← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 201

Sashe 9

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya kasa yarda da abun da Zuciyarshi ke raya mashi, ya yi fatan ace mafarki ya ke yi ba gaskiya ba, wani kululun bakin cikine da takaici Ya tokare makoshin shi..

Muryarshi na rawa ya furta"Shegiya agidana?

Gidan Alkali sheikh Imam?

Sanannan malamin addinin islama!

Me yi ma wasu fada da nasiha akan aikata Barna"?

Yau agidana aka aikata barna?

Ni sheikh? yata Aisha ce ta haifi Shegiya acikin gidana?

Batare da Aure ba? inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..."
wani makokon bakin cikine ya mamaye zuciyarshi, hannayenshi na kerma Ya mika ma Laura yarinyar da sauri tasa hannu ta kar6a, jikinshi na kerma ya zauna Gefen gadon Aisha Cikin sanyin murya ta wanda ya karaya ya furta"mamana, tayaya kika samu Ciki?

Wanene yayi maki aika aikar nan"?

Kunya da bakin cikine suka sa Aisha tagaza furta kalma, taki fitowa daga cikin bargon jikinta sai kerma ya ke yi.

Shurun da tayi ne ya bata masa rai, Ya doka mata tsawar data firgitar da su, Har Jaririyar saida ta fashe da kuka
Yana Huci Yace"Ba zaki bani amsar tambayar da nayi maki ba"?

Aunty laura tana kuka tace"Abien Aisha tsautsayine da kaddara..."
Bata kare maganar ba, Ya zabura ya mi
e ya nufe ta gadan gadan, batai aune ba Taji safkar maruka zafafa kan kuncinta, Har saida shatun hannayensa suka fito rudu rudu akan kuncin ta, gefen bakinta ya fashe jini ya fara
iga.

"Allah Ya isa tsakanina dake Laura, Kin cuce ni kin cuci kanki kin kuma Cuci Aisha, sannan kin Cuci malama Batool!

Kin ci amanata, nasan komai ya faru da Aisha kece Sila, kece kika ja komai, shashasha mara hankali"
Fashewa tayi da kuka Jinjirar hannunta sai kuka takeyi.

"Kunyi tunanin bansan komai bane?

Duk abunda ke faru agidan nan an fada min, Kece Kika matsa ma Aisha kuka tafi partyn dana hanata zuwa, kina amfani da biyayyar da takeyi maki gurin Cutar da rayuwarta.."
Cikin shesshekar kuka tace"wallahi Allah shine shaidana, Ni ban ta6a Cutar da Aishaba, na ruke amanar da ka bani, Kai ka sani in ba ni ba wa kake tunanin zata kula maka da yarka kamar yadda na kula maka da ita"?

Bai kula ta ba, Ya koma ga Aisha Ya sanya Hannu Ya yaye bargon data lulluba da shi wata irin zabura tayi ta mike zaune jikinta na kerma ta dinga girgiza kai batare data iya furta kalma ba.

"Ki gaya min wani fasikin ne yayi maki ciki"?

Cikin rawar murya ta zayyana mashi komai daya faru.

"Dan Allah ka yafe min baba, Ba laifina bane, bayin kaina bane, Na rantse maka da wanda raina yake a hannunsa Bada son raina komai ya faru ba, dr shureim shine Ya yi min fya
e, baba kayi hakuri kayi hakuri, nasan nakarya maka zuciya, Naji kunya baba, nayi abun kunya, har rokon Allah nayi ya dauki raina in huta saboda bakin cikin abunda yaya shureim yayi min..."
sambatu tadinyi yi mashi...

Bai san sa'adda hawaye suka cika idanun shi ba.

Cikin raunanniyar Murya yace"Aishana, meyasa lokacin dana hanaki fita partyn bakiji maganata ba?

Meyasa?

Har ni zansa maki doka ki karya saboda Wannan shashashar ta tursasa maki" ya fada yana nuna Aunty laura da yatsa.

"Aishana baki taba yi min gardama ba, ban taba hanaki abu kika
iyi ba sai akan Paryn nan!

