Sashe 5
The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Karya kike kice bakisona, babu macen dana ta6a nuna inaso tayi rejecting dina, don haka kema akwai soyayyata acikin zuciyarki, idan ma kina jin kunyata ne to ki daina, ni ba Uncle dinki bane, ashirye nake da in aure ki, Aisha kiyi tunani akaina kafin ki yanke shawara, zan jira naji daga gare ki"
yana fadan hakan yayi tafiyarsa, gaba daya tashiga halin damuwa kuma ta kasa sanarma kowa, hatta Benazir da Aneelerh basu san da maganar ba, kusan sau biyar Alhaji musa yana tuntubarta a waya don yaji in ta canza ra'ayi amma ta nace akan ita bazata iya auren shi ba, tana da wanda takeso, daya matsa mata akan ta fada masa wanene takeso sai tace mashi yaya shureim ne, a lokacin ji yayi kamar ya binne ta da ranta saboda bakin kishine da shi, ya ji zafin furta sunan shureim da tayi, zuciyarshi ta raya mashi cewar ba ra'ayinta bane Shiekh imam ne ya cusa mata nasa ra'ayin dama ya nuna yafi sha'awar ta auri shureim daga nan ne ya kuduri aniyar saiya shiga tsakanin su.
Har gida yaje ya samu shureim Ya tambayesa meke a tsakaninsa da Aisha, dr shureim yace babu komai face mutunci, shi ya dauke ta kamar kanwarsa.
Uncle musa yace bai yarda ba, in har yana son ta ya fada mashi zaiyi mashi hanyar auren ta, daya matsa mashi da tambaya kawai sai yace mishi eh yana sonta amma bai ta6a sanar da ita ba.
Hankalin Uncle musa ba karamin tashi yayi ba, saboda ya fahimci dukan su suna son juna, kuma In har Shureim Ya furta yana son Aisha tofa babu makawa sai Sheikh imam Ya bashi ita.
hakan yasa shi yanke shawarar komawa gurin imam malik don ya kara rokonsa akan ya bashi ita, kusan sau biyar yana zuwa gurin imam amma ya rufe ido akan bazai ta6a aura masa aisha ba, ta ko'ina babu sauki, har aunty laura yaba cin hanci na makudan kudi donta karkato da hankalin sheikh imam akansa amma duk abanza, itama aishar ba irin magiyar da baiyi mata ba akan ta amince da soyayyar shi akarshe sai tayi blocking duk wata hanya da zata ha
a ta da shi, hatta gidansu Benazir ta daina zuwa sai dai Benazir tazo gidansu ta same ta, ranshi ba karamin baci yayi ba, shi a ganin shi bata yi mashi halacci ba, kodan saboda dawainiyar da yayi dasu yaci ace ta saka mashi amma saita butulce dama shi baya abu dan Allah sai idan yasan zai samu riba.
bayan wasu kwanaki Uncle musa ya
auke
afa da zuwa Gidan yayansa kwata kwata suka daina jin duriyarshi, da Benazir ta sanar da Aisha baya kasar Ba karamin dadi taji ba, kuma ta saki jiki ta cigaba da zuwa gidan, wani lokaci atare suke zuwa gidansu Aneelerh wani sa'in kuma Anila ce ke zuwa gidajen su ta kawo masu ziyara, har takaiga iyayen su na ziyartar junan su.
Daga baya da soyayyar Aisha ta fara addabar Dr shureim har takaiga dakyar yake runtsawa saboda tunaninta, baya da burin daya wuce ya aureta, aranar daya shirya tunkararta don Ya fada mata irin kaunar da yake yi mata, A lokacin Aysha da Aneelerh sunzo Gidan su suna a dakin Benazir Suna fira, A bakin kofar dakin ya tsaya yana tunanin taya zai tunkareta da maganar?
Zata kar6i tayin soyayyar shi ko kuwa? yana jin fargaban Aisha taki amincewa da shi shiyasama tuntuni yaki sanar da ita saboda fargaban amsar da zata ba shi.
