Sashe 177
The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jinjina mashi kai tayi, cikin shesshekar kuka tace"tayaya baza tayi kuka ba?
Ko a tarihi bata ta6a jin soyayyar uba da
a irin wadda uban shi keyi mashi ba, tunkafin ma yasan shi din dan shi ne"!
lokacin da tayi wannan maganar, ru
ewa yayi, muryarsa na rawa yace ta fada masa wanene daddy minister?
Tasan shi ne?
Ko shi ne daddynsa"!
Cike da zakuwa yayi tambayar kamar zai hadiyi zuciya saboda zumudin ta fada masa, cikin karyayyar murya tace" shine mahaifinka, Prime minister Hateem, jaririn da kaji yana ba da labari bakowa bane face kai, kaine Omair dinsa, ita kuma matar nan data cire maka mask a ranar dinner din da ku ka je, Itace mahaifiyarka, sheikha Mujeedat, aranar da ta haifeka aranar ne munafukai suka hada baki gurin raba ka da ita"
bata kare labarta mashi ba, sakamakon kukan daya fashe da shi, har saida ta razana da ganin yadda yake kuka a lokaci daya kuma yake dariya, ta rasa gane kukan bakin cikine kona farin cikin sanin su wanene iyayensa?
Lamarin Ya daure mata kai tamau, saboda bata ta6a ganin Danish yayi irin wannan kukan ba da dai idanun ta
A ru
e ta shiga tambayar shi meya faru da shi?
Meke damun shi?
Meyasa ya ke kuka?
Na bakin ciki ne kona farin ciki"?
A lokacin kasa bu
e baki yayi ya bata amsa, tsabar yadda yake kukan jikinshi har jijjiga yakeyi, shatun jiyoyin wuyansa dana goshinsa sun fito ru
u ru
u kan fatarsa.
kifa kansa yayi saman ciyayi, hankalin khala atashe Ta dago da shi tare da rungumeshi a kirjin ta, ta
aura tafukan hannayenta akan bayanshi, Cikin sigar lallashi ta dinga bubbuga bayanshi tace bata san ya zatayi ba don ta kwantar masa da hankalinsa, tasan idan tace yayi hakuri kamar ta cuce shi ne, amma yayi hakuri tasan an cutar da rayuwarshi, an tauye mashi hakkin shi na rayuwa, an kuma raba shi da iyayen shi, wanda tayi imanin da ace a hannun iyayensa ya taso ko chief Owais bazai kai shi samun gatanci ba, saboda arzikin iyayensa bazai misaltu ba, mahaifinsa prime ministern canada ne, mahaifiyarsa kuma diyar Ruler din dubai ce, amma har yanzu bai makaro ba, taji dadi da Allah ya raya shi, in sha Allah zai hadu da iyayen shi, tana da tabbacin a cikin shekara daya zasu sauya mashi rayuwar shi in har ya koma gurinsu, zai manta da duk wani bakin ciki da azabtarwar da ya fuskanta agidan kurkukun
addara, zai zamanto daya daga cikin matasan da suka fi samun gata agurin iyayen su.."
maganganu masu dadi khala ta dinga fada masa har saida ta samu ya lafa da yin kukan, sai dai Jikin shi yayi zafi rau, da alama zazzabine ya lullube shi, lokacin daya dago da fuskar shi, ta 6aci da hawayensa, idanunsa sun kada jawur, tayi tsammanin zai tambayeta wanene ya sadaukar da shi, sai baiyi hakan ba, muryarshi tayi rauni ta disashe dakyar ta iya gane me ya ke son fada mata..
Cewa yayi yau ce rana ta farko da yayi farin cikin da bai ta6a yin makamancinsa ba arayuwar sa, a halin yanzu baida burin daya wuce yaga iyayensa ido da ido, yana matukar son yagansu koda da numfashin shi na
arshe ne..."
tsananin tausayinshi ne ya kamata aranar kwana sukayi a zaune yanata yi mata sambatu akan yadda yake zumudin yagan su har tambayarta yayi zasu ji dadi idan suka san shi dan su ne tace mashi fiye da yadda yaji dadin jin cewa sune iyayen shi..."
