← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 158 OF 201

Sashe 158

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baby Junaid an girma yanzu sai dai har yanzu bai daina shagwa6a ba saboda step father dinsa ya sangartashi da gatanci, idan kagansu a tare ba zaka ta6a cewa bashi ne ya haife shi ba, hatta kayan jikin su kala
aya ne.

"Assalamu alaikum..

" sallamartace ta katse su, a tare suke dube ta, Murmushi ta sakar masu Junaid ya ambaci sunanta Mommy
"Na'am daddys Boy..." ta fada tare da kallon Zaki dake bin ta da kallon kauna.

"Sannu da kokori honey, Halan shine ya hana ka yin aiki, kullum baya gajiya da kawo maka assignment, har cewa nayi ya dinga bani inayi masa amma yafi son wahalar min da kai" ta karashe maganar tana zama daga gefen shi.
murmushin gefen fuska yayi mata"ai ni nace ya dinga kawo min inayi masa, saboda banaso ya takura min ke"
Taji dadin maganarsa
"kana ji da mommyn babynka, yanzu dai ya maganar zuwa gidan biki, please ka barni inje, gaba daya satin nan ban leka ma su ba, nasan me kake mawa, wlh zan kula maka da kaina.." ta fa
a tana marairaice masa fuska.

"Ki fahimce ni wifey, bawai banso ki motsa jikin ki bane No, fita ayanzu bazaiyiwu gare ki ba, tayaya zakije gidan biki kina fama da laulayin ciki"? zumbura masa baki tayi.

Hankalin baby junaid ba akansu yake ba, ya mayar da idanunsa akan plasma tv yana kallon cartoon.

"Ai na daina laulayin, Jikin da sau
i yanzu...

" bata kare magabar ba, taji tashin zuciya, nan take ta soma yun
urin amai kafin tayi wani yun
uri aman ya kubce mata kaitsaye ta kwarara shi asaman lap dinsa, zare idanu tayi tana faman jan numfashi, babu alamun yaji kyankyami ko haushin ta sai ma murmushin daya sakar mata"kinji sau
i ko?

Kuma kin daina laulayi"?

Ya fa
a da zolaya, cike da jin kunyarshi ta sunnar da kanta
asa.

"A haka zakije gidan biki, kina yi masu amai, su kansu zasuji ba dadi" idanunta ne suka ciko da kwalla"na hakura da zuwa, amma pls ranar biki, kabarni inje"
Jinjina kai ya yi"In sha Allah zan barki kije, yanzu tashi muje toilet ki wanke min wandona da kika 6ata da amai"
atare suka mike, tare da barin falon, kwata kwata Junaid bai lura sun fita ba,
"Junaid...

" muryar khadija mai aikin su ce ta katse shi, dagowa yayi tare da dubanta yayin da take nufo shi "Aunty Khady, yunwa nake ji, har yanzu baki gama mana girkin bane"?

Ya fada yana yamutsa mata fuska.

Murmushi tayi sai naga tayi min kamanceceniya da tsohuwar mai aikin Anila.

"kwantar da hankalin ka, na kammala shirya mana Dinner, Ina aunty Aneelerh da daddyn naka ne"? adan rude ya juya yana duban gurin da suke ganin babu su yasa shi cewa"nan suke zaune fa,
ila sun shiga
aki"
"Okay, kaje ka fa
a masu dinner is ready amma ka fara knocking room door din kafin ka shiga kamar yadda na koya maka"
Amsawa yayi da toh ya mike da sauri ya nufi bedroom din mommynsa..

