← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 201

Sashe 117

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka zalika Hajiya Madina tana a zaune gefen Senate Lateef, hannunta ru
e cikin nashi sai tausar shi take yi ganin yadda ya yi sukuku kamar ba laka a jikin shi..

Sai da Shikeh Imam ya kammala kallace su tsaf kafin ya samu guri ya zauna kan Sofa din da ke fuskantar su, duk suka bi shi da ido gaba
aya sun
agara da son jin me zai ce..

"Ana ta ja mana rai, ni banga amfanin
auko mana malami ba, sai ka ce dai masu iskokai balle ace za'a mana rukiya.."
faryart ce take gunaguni bata kai ga
arasawa ba, Zayn ya make bakinta da tafin hannunsa ya buga mata warning, harara ta watsa mashi da yake ba kunya ce ta ishe ta ba..

"Nifa na rasa ganewa, kaina ya kulle, meke faruwa ne?

Meke damun kowa ne?

Nifa bana son tashin hankali, kowa ka tambaya sai ya ce a jira sheikh a jira sheikh ga sheikh din ya zo amma ya yi shiru yana ta kallon mu kamar ya samu tashar bollywood..."
Rai a
an bace Dr.Nawaz ya yi maganar shima da yake ba kunya ta ishe shi ba, tsagera ne..

"Karka kuskura ka
ara magana!" A
an tsawace Nadeem ya fa
a, kallonsa ya yi tare da yamutsa fuskarsa batare da ya furta kalma ba.

"Mijin mace
aya, yau ahalin namu ba lafiya, kamar masu zaman makoki, ni bansan meyasa ka matsamin akan in zo ba, ina tsaka da hidimar biki kasa na baro dangina, nayi nayi ka fa
amin meke damunka ka
iya, ga sheikh din ya
araso ya wani tsare mutane da idanunsa kamar wasu masu laifi, wlh zan tafi ne idan na gaji da zama, kuma dai kasan bana zaman jin wa'azi ehe..." Her excellency Muhibbat ce ta fada tana kallon Abdul razak hada murgu
aramin bakin ta, tana karka
afarta..

Da yake yasan halin kayansa bai biye mata ba..

"Nifa Allah na gani, malaman sunnar nan ba burgeni suke yi ba, wlh da nasan tara mu za'a yi don a yi mana wa'azi ba abun da zai sa in wanko
afa in biyo mommy mu zo nan.." Cike da takaici Yusra ta yi maganar tana jifar Imam da harara a fakaice.

In a cool voice Hindu ta ce, "Pls, Yusra, mu
ara ha
uri, bai kamata kina fadin maganganun nan ba.." cuno baki ta yi ita ala dole an takura mata..

Gyaran muryar da sheikh Imam ya yi musu ne ya ja hankulansu ga dubansa, gaba daya suka tattara nutsuwarsu da hankalinsu a kansa, a hankali ya zauna kan Sofa din dake fuskantar kowannan su.

"Innalhamdu lillahee, nahmaduhu wa nasta'eenuhu wa nastaghfiruhu, wa na'oodhu billaahi min shuroori anfusinaa wa min sayyiaati a'maalinaa.

Wa man yahdillahu fala mudillilahu, wa man yudlil falaa haadiya lah "Alhumdulillah.

Indeed, all praise is due to Allah....'
an dakata yana dubansu kafin ya ce, "Sallu Alal nabiyyul Kareem, Sallallahu Alaihi Wasallam..."
atare suka ha
a baki gurin karasa ambaton Sallallahu Alaihi Wasallam
kafin suka fara yin salatin annabi, Faryat dai ta
i tsayar da hankalinta guri guda, bayan sun kammala ya soma magana cikin harshen turanci saboda yana son kowan nan su ya ji me ya ke fa
"Nasan gaba
ayan ku kun
agara ku ji dalilin da yasa aka umarce ku da ku baro komai da kuke yi ku zo nan, wata
il an takura maku amma abu ne na gaggawa wanda da bukatar ku ha
u domin mu nemawa kanmu mafita a tare game da musibar da ta kunna kai a family din nan..

"
Cike da tsantsar ru
ani suke jefawa junansu kallon kallon ga wa
anda basu san meya faru ba.

Numfasawa sheikh Imam ya yi kafin ya daura da cewa, "Kafin mu fara sanar da ku, ina so in fara tunasar da ku da nasiha, saboda gudun halin da zaku shiga..."
Maganganun sheikh Imam sun rikita lissafin kwakwalan su, sai zare idanunsu suke yi cike da fargaba.

Tun da ya fara yi masu nasihar suka yi shiru suna sauraran shi, ko tari babu wanda ya yi a cikin su, da alama nasihar ta ratsa zukatansu, jikinsu ya yi sanyi lakwas saboda tsoron Allah da ya
ara shigar su, duk da akwai tarin fargaba da zullumin abun da zai biyo bayan nasihar tashi don sun san dole akwai ma
asudin yin ta.

"Jazakallahu Khairan Malam, mungode da nasiha, Allah ne kadai zai iya biyan ka.." Hajiya Madina ce ta yi maganar cikin sanyin murya,
"Sai dai gaba daya hankalin mu ba a kwance ya ke ba, mun damu da ganin halin da mazajen mu suke a ciki, sannan babu Baba, Saratu ma bamu san ina take ba, munyi munyi su fa
a mana gaskiyar abun da ke faruwa sun
i sanar da mu, sun ce mu jira ka
araso za mu ji komai a bakinka, don Allah malam ka fa
a mana, koma menene in wani ya rasu ne in kuma wani abun ne a fada mana, we're all muslim mun yi imani da kaddara mai kyau da mara kyau,.."
Ta karasa maganar fuskarta a yamutse, gaba daya sauran suka tsoma bakinsu akan a fada musu meke faruwa.