Kika bijiremin, Ni dama saida raina ya bani wani abu zai iya faruwa shiyasa Na hanaki zuwa, da ace kinbi maganata da duk hakan bata faru ba, Kinga illar Kin bin Umarnin Iyaye ko"?
jinjina mashi kai ta yi Jikinta nata kerma.

"Aisha, Kinbiyewa Son zuciyarki, Kin cuce ni Kin Cuci kanki, Kin kuma Cuci mutanan da suka yarda da mu, sannan Kin zubarmin da mutucina kema kuma Kin zubar da naki mutunci, kinja mana abun kunyar da shiga cikin mutane zai gagaremu, Kin karya alkawarin da kikayi min na kare mun mutuncina da kimata a idon duniya, masuyi maki kallon mutuniyar kirki da zarar sunsan abun kunyar da kika aikata zasu fara yi maki kallon fasika mai fuska biyu, da Ina alfahari dake amma A yanzu babu wannan Aishana, Kin lalata komai, farin Cikin da kika sama min tun ranar haihuwarki a yau kin bata shi, Kin dasa min bakin cikin da har abada bazan ta6a warkewa daga radadin da naji ba, Aisha Ina da makiya wadanda suke son ganin bayana, Idan har sukaji abun kunyar da kika aikata zasuyi min dariya, kuma zasu yi amfani da hakan gurin ganin raunina..."
fashewa tayi da kuka tana fadin"baba kadaina fadin maganganun nan bana jin dadi baba, Kaifa malamine, kafi ni sani baba, Abunda ya faru dani Kaddara ce, wata irin addu'ar neman tsari ce bakai min ba?

Nima haka inayi ma kaina amma hakan bai hana kaddara ta afkamin ba, saboda Allah ya riga daya kaddara faruwar hakan, babu wanda Allah baya jarabta baba, Annabawan Allah sun fuskanci jarabobin rayuwa basu taba gazawa ba, ya kamata kaima kayi koyi da su, baba wannan ne karo na farko daka fara fuskantar jarabawa mafi muni arayuwarka sau
aya tak yarka tayi ciki batare da aure ba, Dan Allah baba Mu dauki Hakan amatsayin Kaddararmu, muyi hakuri mu jure, baba Kafi jin kunyar duniya akan ta lahira?

Mutane bazasu amfane mu da komai ba saboda basune zasuyi mana hisabi ba"!

Maganganun Aisha sun karya Zuciyarshi, har ya gaza yanke mata hukuncin da yayi niyar yi mata.

Mikewa yayi da sauri Ya fuce daga dakin, Yana fita Aunty laura ta mika mata Jinjirar dake ta kuka"ki bata nono Tasha yunwa take ji" Kar6ar jinjirar Aisha tayi, ta fara shayar da ita idanunta akan fuskar Jinjirar yayin da take tsotsar nono sai kallon fuskar mamanta takeyi, hawayen Aisha dake gangarowa ta cikin idanunta kaitsaye yake sauka saman fuskarta, tayi azan In ta haifi yarinyar zataji tsanar ta saboda bata sameta ta hanyar aure ba, amma sai ta ji tsantsar kaunar yarinyar fiye da komai na duniyar nan.

Aunty laura ta kara lallashin Aisha har saida ta kwantar mata da hankali.

"Aisha nayi danasani da nayita kokarin zubda maki Ciki saboda inajiye maki bakin mutane da kuma abunda zai biyo baya idan mahaifinki Yaji, wlh yanzu da kika tunasar damu sai naji jikina yayi sanyi, da na kashe yarinyar nan da nayi danasani na har abada, baiwar Allah gata kyakkyawa kamanninta sak dana Ubanta, Allah ya raya mana ke bisa tafarkin addinin islam, Allah yasa ki gaji Kyawawan halayan Mamanki"
aisha na murmushi ta amsa mata da ameen.

"Bari naje na shirya maki Abinci nasan kina jin yunwa"
"Aunty Laura, Baki gaji ba?

Naga kin raunata" murmushi tayi kada ki damu Aisha, duk raunin da zan ji bai kai wanda kika ji ba.

