← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 201

Sashe 160

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dagaske kike ko wasa kike min" fuskarta babu annuri tace"wallahi dagaske nake maki, dan Allah ki siyamin kalar rigarta komai da komai"
"Batool zan iya yi maki komai a dunyar nan indai baifi karfina ba, amma in banda abunki tayaya zaki ce irin bridal gown din Unaisah ki ke so?

Batool tafi karfin mu, bamu da kudin da zamu iya siya maki ita, har yau ni banma ga rigar ido da ido ba, a hoto Benazir ta nuna min ita, ba'a kaiga kawota gidan ba!

Sai zuwa gobe"
kwata kwata Batool bata fahimtar bayanin ta"ummina ba za ku iya siya min irin ta ba?

Shikenan ni bazan iya mallakar komai da Unaisah ta samu ba?

Idanunta cike tab da kwalla ta karashe maganar, arude ummi ke dubanta cike da fargaban kada abunda take kokwanto ya tabbata akan ta.

"Ki fahimce ni Batool, bamu da halin da zamu iya siya maki ita!tafi karfin arzikin mu, kuma babu yadda za'ai ki sanya kalar rigar Unaisah aranar auranta, zakija mana surutu tun da ba auranki akeyi ba"
"amma ki canza wata rigar mai saukin ku
i in sha Allah zamu siya maki, amma dan Allah kidaina fadin ba zaki iya mallakar komai da Unaisah ta samu ba, kema zaki iya samun fiye da shi amma kinga wannan bridal gown din da kike magana akai ba iyayen ta bane suka siya mata ba, Mijin da zata aurane ya siya mata..." bata kare maganar ba, taga ta zabura ta mike tsaye jikinta ya hau yin kerma cikin muryar fushi mai tattare da bacin rai tace"zanje na fadawa Abbana, nasan zai siya min irin ta.." fucewa tayi daga dakin.

A rude Ummi tamike tabi bayanta gabanta naci gaba da faduwa ta rasa gane meke damun Batool ne? kamar
amar yarinya, Meyasa takeson irin rigar Unaisah?

Maganganunta kamar suna nufin tana hassada da ita, wallah bata fata abun da take hasashe ya zamana gaskiya.

Ko sallama ba tayi ba ta shigo dakin, abun da ba dabi'arta ba, motsinta yasa shureim dagowa ya dubeta, kwata kwata bai lura da moods din fuskarta ba.

Zama tayi gefenshi ko gaishe da shi batayi ba cikin shesshekar kuka tace"Abbana dan Allah, dan sonka da annabi, ka siya min irin rigar Unaisah ta aure!

Wallahi ita nakeso Abba" bai san sa'adda ya furzar da ruwan lemun daya kur6a abakinsa ba, da sauri Ya aje cup din kan table ya dubeta da idon basira.

"Batool me ke damunki?

Ba kiyi min sallama ba, ko gaishe ni bakiyi ba, ba sannu da dawowa kuma ki rasa da wani zance zaki tarbeni sai da wannan"?

Ya fada fuskarsa a yamutse.

Bata kaiga furta kalma ba, Ummu ta shigo dakin, anan ta fayyace masa komai..

"Haba Batool, wallah idan akan farin cikinki ne sai inda karfinmu ya kare, ba abunda ba zamu iyayi maki ba, amma ki gane rigar Unaisah tafi karfin mu, kuma in banda abunki ai babu me sanya irin rigar amarya ita nata dabanne, kuma ba an baku kyautar anko na kawayen amarya ba? kiyi hakuri ki sanya su mana.."
bai kare maganarba, ta fashe masu da kuka kamar ranta zai fita, gaba daya ta daga masu hankali, suka rasa shawo kanta, dr shureim daya rude yayi zaton iskane suka shigeta nan take ya fara yi mata rukiya
Cikin shesshekar murya ta furta"abba da hankalina!