Shiru Sheikh Imam ya yi, shi kanshi yana jin fargaban sanar da su, saboda ya lura akwai masu
arancin tawakkali a cikin su.

"Bismillah Owais, ka fada masu komai dake faruwa..." Ya fa
a idanunsa akan Chief Owais da ya raku6e kansa jikin Sofa, gaba daya suka mayar da dubansu gare shi.

Tunani ya ke yi taya zai fara sanar da su? ya zasu dauki abun?

Me zai biyo baya?

Ba kaitsaye ya fara sanar da su ba, saboda harshen sa yayi rauni, ba zai iya
aga muryarsa ya yi magana mai tsayi ba.

A hanakali ya zaro wayarsa daga cikin trouser pocket dinsa, ya mike cike da rashin kuzari a jikinshi ya
aura wayar saman c-table din dake a gaban Imam Malik, bayan ya kunna masu video din dake
auke da duk wani bayani game da gidan Kurkukun
addara da miyagun ayyukan da ake aikatawa a cikin sa..."
ure musu volume yadda kowa zai ji dakyau, zama yayi dirshan gaban table
in tare da sadda kan shi
asa..

Da ya ke cikin harshen turanci ya yi audio din kowannansu yana sauraro kuma yana fahimtar me ake cewa, tun suna jin abun kamar shirin wasan kwaikwayo har suka fara ru
ewa da jin irin azabtarwar da ake yiwa matasan yaran da basu ji ba basu gani ba.

Lokaci
aya suka ru
e, suka fara tambayar Owais wai dagaske ne abun da suke sauraro yana faruwa ko dai
agaggen labari ne na almara?

Gaba daya sun kasa yarda da gaske ne saboda aganinsu ba zai ta6a yiwuwa a rayuwar zahiri ba, don ko a tarihi basu ta6a jin makamancin labarin kurkukun
addara ba, sai dai abun da ya
aure musu kai chief Owais ne ya ke yin magana a cikin audio din, sun gane voice dinsa ne.

Hajiya Laura ta ce yaushe Owais ya zama
an jarida mai karanta hausa novel?

Abun da daure kai.."
Her excellency Muhibbat ta ce, "Ni na rasa ganewa, mu da muka zo don mu ji meke faruwa da mazajen mu why za'a kama bamu labarin
anzon kurege..."
Lokacin da audio din ya yi nisa hankalin wasu daga cikin su ya tashi matu
an matasan cikinsu har sun fara zubda
walla saboda yadda labarin ya ta6a zuciyar su har suna fadin wannan rashin imanin ya yi yawa, yaran nan ana zabtar da su wlh, saboda ba
in zalunci na wasu mutanan da babu Allah a ransu, kowa dai yana ta tofa albarkacin bakinsa, wadanda suka fi tausayi a cikin su irin su Jazz da Hindu da Zulaihat da Turai tuni sun fashe da kuka saboda tausayin yaran da ya kama su tsigar jikinsu har tashi take yi, musamman da aka zo kan labarin Unaizah da Majnoon wa'iyazubilla!

Kuka sosai suke yi abun ya ta6a zuciyar su, hatta Gimbiya Mujeedat saida ta matse
wallarta, itama Hajiya malika zuciyarta ta yi rauni ta dinga fadin Owais ku yi mana bayani mana, wani darasi ne ake so mu
auka acikin labarin nan?

Meyasa kuka kunna mana shi?

Ko dan mu
ara imani ne um?"
Cikin sanyin murya Owais ya ce mommy ki yi hakuri ki
arasa sauraran shi, ta ce toh Owais Allah yasa mu ji Alkhairi, duk rashin tausayin su twins saida jikinsu ya yi sanyi lakwas dama zuciyarsu a raunace take duk sunyi sukuku da su a ransu suna ayyana in da gaske labarin kurkukun kaddara ke faruwa ya wadanda abun ya faru da su zasu ji?

Dr.

Nawaz da Faryart da Yusra ko gizau basu yi ba, tabbas labarin ya ta6a zuciyoyinsu sai dai ba kamar sauran ba, saboda su a tunaninsu bazai ta6a zama gaskiya ba,
agaggen labari ne kawai, jin abun suke yi wani iri.

Ibad sarkin tsoro ga tausayi da ya addabe shi, tuni ya aje game din da yake bugawa, jikinsa sai kerma ya ke yi kamar mazari hakan yasa Sir Mubarak ya rungumo shi a jikin shi.

A hankali Zaki ya zaro hanky daga aljihu ya soma share
wallar dake gangaro masa saman kuncin sa, zuciyarsa ta karaya.

Shiekh Imam dake kallon fuskokinsu a hankali yake karantar yanayin su, tun anan ya fahimci masu rauni da marasa raunin cikin su..

Hatta Yazrin so take ta fashe da kuka ta kasa sai dai ta sadda kanta
asa, gimbiyar izza kuwa tun da ta fara sauraron Audio din bata motsa ba, dama ita haka take da wuya mutun ya iya karantar abun da ke a ranta ta yanayin fuskarta, saboda tsabar izza, Amma fa da alama ta razana da jin labarin kurkukun kaddara, duba da yadda yatsu ta suke ta kerma, cheeks dinta sun yi jawur saboda ka
uwar da ta yi, haka zalika Hajiya Jamila tausayi yasa ta kasa jurewa, sai faman sharce
walla take yi da yatsun ta.
Chapter 117 · 0% Book details