Shin wacece Khadija mai aikin Anila? ko zaku iya tunawa da Yan uwan mariganya Aisha wadda kuka fi sani da (ANA)
_Janet da Esther, wadanda bayan da suka musulunta Ana ta sauya masu suna, Janet khadija, Esther (Zainab) tun lokacin da al'amarin Mutuwar Ana Ya fasu sunji tashin hankali da bakin cikin abin daya faru da yar uwarsu a lokacin da labarin ya ris
e su, wanda silar hakan yasa gaba dayansu suka kamu da depression har jinya sukayi gadon asibiti, sunji mutuwar Aisha, saboda suna son ta fiye da komai, tamkar uwa take a gare su, da ya ke Anila tasan basu da kowa a arewa kuma marayu ne tasan idan suka koma
auyensu na kudu a matsayin musulmai danginsu ba zasu kar6e su ba, wannan dalilinne yasa ta kai kukan ta gurin abie a lokacin da sukazo cikin mawuyacin hali, ta rokesa akan ya taimaka ya bar su su cigaba da zama tare da su, abie yace ko bata fada ba shima bazai bari su koma ba, zai ruke su a hannun shi, kuma zai dauki nauyin komai na rayuwarsu, tun daga lokacin zainab da Khadija suka kasance karkashin kulawar Abie da iyalin sa, a yanzu haka Zainab tana zaune agidan abie yayin da khadija ta ke aiki agidan Anila, Yanzu haka sun kusa yin aure har an sanya bikin auran su_
~_______________________
*THE DAY BEFORE WEDDING DAY
Tana a kwance cikin bathtube wanda ke a cike da ruwan
umi daidai kirjinta ruwan ya tsaya ta kishingide kanta, idanunta suna a lumshe tayi zurfi a cikin tunanin ta.

"burina zai cika na ganin nayi aure sai dai farin cikina ragagge ne..."
Bata
are zancen zucin nata ba, tajiyo sautin
wasa kofa daga waje, Kwan!

Kwan!!

"Unaisah!

My baby Girl!

Kina ina!

Daddynki Ya dawo, Yana son ganin ki" Benazir ce ke kwa
a mata kira..
waro idanu tayi cike da farin ciki ta yi saurin
auraye jikinta da ruwa, ta fito daga kwamin ta warci towel dake rataye jikin hanger ta yi daurin gaba da shi.

Sai rawar jiki ta ke yi jin daddynta ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa joss, shigowa bedroom dinta ta yi adaidai lokacin Benazir ta shigo dakin.

Unfortunately, garin rawar jiki, sul6i ya kwashi kafar Unaisah gaba daya ta tafi zata kifa, a gigice Benazir ta nufeta kafin ta karasa tuni ta kife
asa nan take daurin towel din da tayi ya warware ya dawo kan qugunta sumar kanta ta baje kasa.

"Subhanallah, daughter, tashi baki ji ciwo ba!

" kasa amsa mata tayi saboda zafin dataji sakamakon dakar tiles da kirjinta yayi.

Cikin sauri Benazir ta nufe ta, tana kokarin kai hannu don ta mi
ar da ita, kwatsam ba zato ba tsammani ta yi arba da waist tattoo dinta ya zanu ra
"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..."
Ta fa
a da tashin hankali tsantsa akan fuskarta.
sallallamin da tayine yasa Unaisah ta tattara sauran karfin daya rage mata a jikinta tayi saurin mi
ewa tare da jan towel din ta daure kirjinta.

Ta yi zaton fa
uwar da ta yi ne yasa Benazir ta
aga hankalinta hakan yasa tayi saurin furta"mommy, banji ciwo ba, lafiyana lou,"
daura hannu biyu Benazir tayi asaman kanta tana fadin"nashiga Uku!

Unaisah Uban wa ya zana maki tattoo a waist din ki!

Yaushe akai!

A ina"?
gabanta ne ya fa
i aru
e ta zabura ta mike Tsaye jikinta ya kama kerma kamar mazari duk tabi tasha jinin jikinta..

"Bakiji ina magana bane?

Uban wa ya zana maki tattoo?

Da yaushe akayi maki shi ."
ta fa
a rai a6ace ta fusgota ta juyar da ita tare da tum6uke towel din ta
ura idanunta akan tattoo din, zanan giant snake ne nanna
e da sunan Garkuwa da wani irin salo akayi tattoo din launin black and red ya yi bala'en yin kyau a fatarta.