Har ya zaro waya daga Aljihu da niyar Ya kirata don ta fito su ke6e, kwatsam kunnuwansu suka jiyo mashi firar da su ke yi..
"Yanzu tun da mun kammala karatu me ya rage mana"?
Benazir ce tayi tambayar.
Aneelerh tace"Aiki da kuma Aure, amma Abie yace bazai bari in fara aiki a private hospital din daya bu
e min ba har sai na tsayar da miji"
Benazir tace"Why not Ki ba Uzair damar ya turo da magabatansa?
Tun da naga Jininku Ya ha
u da shi"
Murmushi Anila tayi"Wai da Ke nake Jira, Idan Kinba Taj damar Ya tura da nasa magatan Gidan ku nima sai in ba Uzair Damar Ya tura gidan mu..." wani kallo mai kama da harara Benazir tayi mata..
"Pls mana ki amince masa nasan fa Kin mutu akan kaunarsa amma sai ki ta wani Ja mashi Aji"
"hmmm nifa ba aji nake ja masa ba, Ina tunanin ta yadda zan tunkari mommy da wannan maganar, daddy baida matsala nasan zai amince min, amma mommy bansan ya zata dauki abunba kinsan Mommy bata son dan jarida sannan shi ba dan wani Hamshakin mai kudi bane..."
Tun da suka fara magana Aisha bata tsoma baki ba, tayi shiru kamar hankalin ta baya akansu, har saida Benazir ta
an dafa kafadarta tukunna ta mai da hankali akansu.
"Meke damunkine?
Tun dazu kin yi shiru ba ki ce komai ba, ko baki ji abunda muke magana akai bane"
Murmushi tayi"Naji mana, mamakine ya kamani, Naji kuna maganar Taj da Uzair su wanene su din?
Yanzu duk kawancen mu daku ashe har akwai wani sirri naku da bansani ba"?
Dariya su ka yi, Anila tace"Ay mana afwa Ustatha, ba haka bane, wlh mu ma bamu dade da sanin su ba, kin tuna ranar da muka fada maki zamuje shopping mall?
One week da dawowarmu"?
"Hakane na tuna, Ay ranar na fadamaku Uzirin daya hana ni fita"
Benazir tace"toh A ranar muka hadu da su, kyawawan Samari kuma sun kwanta mana arai"
Taya su murna tayi Allah ya sa su zama Alkhairi agare ku
Suka amsa mata da ameen.
Anila tace"pls muna so muji ra'ayinki, Donni bana so mu riga ki yin aure, nafi so yadda muke aminnan juna, Muyi aure atare ya'yan mu su taso a tare"
Benazir tace"Aisha fa bata da matsala, Kinsan Allah yayi ta da farin jinin samari iri iri, attajiran masu kudi, Manyan Malamai sai ta zaba ta darje, Ko yau ta fidda miji baba Imam aurar da ita zaiyi Allah"
ta fada tana dariya, Murmushin takaici malama Aisha tayi Cikin raunanniyar murya tace"Bazan boye maku ba, dani daku mun riga da mun zama daya, Munsan sirrin Juna, Wallahi bana alfahari da farin jinin da nake da shi, saboda mafi akasarin mazan da suke sona ba dan Allah bane sai don Surar Jikina, Wlh Benazir da wuya namiji yazo gurina da sunan soyayya batare daya neme ni ba, Ina jin bakin ciki da taikacin hakan, ni nasan zaiyi wuya asamu wanda zai soni dan Allah..." dakyar ta kare maganar saboda kukan daya ciyota, Kalamanta sun karya masu zuciya.
Cikin shesshekar kuka tace"Inason Aure fiye da tunaninku, inaso in raya sunnar manzon Allah SAW amma taya zan samu wanda zai soni dan Allah"?
Gaba daya tausayinta ne ya kamasu.
