← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 201

Sashe 171

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da izza ya furta.

Da sauri ta dawo mazaunin gaba Ta bude ta shiga ta zauna tana ta faman sauke a jiyar zuciya, ta
anyi mamakin ganin shi ne zai yi driving da kan shi bayan bata saba ganinsa yana driving ba.

Bayan ya tashi motar, ya yi reverse ya fusgeta da matsakaicin gudu motar ta fuce daga gida.
~____
_____
______
______
_______
________
UNAISAH
tana tsaka da sharar baccin ta, Kwatsam hasken
akin Ya
auke
uff, sai na Candles da ke ci,
arar qira'ar alqur'anin daya kara
akin ne Ya farkar da ita a firgice ta farka tana zare sleepy eyes
in ta, wata irin fa
uwar gaba taji sa'ad da ta lura babu hasken fitilun
akin sai na candle lights!

Zuciyarta ta shiga harbawa da sauri da sauri kamar ana mata lugudan ta6are a
irjin ta.

Bata ta6a tsintar kanta a cikin tsoro irin na wannan lokacin ba tun bayan rabuwarta da kurkukun
addara!

Abu biyu ne yazo aranta, watakil Yaya Owais ne Ya kashe hasken
akin sa'ilin da take bacci don ya bata mamaki, ko kuma Electricity din gidan ne Ya samu matsala, gaba daya ta manta menene yayi silar farkawarta daga bacci.

A tsorace ta furta"Yaya Owais?

Kai ne ka shigo?

Kana ina?

Nasan kaine ka kashe min hasken
aki, dan Allah kayi min magana, gaba daya na tsorata.."
Ta fa
a tare da mi
ewa daga kan kujerar, jikinta nata kerma kamar mazari.

La66anta na kerma ta kuma cewa"hubby, pls kada ka wahalar dani, bazan iya jurewa ba, idan kaine ka yi min magana ko hankalina ya kwanta, tun
azu nake jiran zuwanka...

"
bata
arashe maganar ba, Unexpected ta tsinkayi sautin takun tafiya a cikin kunnanta daga bayanta, tuni tasha jinin jikin ta, jin ya
i amsa mata yasa tayi tunanin ba ya ya Owais ba ne, wani ne ya shigo gidan, nan fa ta
ara shiga tashin hankali, tsoro ya hana ta juya ta fuskance shi, sai faman zazzare idanunta ta ke yi, dakyar ta iya
yalla idanun ta ta cikin mirror
in gaban ta ta soma hango shi da taimakon Candle lights...

Walking magestically ya ke nufo cikin bedroom
in kamar baison taka
asa, daga
asa ta soma
are ma shi kallon
urullah da tsantsar ru
ani da fargaba saboda bata tantance wanene ba, tsayin sa ya zarce na Chief Owais.

Sanye ya ke cikin shiga ta larabawa, wata hadaddiyar dishdasha long tunic, launin ivory white ta bayyana tsantsar zazzafar surar sa mai matu
ar jan hankali, daga fadadan kafadunsa wata madaidaiciyar bisht cloak ce (alkyabba ) launin Golden-brown, daga gefenta da bakin ta gaba daya adon duwatsu masu daraja ne lullu6e da rigar, sai kyalli su ke yi suna she
i, wuyan hannunsa na dama yana asanye da Expensive rolex Watch irin wadda sai dan wane da wane su ke sanyata, both mid fingers dinsa suna a sanye da gemstone-encrusted rings, yayin da kafafunsa ke asanye da hand made Leather arabian shoes, mayar da idanunta tayi akan fuskarsa cike da fargaba take kokarin gano wanene sai dai kash rabin fuskar tasa yayi covering dinta da Gold leaf Mask, gaba
aya kansa a na
e ya ke da turban, irin na
in larabawa, daga kasan rawanin doguwar sumar kansa ce ta zubo, wutsiyoyin kitsonsa biyu suka hauro ta saman kafa
arsa har izuwa kan broad chest dinsa, daga bayan sa wata sumarce har mid back dinsa mai kyan gaske tana ta she
i brown shar da ita..

