← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 201

Sashe 57

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu wanda bai tambayi ina baba ya ke ba a cikin su, da suka rasa amsar da zasu basu a a karshe sai dai suka ce masu baba bayanan jiya bayan an gama celebration din Owais, likitan amininsa ya kira sa a waya ya fada masa baya da lafiya, basu san ma ya tafi ba, abun da ya sa ma basu sanar da shi abun da ke faruwa ba saboda basu san su
aga hankalin shi.

Lokacin da suka tashi tafiya saida suka koma
akunan marasa lafiyansu suka kara duba jikin nasu, still momma bata farka ba, sun so su gana da mahaifiyarsu a
arshe dole suka hakura, su twins ba su bar asibitin ba suna a tare da mommynsu, Sharafuddeen ma bai bi su ba.

Jazz da mom Turai ne kadai suka bi sauran suka dawo estate din su..

CIGABA
____________________________
Zaune su ke saman gadon Aunty Ummi, su biyu suna fuskantarta, yau gaba
aya sun rasa gane kan ta, duk ta bi ta kuntata kanta.

"Aunty Ummina meke damun ki ne? babu walwala atare dake, ko murmushi baki yi.." Batool ce ta fada tana marairaice mata fuska.

"Pls aunty Ummi, Ki fa
a mana damuwarki mana ko baki da lafiya ne..?"
Kallon Unaisah ta yi,
"Kada ku damu, Lafiyana lou, kawai hankalina ba a kwance yake ba, tun dazu gabana ke faduwa, Ina jin ba dadi a cikin zuciyana." ta fa
a fuskarta a yamutse..

"Ki daina sanya damuwa aranki pls, zata iya haifar maki da wani ciwon, kinsan mun damu dake bamu san mu ganki a wani yanayi mara dadi..." Murmushi ta saki har cikin ranta ta ji dadin maganar Unaisah..

"Shiyasa nake bala'en son ku wlh, kuna da hankali, kuma kun damu da duk wanda ke tare da ku, nima ba zan so in sanya ku a damuwa ba don haka na daina, tun da baku so, but pls ku ta ya ni da addu'a."
murmushi suka saki atare suka hada baki gurin furta, "In sha Allah zamu yi maki addu'a, muma muna son ki sosai, Allah ya bar mana ke aunty Umminmu.."
"Ameen." ta fa
a da fara'arta,
"Me yakamata mu yi yanzu?

Yoga or what"?

Ta tambaya don ta ji ra'ayinsu..

"Ai bamu iya ba"
"Zan koya maku yanzu, in muka gama sai mu yi wanka."
Saukowa suka yi daga kan gadon, gaba dayansu riga da wando ne a jikinsu na shan iska, akan tattausan rug din dakin suka fara motsa jikin su, da kanta take koya musu yadda zasu yi yoga din, tuni suka fara ha
a gumi suna sakin nishi..

Wayar Ummi ce ta soma yin ringing, mikewa ta yi daga kwancen da take a
asa ta dube su duk sun baje sun
age kafafunsu sama doguwar sumar kansu ta lullube fuskokin su..

"Ku cigaba da yi, zan amsa kira.." tana fada ta mike ta dauko wayar, mood din fuskarta ne ya canza ganin sunan me kiran ta, nan take ta fara tariyo maganganun da suka tattauna da Chief ta rasa gane meyasa take kokwanto akansa?

Kamar mara gaskiya ta dubi su Unaisah dake ta aikin motsa jiki, ganin hankalinsu baya akanta ne yasa ta lallaba ta shige toilet ta yi picking call din sam ta kasa magana sai mayar da numfashi take yi kamar wadda ta sha gudu.

Husky voice dinsa ce ta ratsa kunnanta, "Ummi ya muka yi da ke? shiru ta yi bata amsa masa ba..

"Nace zan zo kin hana ni, kema kin ce zaki zo amma baki zo ba, ina ta jiran ki, meyasa kika fara canza minne?.." Ya fa
a cike da rashin jin dadi.

Dakyar ta daidaita nutsuwarta kafin ta ce,"Me zan yi maka idan nazo uhm?"
"Abun da kika saba yi min, Ummi a bu
ace nake da ke, tsawon wata baki bani hakkina ba.."
Murmushin gefen fuska ta saki ta so ta bijire masa amma tunawa da maganar Chief ya sa ta kashe masa murya, "I need you too my big boss, fiye da yadda kake bukatana, ba canza ma na yi ba, ba a bani iznin fita bane, kuma ina yin taka tsantsan ne saboda sharadin da ka gindaya mini."
tana iya jiyo sautin ajiyar zuciyarshi alamar ya ji dadin kalamin ta.

"Yanzu da yaushe za ki zo guest house
ina?"
"Zaka iya ha
ura har zuwa weekend?"
"Zan iya amma bisa sharadin idan ki ka zo kwana za ki yi.."
"Ba damuwa big boss, your command is my wish, kasan kai nawa ne ni kadai.."
Shu'umar dariyarsa ya saki, idan na dam
e ki this time, ba zan raga maki ba,.."
Wani iri ta ji aranta kamar kalamansa basu yi mata da
i ba, sai ta ji inama dr Shureim ne yake furta mata su bayan sun yi aure, mafarkin da ta da
e tana yi.
har su ka yi sallama babu walwala akan fuskarta.