Ta fada tare da fucewa ta shiga kitchen da kanta Ta hada mata farfesu bayan ta gama ta kawo mata adaki.

A bangaren Sheikh Imam bayan daya Koma dakinsa safa da marwa ya cigaba dayi, Zuciyarshi cike fal da tunanin ta yadda zai bullowa lamarin saboda bayason asirin abun da ya faru da yarshi aisha ya tonu a idon duniya, yana jiye masu tsoron tozarcin da zasu fuskanta agurin mutane..

A bangaren Dr shureim tun bayan daya Koma Egypt gurin aminsa, Bai kara samun kwanciyar hankali ba, saboda damuwar abunda yayi ma Aisha, Sai da ya shafe sati daya cur bai runtsa ba, abinci sai anyi dakyar ake samu yaci, ya yi duhu ya rame saboda tunanin A wani hali aisha take aciki, ga wani irin azababben sonta daya kara nunkuwa acikin Zuciyar shi, har takaiga baya iya bacci batare da yayi mafarkinta ba, Sometimes sai yayi tunaninta ya ke samun nutsuwa a cikin zuciyar shi, kusan kwana yakeyi akan darduma yana istigfar tare dayi ma Aisha addu'ar Allah yaye mata damuwarta ya kawo mata sauki acikin rayuwarta, saboda yasan zunubin daya aikata mata bazai barta ta zauna lafiya ba, dole su fuskanci kalubale ita da Mahaifinta.
tun yana boye abunda ke damunshi har amminsu ta lura da rashin walwalar shi ta dinga tambayarshi meke damunshi yaki fada mata, ta kasa jurewa ta kira iyayen shi ta sanar da su halin da Dan su ke a ciki, da jin hakan Hajiya layla ta bashi Umarnin ya dawo Nigeria, saboda ammi tace ta rasa gane kanshi, baya bacci baya son cin abinci, wanka ma saita matsa mashi ya ke yi kamar karamin yaro.

Bayan ya dawo Nigeria, Iyayenshi suka tasa shi agaba da tambayar meke damunshi? ya
i ya sanar dasu, Ba irin lallashin da basuyi mashi ba amma duk abanza.

Saida Ya samu nutsuwa ya kira Benazir a dakinsa ta same shi ya tambayeta Ina Aisha?

Tace mashi rabon ta da Aisha kusan wata tara da kwanaki, Aunty Laura tace masu ta tafi sudan gurin kawunta, Ko sun kira layinta basa samu kuma koda zata tafi ba ta yi masu sallama ba"
Hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, Zuciyarshi ta karaya sosai.

Ana haka saiga kiran Sheikh Imam Ya shigo wayar shi, wata irin kunyace ta kama shi kamar bazai daga kiran ba sai kuma Ya daga, Ko sallamar shi sheikh Imam bai amsa ba Yace shureim Inason ganinka, Ka same ni agidana, Ya amsa mashi da toh.

Bai bata Lokaci ba, Ya shirya kanshi cikin shadda Ya nufi gidan Sheikh Imam A garden Ya taras da shi zaune kan kujera fuskarshi babu walwala kamar bai taba dariya ba, tuni Shureim Yasha Jinin jikin shi.

Bayan daya zauna kan kujerar dake fuskantar sheikh Imam Malik Ya yi shiru Yana sauraron shi..

Kallo
aya sheikh Imam yayi mashi Ya lura da irin ramar da yayi daga gani yana acikin damuwa.

"Akwai wata rana, dana farka tsakar dare, na fito daga daki Ina zagaye Gidana, dama Ina yawan yin hakan sometimes bana iya bacci batare dana tofe ko'ina da addu'a ba, ina gab da zan gifta dakin aisha Najiyo shesshekar kukan ta, Kasan me naji tana fadi"? ya tambaya da tsantsar bacin rai Yana kallon fuskar Shureim daya gama rudewa, Girgiza kai yayi"aa baba'
"Addu'a takeyi Allah ya cika mata burinta na ganin ta auri yaron makwabtana data mutu akan kaunarsa batare da sanin shi ba.."
wata irin karaya Zuciyar dr shureim tayi.
Chapter 9 · 0% Book details