Duk
amshim da bedroom din ta ke yi saida
amshin turarensa ya disashe shi, wani irin sweet fragrance mai rikita shau
in bawa, daga yanayin tafiyarsa ta fahimci yana da izza da qasaita daga gani mutum ne mai tsantsar ilmi da aji kuma wayayye mai cikar kamala da nutsuwa.

Unaisah ta gama ru
ewa, Tsoro da fargaba suka cika Zuciyarta da ke tayi mata dakan sakwara, aranta tana ta tunanin wanene wannan Hamsha
in saurayin? shin tayaya akai ya shigo gidan Auranta?

Kwata kwata bata yarda Mutun ne ba, tafi alakanta shi da jinsin jinn saboda zubin sa!

Anya kuwa Yaya Owais ya sanya malamai suyi safkar alkur'ani a gidan kafin ta tare?

Tana kokwanto saboda gayanan tunkan aje ko'ina ta fara ganin ifritun Aljani..

Yawu ta ha
iya mai zafi makoshin ta ya bada sauti
utt, cikin rawar jiki ta fara tunanin mafita!

Gashi tamanta waya agida balle ta kira wani ta fada masa Aljani Ya kawo mata farmaki, ita kadai baiwar Allah, tunanin guduwa tayi duk da tasan ba lallai takalman kafarta su bata hadin kai ba saboda tsinin su.

Ganin Ya kusa karasowa cikin
akinne Yasa Ta fara neman gurin da zata 6uya cikin rawar jiki ta soma ja da baya cikin san
a don karya ji takun ta.
zukunnawa tayi
asa da rarrafe ta dinga yin tafiya ta nufi karkashin gado ta shige ciki ta 6uya gabanta nata fa
uwa, aranta tana mai cigaba da ambaton La'Ila ha'illa anta subhanaka Inni kuntu minazzalimin"
~________________________________
A hankali ya
arasa shigowa tsakiyar dakin, cikin takun
asaita ya nufi gaban gadon, Unaisah dake a karkashinsa tana le
afafunsa da ke tunkaro gadon, tashin hankali tuni gumi ya wanke fuskarta, runtse idanunta ta yi gam ta dinga karanto Ayatul kursiyo a cikin zuciyarta da sauran addu'o'in neman kariya daga sharrin jin.

A hankali ya zauna daga gefen gadon ya
aura
afarsa
aya kan
aya..

Zuciyarta ce ta tunzurata akan ta duba
afarsa taga idan irin na mutanene ko kofaton jaki irin na aljanu kamar yadda Aunty Danejo ta ta6a bata labarin cewa Idan aljanu suka yi suffar mutane zaka iya gane su ta kafarsu saboda ba irin na mutane bane, Kofaton Jaki gare su.

Cikin san
a ta zu
unno da kanta ta
urawa fatar
afarsa ido, Har saida gabanta ya fa
i ganin kafar tasa fara sol kamar ta jariri yadda kasan bai ta6a taka
asa ba, hasken fatar sa irin pure shining white
in da ba acika samun shi ba ne naturally.
ewa tayi, duk da tana kokwanton kamar mutunne tun da bata hango kofaton jaki ba, zuciyarta ce ta raya mata idanunta ne suke nuna mata ba daidai ba, watakil owais ne girgiza kai tayi in har Owais ne bazai ta6a zama fari ba.

Ganin Ya motsa kamar ya mi
e yasa ta katse zancen zucin nata, kanta harya fara ciwo, ga yunwa da bacci tana ji, ga zullumi da fargaba sun cika zuciyarta..

Shigewa toilet ya yi, tana lekensa taga glashin bangon toilet din ya disashe, aranta ta ayyana ya koma mazauninsa kenan, tunda ance toilet gurin zaman aljanu ne, cikin sauri da rawar jiki ta fito da niyar ta fece, kwatsam ta hango tamfatsetsiyar waya ajiye saman bedside drawer, fasa fita tayi
Yatsun hannunta na kerma ta dauki wayar ta danna number din daddynta ta kira ta kara a kunne cike da fargaba..

