma ya ke yi saboda tsantsar bacin rai, har wani gurnani yake fitarwa..
wani irin faduwar gaba taji, Hankalinta ya tashi matu
kallon kallon su ke jefawa junansu sam ya kasa magana, tun da taga ya kawar da idanunsa daga kallonta ya mayar da su akan akwatinan karfen da ke a kasa da buhunbuhunan makaman da tabari, nan fa tasha jinin jikinta, zufar tashin hankali ta fara wanko mata fuska, adabarbarce ta furta"E..el..elder...."
bata karasa maganar ba, Ya daka mata tsawa tamkar zai fasa dodon kunnanta, Yana huci cike da bakin Ciki Yace"kin bani mamaki!

Dake za'a ha
a baki a ci amanata? nayi kuskure dana barki araye tun farko.."
duk da tsoron shi da take ji hakan bai hanata yin karfin halin cewa"kamar yadda nima ka bani mamaki Obinna, kaine ka fara cin amanata tun farko.."!
bata
arasa amayar da abunda ke aranta ba, taga ya nufota gadan gadan Jiki na bari ta soma ja da baya, zagaye dakin suka dinga yi, ta soma yin tsalle tana hayewa kan tukwanan kasan dake adakin cike da tsoron karya kamata, cikin tashin hankali ta dinga daddafe bangon bayanta da tafin hannunta wanda ya 6aci da jinin data goga a jikin Gabriella, wanda silar hakan Yasa sahun yatsunta suka fito radau a jikin bangon kamar an zana shi, gaba
aya saida ta faffashe tukwanan da kafafunta, da ta ga zai cimmata ta 6ace ta koma kan gadonta, ransa ne ya 6aci nan take yayi tsafi gaba daya gadon da take akai ya jirkice wanda silar hakan ta kundumo
asa har kanta Ya da ku ta suma.

Bata kara sanin inda kanta yake ba, sai dai ta farka ta tsinci kanta a dakin da yake hukunta wadanda suka ci amanarsa nan take ta fahimci shine ya kawota nan..
(Kunji yadda akai Elder Ya rutsa da Khala
Wata irin jijjiga Jeremiah ya yi, A lokacin ya gama daidaita jikin shi, dama abunda ya tsayar da shi kenan, babban kuskuren da zasu yi shine su bari Jeremiah ya baro bakin rijiyar, domin kuwa in har ya dira
afarsa duk wani mai sauran rai da babu sihiri a jikin shi sai ya mutu in ba wani iko na Allah ba, aikuwa yana
aga
afarsa kafin Ya dire ta
asa, Danish ya watsa da gudun gaske ya durfafe shi, yana
arasawa gaban shi ya daka uban tsalle ya haye kanshi ya cakumeshi da hannuwan shi biyu, da iya
arfin shi na
arshe ya ingizasu gaba
aya suka rubza cikin rijiyar, nan take murfinta ya maida kan shi ya rufe makullinta ma ya datse kan shi...
(Evil wall rijiya ce mai fa
i da tsawo, tsohuwar rijiya ce da tayi shekaru aru aru tun zamanin kakannin Elder tun kan Elder ya gurfanar da kurkukun
addara rijiyar ta ke anan, gaba
aya rijiyar ginin dutse ne tana da hatsarin gaske mutun bazai iya rayuwa acikin ta ba idan har babu sihiri a jikin shi, saboda giggan shaidanun dake rayuwa a cikin ta, ko ma
iyi na banayiwa fatan ya tsinci kanshi a cikin rijiyar koda a mafarkinsa ne saboda izayar da zai taras, daga jikin kowace kusurwa ta rijiyar yanace dadda6e da Evil spiders da manyan kunamu jibga jibga, ga giant snakes din dake bin jikin bangwayen rijiyar, gaba dayansu evils ne suka rikida ba ainihin kwarin ba ne.
ga wasu zanunnuka masu ban tsoro jikin bangwayen rijiyar, ga wasu halittu bakake munana, masu idanuwa barkatai a jikin su, wasu gashi gashine buzu buzu a jikin su, wasu halittun kuwa har kananun macijjai suke fitarwa ta bakin su, bala'i iri iri, daga kasan rijiyar wani irin fadi gare shi, hada koramar ruwan jini na sihiri da manyan duwatsu, ga wata gajeruwar bishiya mai rassa tare da manyan ganyayyin da sukayiwa kasanta inuwa, daga kasan ta akwai wata shimfi
a ta alfarma da akayita da jan carpet mai fadi anan giant din da suke horaswa ya ke zama kamar gunki bazai taba motsawa ba, in ba evils sun tashi bashi horo ba, koda yaushe da bakar izayar da zasuyi mashi, kamar yadda na fada abaya, tun suna bashi wahala su tsoratar da shi har sai sun kaiga bugun shi da bulalai su dinga azabtar da shi da masifu iri iri tun yana kuka ya suma su farfado da shi, har sai ya koma yana yin komai daga kwance tun daga kan amai, fitsari, kashi, saboda azabar da su ke yi masu takansa su fita hayyacin su, da zarar Elders sun tura ka rijiyar kayi bankwana da farin ciki da duk wani jin dadi, kunnuwanka ba zasu
ara jin sauti mai dadi ba, sai na tashin hankali, baka da abinci daya wuce
wari da kwan halittun dake a ciki, ruwan sha kuwa sai dai kasha jinin dake a cikin tulunan da suka aje maka, ko wanka baka isa kayi ba, cikin kazanta zaka zauna shiyasa dayawa matasan da suke diba idan zasu basu horon zama giant da wuya suke tsalle rijiyar shaida nu, mafi rinjayen su anan suke rasa rayukan su.

Rijiyoyin suna da yawa kowani giant a rijiya daya zasu kulle shi, kamar kabari, babu shige babu fuce, rayuwar kunci da azabtarwar, daga lokacin da tsoro yabar idanunsu, suka jure wahalar har suka fara rama bugun da evils keyi masu idan suna gabza fada atsakaninsu to daga nan evils din zasu gane zai iya jurewa, anan ne zasu zana mashi tattoo abayanshi yana kuka da ihu kamar ana zare ranshi saboda azabar ra
i, irin tattoo din da su ke yi masu, ba irin wanda muka saba gani anayi bane, da akaifu evils suke zana masu shi abayansu, a fa
an da suke gabzawa da giant, idan yayi nasarar jure azabtarwar su ya rayu bai mutu ba, daga nan ne zasu samu matsugunni a jikin shi, su gauraya da shi ta yadda zasu ba shi
arfin su.
Chapter 174 · 0% Book details