← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 201

Sashe 39

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 5 min read

Tashin hankalin da ba'a saka mashi date, tun kan ya karasa suka fara jefawa junansu kallon kallon mai nuni da tsantsar al'ajabi da rudani hadi da tsantsar tashin hankali, ga wani irin faduwar gaba da suka fara ji, Lokaci daya suka zazzare idanunsu jin abun da basu taba zata ba, murya na rawa Justice ya furta"ba zai ta6a yiwuwa ba Owais, wannan wani irin labarine mai kama da almara?

Bazai ta6a zama gaskiya ba wlh, Owais ka sake bincike watakil kunyi kuskure, Baba bazai ta6a zama daya daga cikin azzaluman mutanan ba, ka bani mamaki Owais ka rasa wa zakai wa kazafi sai baba? sai kace bakasan halin shi ba"?

Cikin fusatacciyar murya ya fada tsabar bacin rai shatun jiyoyon wuyansa sun fito rudu rudu kan fatarsa..

"Tayaya zaku yarda da abunda wata tsohuwa bare ta fada?

Wallahi karya takeyi maku, ba momma bace, wanda ya mutu baya dawowa ba, ni batai min kama da mai hankalin ba, makiya ne suka turota don tayi ma grandpa kazafi, Ai wlh da nasan abunda makirar matar nan ta aikata, da tun lokacin dana ganta kwance kan sofa, zan danne hancinta da fillow har sai ta bakunci lahira...."
Captain yaseer daya gama rikicewa jikinshi na 6ari ya dubi Imam malik daya sadda kanshi
asa "shekh pls kayi masa rukiya, Owais Ya haukace, He needs a psychiatrist to examine his brain, he's not well, Owais would never say this in his right mind, saboda wlh bayin kansa bane, Owais ba zai taba fadin maganar nan da hankalinsa ba, zai iya yiwuwa aljanunne suka shige shi, dad...Uncles pls kuce mana karyane abunda Owais ya fada akan grandpa, ni nasan ba acikin hayyacinsa ya fada ba, Baba ko kiyashi bazai iya kashewa ba, balle rai..."
tashin hankali Ya hana Ziyad furta kalma, kunnuwansa sunjiye mashi abunda ya fi karfin jin shi, baima san sa'adda ya fara unbottoning din rigarsa ba, saboda wani zafi daya taso mashi, still basu gasgata maganar owais ba, amma fa sun ka
u ba kadan ba saboda sunsan mawuyacin abune Owais yayi masu karya saboda ba halinsa bane, kawai suna jin tsoron su gaskata abunda ya fada musu ne..

Gaba daya ubannin nasu sun kasa magana saboda sun razana da ganin yadda suka
aga hankulansu, ta wani bangaren zuciyarsu ta karaya da jin kalaman dake futowa daga bakunansu, bayin Allah saboda yardar da sukayiwa kakansu sun kasa yarda da maganar da aka fada musu akansa..
runtse idanu shi yayi gam a hankali wasu zafafen hawaye suka fara shararowa kan kuncin sa, cikin shesshekar muryarsa mai rauni ya furta"sheikh ni dama nasan za'a rina, baba ya karya mana zuciya, wlh ba kazafi nayi masa ba, shine Elder na gidan kurkukun kaddara kamar yadda kukaji, zaku Iya tuna yaran da nake ruko agurina?

Wanda nace maku sojojin america ne suka tsince su a dajin Evil forest kuma suka dam
a case din mu a hannun hukumarmu?

To wadannan yaran suna daga cikin fursinonin kurkukun kaddara, A Lokacin sun ku6uta daga gidan kurkukun ne, ai kowa daga cikinku ya gansu a ranar farewell dinner din Uncle Hateem.." nan fa kwakwalensu suka fara tariyo masu fuskoki yaran masu bala'en kama da wasu daga cikin su, still basu gasgata maganar shi ba, amma fa sun fara shan jinin jikinsu, maganarsa ta haifar musu da kowanto..

"Bayan mun kai farmaki, Munyi nasarar ceto wasu daga cikin yaran, A yanzu haka suna akwance gadon asibiti karkashin kulawar likitoci, Aminina omar shima an kwantar da shi tare da dan uwan yaran Salsabeel, har yau basu farfado daga Coma ba, Idan har yanzu baku yarda ba zan iya nuna maku videos din yaran da muka kubutar..."
Wayarsa ya zaro daga cikin front pocket din aljihunsa ya kunna masu video din fursinonin ya nuna masu gaba daya suka le
a suna kallon su, gasu nan a kwankwance saman gadajen asibiti jikinsu sanye da patient uniform, har sheikh imam saida ya kalla, ya kuma kunna masu videos din su Unaisah daya dauka yayin tattaunawarsu a questioning room, wlh sun girgiza gaba dayansu ashe basu ji komai ba agurin khala, sai yanzu da suka ji ainihin labarin azabtarwar da akeyi masu agidan kurkukun
addara, abun ya taba zuciyarsu sosai, kamar zasuyi hauka saboda tausayin su daya kama su, su Captain duk sun yarda dagaske ne abunda owais ya fada musu sai dai basu yarda kakansu Obie yana daga cikin azzaluman da suka azabtar da su ba, saima cewa sukayi koda zasu yarda labarin na zahirine amma bazai taba yiwuwa baba ya aikata ba, saboda su sun yarda da shi sun kuma san halin shi, sheikh Imam Ya kasa furta kalma, saboda raunin da zuciyarshi tayi, baiyi zaton abun ya munana har haka ba, sai ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihurraji'un yakeyi Bai ma san sa'adda ya zabura ya mike tsaye jikinsa na 6ari Ya kama zarya a tsakar falon ba, Cazbahar hannunsa tuni ta jima da barin yatsunsa ta fa
a kan floor, har kwalla saida ta zubar masa bai bari sun gani ba yayi saurin sanya tafin hannunsa ya goge ta, hakika Baba Obie ya karya Zuciyar Imam malik, bai taba zaton zai iya aikata makamancin rashin imanin nan ba, abu biyu dayafi kona masa rai ya karairaya zuciyarsa irin yadda suka shafe shekaru suna aikata fasadi a doron
asa batare da an kama su ba, Yaji takaicin irin azabtarwar da sukayiwa yaran da basu ji ba basu gani ba, abun takaici yaran jininsu ne, babu imani ba tausayi suke azabtar da su, labarin da owais ya basu ya fama masa tsohon raunin da ke a cikin zuciyarsa, Bazai ta6a mantawa ba, yaso ya fada musu ainihin dalilin dayasa ya fara zargin ahlinsu sai dai ya kasa ganin halin da suke a ciki, abun dayafi damunsa makomar Ahlin Obie, ya'yansa masu daraja da kima a idon duniya, babu na banza acikinsu, kowa yabonsu yakeyi saboda kyawawan halayensu da dabi'unsu, amma fasikin mutumin nan saida ya zubar masu da mutuncinsu!

Bai kyauta ma kanshi ba, da alama abun ya taba zuciyar imam so yake yayi kuka don ya fitar da abunda ke ransa sai dai ya kasa saboda bai son suga rauninsa hakan zai iya
ara jefasu a mawuyacin hali..
a karo na biyu ya share kwallarsa yayin daya basu baya, saida ya daidaitsa nutsuwarsa ya daure ya cije cike da karfin hali ya juyo ya fuskance su a lokacin sun kasa yin kukan na zuci sukeyi mai radadin gaske...
Chapter 39 · 0% Book details