Unexpected wayar Taj dake aje kan bedside drawer ta fara ringing, at same time suka farka.

"Wanene Ke kira" ta tambaya tana duban Taj daya dauko wayar yana kallon screen dinta yace"ban sani ba amma bari na
aga maybe wani emergency call ne"
Amsawa tayi da ''to'' Picking yayi ya kara a kunne
ko sallama batayi ba ta fashe da kuka kamar ranta zai fita.

Har Benazir saida taji yo kukanta, hankali atashe suka dubi Juna..

Har suna ha
a baki gurin furta"Unaisah!

Meke damunki?

Meyasa ki kuka um miya faru wayar waye kuma wannan"?

Dakyar ta shanye kukan, Cikin shesshekar murya tace"yaya Owais baizo ba, Inata jiran shi ni kadai agidan tsoro nake ji, kuma yanzu wani ifritun aljani
aton maridi ya shigo dakina, baka ganshi ba daddy, dogo fari fat kamar fatalwa ya saka kayan larabawa, tun dazu nake boye a karkashin gado har saida Ya shiga toilet sannan na samu na fito har na dauki waya, wallahi daddy Mutuwa zanyi in baka zo ka
auke ni ba, kashe ni zai yi, dan Allah daddy ka zo tare da Baba Imam ya kora mana aljanun gidan da ayar Allah, in har ba so ku ke ku rasa ni ba....

"
yar ta
are maganar..
kalin Benazir idan yai dubu to Ya tashi, Taj ne kadai bai
aga hankalinsa ba, kallon juna su ka yi.

Kafin wani ya furta kalma kiran ya katse.

"Bazan iya jira ba, zanje kawai na tafo da ita, tayaya zai barmin
a a irin wannan lokacin tana ta jiran shi, wunin yau ko abinci bata ci ba saboda sunce zasu ci agidan su, gashi harta fara gane ganen aljanu"
Cikin 6acin rai ta
arashe maganar tana
okarin saukowa daga kan gadon Taj yayi saurin ru
o hannunta, cikin fushi kamar zatayi kuka tace"kana fa jin abun da tace!

So ka ke mu rasa ta ne?

Tun kan aje ko'ina har ya fara nuna rashin kulawa akanta!

Ba fa dan na gaji da ita na bashi ita ba"
Murmushin gefen fuska Taj yayi"Ummu Unaisah, Ki kwantar da hankalinki, ru
ewa tayi ne amma ba aljani bane tagani, Mijin ta ne"
Aru
e Benazir tace"ita fa da kanta tace aljani ne!

Unaisah batasan fuskar Owais bane da zata rasa gane shi!? ina Owais yaga hasken fata? idan kai baka dauki maganarta serious ba nina
auka.."
tana
arashe maganar ta fusge hannunta daga nashi ta nufi closet ta dauko veil ta yafa.

"Karki Fita Benazir, ban baki izni ba, ki dawo zanyi maki bayani.."
"Ai fa sai ka yi Tajo, kaima kasan ba sauraron ka zan yi ba...

"
~____________________________________
_A 6angaren Unaisah, batasan ya akai kiran ya katse ba, ta dinga trying baya zuwa, kamar ta yi hauka, batai aune ba, kwatsam ba zato ba tsammani taji motsinsa abayanta, Kamar numfashinta zai
auke tsabar razana, bugun Zuciyarta ya tsananta, gumi Ya cigaba da tsastsafo mata ta saman goshinta da hancin ta, wani irin tsoro ne ya ziyar ce ta, duk tabi tasha jinin jikin ta..._
Kafin tayi wani
waran motsi sanyayyar Muryarsa ta ratsa kunnanta"My Phone....

"
Ya Ilahi Wani irin ru
anine Ya cika zuciyarta jin muryar ifritun Aljanin tayi mata shige da ta wani wanda ta da
e da rasa shi arayuwar ta, muryarsa da ko a mafarki taji ta saita shaideta, ko da tana a cikin maye ne..
Chapter 171 · 0% Book details