Lallashinta suka somayi tare da kwantar mata da Hankali, su ka ce In sha Allah zasu tayata da addu'a Allah ya bata miji nagari wanda zaiso ta tsakani da Allah.
Dr shureim dake a labe yana sauraronsu tun dayaji maganganun Aisha sai jikinsa yayi sanyi zuciyar shi ta karaya, Har Yaji shakkar furta Yana sonta saboda gudun kada tayi tunanin shima surar jikinta ya ke so.
Bayan wani Lokaci, Alhaji Ubaid Ya tsunduma a harkar siyasa kuma cikin sa'a ya shiga da kafar Dama, Arzi
in shi ya habbaka sosai, Rawar kai a wurin Hajiya layla har ba'a fada, dama ta jima tana cusa mashi ra'ayin ta akan ya shiga siyasa saboda taga yadda Alhaji musa ke fantama da dukiya abunda take ma kwadayi kenan, dama arayuwarta ta tsani taga Alhaji musa yafi Alhaji Ubaid Arzi
i tana jin haushin hakan sosai.
Dr shureim ya so ya kalubalanci siyasar da mahaifinsa ya shiga, Amma Hajiya layla ta take mashi burki ta hana shi magana adole yaja baki yayi shiru.
Alhaji musane yayi mashi hanyar da ya shiga Jam'iyarsu, a Karon farkon da Jam'iyar JDP ta tsayar da shi a matsayin Dan takararsu Na Gomna sunyi murnar da bazata Misaltu ba.
Saboda Farin Cikin hakan yasa Hajiya Layla ta shirya masu gagarumin Party don taya Alhaji Ubaid murnar takarar da aka tsayar da shi da kumayi mashi fatan Alkhairi.
Kafin Shigarshi siyasa saida ya fara tuntubar Shiekh Imam don ya bashi shawara, Sheikh yace shi bazai hana shi yin siyasa ba amma da zai bashi shawara yacigaba da kasuwancinshi sai yafi zama alkhairi a gare shi, saboda yawancin yan siyasa sai sun kauce hanya suke samun mulki, Nasiha sosai yayi mashi har yace ya dauki shawarar shi amma daga baya sheikh imam sai dai yaji labari agurin mutane cewa Alhaji Ubaid Ya tsunduma a harkar siyasa yayi mamaki sosai saboda bai ta6a bashi shawara bai dauka ba sai a wannan karan, abun daya kara
aure mashi kai,
auke kafa da Alhaji Ubaid yai kwata kwata ya daina shigowa donsu gaisa sai in sun hadu a masallaci, daya fahimci kaukaucewar da yakeyi masa sai ya kyale shi don ya gano baya son ya hana shi yin siyasa shiyasa ya janye jiki da shi.
Lokacin da Celebration din Ya matso, Hajiya Layla ta gayyaci yan uwa da abokan arziki don su tayasu Murna, daga cikin wadanda ta gayyata hada Aunty Laura, Benazir kuma ta gayyaci Anila da malama Aisha, koda Aisha ta nemi izni agurin baba Imam yace bai amince taje party ba saboda yahudancine babu shi a addinance, bata ta6a musa masa ba sai akan maganar Party din nan, ta dinga rokonshi akan yabarta taje saboda ta yi ma Benazir alkawarin za ta je, In har ba ta je ba Benazir ba za ta ji dadi ba, Shiekh imam Yace tayi hakuri kawai, don bazai ta6a bari taje ba, wunin ranar kwata kwata babu walwala akan fuskarta, Har Aunty laura ta roka akan ta nema mata alfarma agurinsa aunty laura tace ita bazata sanya masu baki ba, saboda an nuna mata iyakarta don haka suje can su karata ita da uban nata, abunda yasa tace haka saboda taji haushin bukulun da shiekh imam yayi mata akan kudin da Alhaji musa yayi mata alkawarin zai bata intaja hankalin imam da Aisha suka amince da auranshi amma gaba daya suka watsa mata
asa a ido abun ya kona ranta.