Dafe wayar ta yi akan kirjinta ta lumshe idanunta, tana tariyo maganganun chief Owais a cikin kunnanta sun tsaya mata a
ahon zuciya, ta kasa yarda, big boss bazai iya rashin imanin nan ba, ita ba ta yi masa kallon mutumin banza, Saboda komai ya faru game da haramtacciyar mu'amalarsu tare da hadin kanta ne ba dole yayi mata ba, shiyasa bata ganin laifinsa, kawai abu biyu ne ya jefa ta a ru
u, me ya kai diary din Unaizah da hotunansu a ciki
Yarinyar da bata taba barin Uk ba
abu na biyu zanen tattoo din sa dana Danish
bazata ta6a yarda ba in har bashi Uncle Musa dinne ya bayyana mata komai da kansa ba, amma ta fara tunanin zata basu hadin kai saboda dalili biyu!

Na farko don ta wanke Uncle Musa daga zargin da suke yi akan shi!

Dalili na biyu saboda bata so tayi disrespecting din Chief Owais, tana ganin girmansa bazata iya
in bashi hadin kai ba
Fitowa ta yi daga cikin toilet din, turus ta tsaya tana kallon su Unaisah dake sharar bacci, daga motsa jiki suka zarce yin bacci..

Tattausan Murmushi ta yi tare da dan girgiza kanta.

"Babes anji jiki, kun yi tunanin yin yoga abu ne mai sau
i.." ta fa
a tana yin yar dariya..

Batare da saninsu ba ta dauke su hotuna har kala goma, ta koma gefen gadonta tana kallon hotunan nasu, ba karamin burgeta su ka yi ba, duk in ta kallesu sai ta tuna da babynta,
ar kyakkyawar jinjira, jinin arab,
_Wanda ya fi ni sonki ya
auki abunsa, laifina ne dana tafi na barki, watakil kuma hakan shi ya fi zama alkhairi, I luv u little Batool dina.." Idanunta cike tab da kwalla ta fada_
Aminnanta ne suka fa
o mata aranta, nan da nan ta ha
e rai, tana kewarsu tana son su zauna su yi firar yaushe rabo sai dai ba ta jin zata iya yin hakan saboda fushin da take yi da su..

"Sun haifi
a'yansu sun basu kulawa, amma ni basu kula min da
ata ba, har ta mutu.." kifa kanta ta yi saman pillow, tana kuka
asa
asa don kada sautin ya farkar da su Unaisah.

Bayan sallar magrib suka hallara a tv room din gidan kamar
aramar cinema, su hudu ne zaune kan kujeru, sun nutsu suna kallon indian drama a cikin faskekiyar plasma tv din dakin.

Unaisah tana a kusa da daddynta ta langwa6e kanta saman kafadarsa, yayin da Batool take a gefen Ummi hannayensu ruke cikin na juna, cikin nishadi suke kallo.

Wani romantic scene da aka zo, jaruman suna kokarin yin kisss kusan atare Taj da Ummi suka rufe masu idanunsu da tafukan su, aikuwa gaba daya suka tuntsire da dariya, su kansu basu tsammaci zasu ga abun da zaisa su ji kunya ba.

Saida aka wuce gurin, tukunna su ka bu
e masu idanunsu.

Da yar shagwa6a Batool ta ce, "Aunty Ummi, why did you cover my eyes?

"It's not appropriate for you to see" dariya su ka kuma yi..

"Daddyn Unaisah ya batun sauran yaran fa?

Ina ta so inyi maka magana, ko har yanzu baku yanke shawara ba ne?

Wlh sun takura, kullum na yi waya da su sai sun roke ni akan in yi ma Chief magana a dawo da su nan.." Ta fada tana kallon Taj.

Unaisah ta ce, "Wallahi munyi missing dinsu, nima duk idan mu ka yi video call da su har kuka suke yi min, pls daddy, kayi wani abu mana, ko mu mu koma can gurin su ko su dawo nan zai fi masu kwanciyar hankali.."
Taj ya ce, "Nima suna a raina, ko
azu saida na yi ma Chief maganarsu, na ce masa gwara a dawo da su nan din su san cewa mun dawo ga kuma abun da ya faru, in ya so sai mu lallashe su su yi hakuri su rungumi kaddara, sai Chief
in ya ce shima yayi tunanin yin hakan amma da akwai dalilin da ya sa ya za6i su cigaba da zama acan din har zuwa time da zamu kammala kama Elders, yana so ya basu mamaki nima kuma na goyi bayan hakan, ko dan saboda Sajeed ya
wallafa rai akan yar uwarsa, bamu san ko hada ita cikin yaran da muka ku6utar ba, mun bari sai zuwa time da lafiyarsu ta inganta saboda akwai majinyata a cikin su, wasu ma har surgery aka yi masu,"
Tsananin tausayinsu ne ya kama su, nan da nan walwalarsu ta ragu.

"Daddy, when will we go to the hospital to see them?

Batool ce ta tambaya,
Unaisah ta ce, "I even asked the Chief about it, but he said no for now because the hospital is far from the city.."
Bata
are maganar ba Taj ya ce, "Kuyi hakuri zuwa lokacin da za su ji sauki, cikin gari za'a dawo da su, a hada ku gaba
ayanku" murmushi suka yi,
Ummi ta ce, "I can't wait to see wallahi, har walima zamu ha
a don taya su murnar samun yan'ci ..." murmushi suka saki gaba
ayansu..

"Amma daddyn Unaisah, taya za'a iya gano iyayen su da suka sadaukar da su?

Kuma har su nawa ne pls"?
Chapter 57 · 0% Book details