Ni ce batool, babu wani aljani a jikina, Ku dainayi min ru
iya kawai kuyi min abunda nakeso, ban taba tambayarku wani abu kun kasa yi min ba, meyasa ba zaku iya siya min kalar rigarta ba!

Tayaya zan yarda kuna sona?

Maganganunta sun daga hankulansu.

Tsawa dr shureim Ya daka mata ganin taki ta saurare su
"Ya isa haka Batool, na fahimci rashin wayau ke damunki, karki kuskura ki kara wata magana anan idan ba so kike ranki ya 6aci ba!

Haba sai kace yarinyar goye?

Kodan kinga muna lallashin ki shiyasa kike mana abunda kika ga dama?

In banda rigima me zakiyi da rigar amarya?

Ke za'ay ma aure ne?

Ummi ce ta balbaleta da fada ta inda take shiga bata nan take fita ba, Dr shureim sai kokarin dakatar da ita yakeyi saboda baisan 6acin ran batool dinsa.
ewa tayi fuskarta sharkaf da hawaye cikin fushi ta fuce daga dakin, suka biyota da sauri suna ambaton sunanta kafin su karaso tuni ta shige daki ta kulle kanta.

Bubbuga kofar suka dinga yi suna lallashinta akan ta bu
e ma su
ofa, tana ji tayi banza ta kyalesu, gaba daya tsoro sukeji kada ta lahanta kanta.

Da suka gaji da buga kofar, a kan stairs suka zauna ransu duk ajagule.

"Ina ma ace zan iya siya mata rigarnan wlh dana siya mata, saboda banason bacin ran batool, Idan tana kuka har cikin raina nake jin
aci, saboda tana tuna min lokacin da tana jinjira"
hawayen da suka cika idanun shi suka soma kokarin saukowa kan kuncinsa da sauri ummi ta sharesu da yatsunta.

"Pls, kada ka sanya damuwa aranka, ni kaina nayi fatan hakan amma ba zamu iyaba, dole sai mun danne son da muke mata mun koya mata hakuri da babu idan ba haka ba zamuci wahalarta agaba.."
a kansa yayi"ni lamarin ma tsoro ya bani wlh, lokaci daya ta sauya dabi'unta irin na yara amma meyasa takeson dolin doliya sai irin rigar Unaisah"?

Ya tambaya yana duban ummi.

"Kasan wani abu, nifa ba tun yau ba, na lura da wani abu, Batool tana kwaikwayon komai na rayuwar Unaisah, na rasa gane gasa ta ke yi da itane?

Kishi ne ko hassada.."
bata kare maganarba ya katseta"bana tunanin haka, pls mu kyautata mata tazo"
Ummi tace"dole fa sai munsan meke damunta tukunna zamu kamo bakin zaren, Batool fa saboda bedroom din Unaisah yana a upstairs yasa itama ta nace mana akan mu maida mata bedroom dinta up, sannan ta matsa mana akan mu maidata jami'a don tayi graduation tare da su Unaisah, ka lura da kyau yanzu haka zanan kunshin hannunsu iri
aya ne babu banbanci"
Ta fada tana duban shi, abun duniya ya ishe shi.

"Aisha, bansan ya zanyi ba!

Wai menene dalilin dayasa take son komai irin na Unaisah ne?

Ummi tace"nima abun da nakeso na sani kenan, dole akwai abunda take mawa.."
gaba daya sun rasa mafita.

Gashi ta kulla kanta adaki tun safe su ke ta kokarin shawo kanta amma abun yaci tura, ba ci ba sha, har marece ya yi Batool bata fito ba, ko magana batayi gaba daya ta daga hankulansu.

Suna a zaune cikin falo kan sofas sun zagba tagumi, kwatsam sallamar Unaisah ta katse su cikin sauri suka dubi kofar falon, Shigowa tayi sanye da hijab ta ruke lunch box a hannunta.

Tuni kamshinta ya cika hancinan su.

"Unaisah.."
"Na'am Aunty Ummi, Uncle shureim ya ku ke?