Unaisah duk tabi ta rude tsabar ka
uwa cikin sauri ta mayar da towel din da benazir ta cire mata ta mayar kan kirjinta ta daure shi.

"banza shashasha!, kina a cikin hayyacin ki kuwa?

Ba zaki amsa min tambayana ba?

Sunan uban waye garkuwan?

Ta fada kamar zata rufeta da bugu, ta tsorata sosai, bata ta6a ganin mommynta cikin fushi irin na yau ba.

Cikin rawar murya ta furta"nick..nick..

Nickname dinsa ne"_
"Shi ubanwa"!

Ta katse ta da tsawa.

"Dad.. danish..." zare idanu Benazir tayi"na shiga Uku Unaisah, baki da hankaline? tayaya zaki yi zanan tattoo da sunan wani kato a waist din ki, Kin manta gobe za'a daura maki aure?

Wani irin abun kunyane kikeso kija mana Unaisah?

Idan mijinki yaga wannan me kike tunanin zai biyo baya..."
ta fa
a idanunta cike tab da kwalla, ji ta ke kamar ta kikkifa mata mari kota huce takaicin da ta ke ji.

Cikin shakakkar murya ta furta"ki yi hakuri mommy, nayi kuskure..

"
"Sorry for your self Unaisah, wlh ba zaki kwana da tattoo din nan a jikin ki ba !

Wai meke damunki ne?

Bayan kinsan haramunne yin tattoo a jiki?

Ina hankalinki ne?

Girgiza kai tayi batare data iya furta kalma ba..

"dole ki goge shi a yau din nan kafin gobe, ki rasa sunan wa zakisa sai sunan matacce mutumin da babu shi araye, Ina laifin ma sunan wanda zaki aura"!

Ta fa
a cikin bacin rai...

Zafafan hawaye ne suka wanke fuskarta masu dumi
In a weak voice ta furta"bazai gogu ba, in har ba fatar jikina za'a gurje ba.."
"Kina nufin permanent tattoo ne"?

Girgiza kai tayi"temporary tottoo ne, amma zai dauki lokaci kafin ya goge"
"Hmmm, nasan maganinki, Idan na fa
a ma dadynki, kin yi bayani kuma Allah ba zaki kwana da shi ba, lalle zansa in dame shi, wallahi kin ban kunya, har kika iya zuwa wani
ato ya zana maki tattoo a waist
inki don hauka"
tana fada ta juya zata fuce, da gudu tabi bayanta tayi saurin shan gabanta tana kuka tace'dan Allah ki rufa min asiri kada daddy yaji, wlh ransa zai baci, zai yi fushi dani, bana so na rabu daku kuna fushi dani, zan iya samun matsala agidan aurena.."
ta fada tana jan magina, hawaye wasu nabin wasu akan fuskarta.

"nayi danasani mommy banyi zaton zai zamarmin matsala ba sai da kika ankarar dani, ki yarda dani wallahi ba namiji ya zana min shi ba, babu wanda yaga tsiraici na, tsautsayi ne yasa naje akayi min a tattoo studio kuma artist din da tayi min macace, wallahi bata ga jikina ba, iya fatar gurin da tayi zanan tagani kadai ban kware jikina ba, kuma wallahi a private room dinsu ne babu wanda ya gani"!
cikin shesshekar kuka ta fa
"Mommy ki taimaka min mu nemi mafita kafin gobe..."
kalaman Unaisah sun karya mata zuciya, wani irin tausayinta ne ya kamata.

"Unaisah meyasa kika yi tattoo da sunan garkuwa"?

Ta kuma tambayarta!

"Zan fada maki amma kada ki fadamawa kowa, ki rufa min asiri, nasan zakiji haushina watakilma kiyi min kallon mara hankali amma wlh ba haka bane, soyayyarshi jarabtace daga Allah, in ba haka ba tayaya zuciyata zata dinga azabtar dani da son matacce?
Chapter 158 · 0% Book details