Ina fata kun wuni lafiya.."
murmushin ya
e suka sakar mata"lafiyalou Unaisah, Ya shirye shiryen biki"
"Alhamdulillah, munji shiru baku leko ba, Nima gurin yar uwata nazo duk yau banji duriyarta ba"
walwalar fuskar su ce ta dauke duff, damuwar da suke boyewa ta bayyana akan fuskokinsu.

"Ina Batool din?

Ko tana daki"?

Har suna hada baki gurin furta"tana a
a..

Au bata nan ta tafi unguwa.." kallon juna su ka yi.

Da ru
u Unaisah take dubansu jin yadda suka bada amsa daban daban.

"Aunty Ummi, meke faruwa ne?

Ina Batool?

Ko wani abu ya faru da itane"?
wafa Ummi tayi"Unaisah, Batool tana a daki, amma bata jin dadi, bacci takeyi, ki bari zuwa anjima zamu leko gidan tare da ita.."
girgiza kai tayi"i'm sorry Aunty Ummi bazan iya tafiya banganta ba, Inaji araina wani abu na faru badaidai ba, gaba dayanku da damuwa akan fuskokin ku, bayan haka tunda bikina ya matso Batool kullum tana a tare dani, amma yau ko kadan bata leko ni ba, tayaya hankalina zai kwanta?

Dan Allah kubarni naga yar uwata.."
ta fada tana kokarin wucewa ciki da sauri suka sha gabanta kamar mara sa gaskiya duk sunbi sun rude, kwata kwata basu san tasan meke faruwa saboda sunsan son da take ma yar uwata zata iyayi mata komai donta faranta mata rai su kuma basu san hakan ya faru zataja masu abun kunya ne.

"Dan Allah Uncle shureim ku fada min meke faruwa?

Kada ku boyemin abunda ke damun ku..

"
idanunta cike tab da kwalla tayi maganar.

Kallon juna su kayi, Ummi ta dinga girgiza mashi kai donta lura kamar so ya ke ya fada mata.

"Unaisah, dan Allah kiyi hakuri ki koma gida, wallahi bamu son kiji abunda ke faruwa, ba zakiji dadi ba,"
Gyada kai tayi"tunda ba zaku fadamin ba, zanje na fadawa mommyna da daddyna, nasan su zaku iya fada musu..."
juyawa tayi cikin sauri suka tarota.

"Unaisah, abun kunyane, Mun rasa gane kan Batool, ta canza mana, rigima takeyi mana kamar karamar yarinya, saboda kawai tace mu siya mata irin gown din auranki munce mata bamu da halin da zamu siya mata shine ta kama fushi damu, taita kuka, tun safe ta kulle kanta adaki, baci ba sha, munyi munyi da ita akan ta bude mana kofar dakin ta
iya.." dr shureim ne yayi maganar.

Ummi tace"dan Allah karki damu kanki Unaisah, in banda abun Batool ai abun amarya na dabanne babu mai yin irin shigarta.."
Gabanta ne ya fadi, damuwa ta mamaye zuciyarta, dama sai da tayi fargaban hakan cos tun shekaran jiya da aka raba ma su Invitation bags ta lura Batool bata gode ba.

"Dan Allah Unaisah kada ki fadama kowa, daga mu sai ke, yadda mukayi maganar anan mu binneta anan pls, wlh abun kunyane maganar nan ta fita, kema mun fada maki ne saboda ba mu da mafita"
Cikin karyayyar murya tace"Batool bata kyautamin ba, kawai saboda tana son rigar aure na shine ta haramtawa kanta zuwa gurina, Ta kulle kanta adaki? ta tambaya cike da takaici.

"Bana fata Allah ya nuna min ranar da Batool zata nemi wani abu agurina in gaza yi mata shi, tafi karfin komai wallahi, zan iya hakura da komai in bar mata"
waro idanu waje sukayi cike da mamakin maganarta, juyawa tayi da sauri ta nufi up, suka bi bayanta da sauri.
Chapter 160 · 0% Book details