A washe garin ranar da sukayi firar, bayan ya sama masu abun da zasu ci, suka kama hanya, dayaga bata sauri yace ta hau ya goyata tace aa bata so ya wahala, tun da ta danji sauki zata iya tafiya da kafafunta, ko ta dafa shi tun da babu sanda atare da ita.
Batasan yadda ya matsu su koma gari ba, batai aune ba taji ya sungumeta akan kafadarsa ya 6ace da su..
Cikin sa'a suka fa
o wani forest din, A gaban wata bishiya ya sauke khala agajiye suka baje kasa nan bacci yayi awon gaba da su.
Har mafarkin prime minister ya yi acikin baccin sa.
Suna tsaka da yin baccin kwatsam
arar Mota ta cika kunnuwansu, a firgice suka farka har sun zabura zasu mike saboda sunyi azan wani mugun abunne amma da sukaga ba abun da suka zata bane sai hankalinsu Ya
an kwanta.
Wata katuwar motar daukar kayace kirar toyota mai budadden baya, ta kunno kai cikin dajin, dattijai ne guda biyu daga gani wani mahimmin aikine ya kawo su cikin dajin..
Kwata kwata basu lura da su ba, har saida sukayi parking din motar, fitowa su ka yi daga ciki.
aya daga cikin su yana aru
e da bindiga irin ta mafarauta, yayin dayan qugunsa ke a soke da Sheath Knife, daga gani mafarauta ne ko wani abun suka zo nema a cikin dajin, suna
arin wuce wa cikin dajin idanunsa sukayi masu tozali da su, kura masu idanu sukayi kamar sunga wani mugun abu, kamar yadda suke kallonsu haka suma suke kallon su, khala ce ta yi karfin halin yi masu magana tace su taimaka su fitar da su daga dajin, kallon juna sukayi jin tayi magana da yaren da basa jin shi, da ta fahimci basu jin hausa sai ta maimaita maganar cikin harshen turanci.
An ci sa'a suna jin yaren daya daga cikin dattijan yace tayaya zasu taimake su bayan basu san su wanene su ba?
Don shi kwata kwata basuyi mashi kama da mutane ba, musamman matashin dake a bayanta" ya fada yana nuna Danish da yatsan shi, dayan dattijon yace"su fada masu gaskiya mutanene su ko aljanu?
Me kuma su ke yi a cikin daji"?
Ta lura Danish su ke ji ma tsoro duba da yadda su ke kallon shi ga dukkan alamu kyan shine basu taba cin karo da mai irin shi ba, ga zanan tattoo dinsa dayasa suke zargin dan wata
ungiya ne ta
an ta'adda.
Khala tace ba abunda suke tunani bane, suma mutane ne kamar su, matashin da suke gani atare da ita jikanta ne kaddara ce ta ritsa da su suka tsinci kansu a dajin su taimaka su shigar da su cikin gari.."
Karya ta shirga masu ta dinga rokonsu dakyar ta samu suka aminta da su, su ka ce su shiga motar, su jira su su gama abun daya kawo a cikin dajin, bayan sun bu
e masu motar suka shiga daga ciki, hankalinsu ba karamin kwanciya yayi ba ganin sun samu taimako, nutsawa dattijan su ka yi cikin dajin tsawon rabin awa, kafin suka dawo hannayensu ru
e da damun ganyayyakin da suka tsinko, abayan motar suka tura ganyayyakin, kafin suka bude motar, suna shiga mazaunin gaba suka yi arba da abun daya daure masu kai, mutanan da suka bari a motar sai bacci su ke yi ga zufa da ta wanke fuskokin su daga yanayin yadda suke fitar da numfashi yasa suka fahimci basu da
oshin lafiya.
Jan motar su ka yi tare da bata wuta suka kutsa cikin gari sun danyi tafiya mai nisa kafin suka
araso cikin birnin abomey-calavi da ke a
asar Benin.
Koda suka shigo cikin gari, sai suka faka motar suka soma kokarin tada su daga bacci don su fa
a masu sun karaso cikin gari su sauko su tafi..
Sai dai me?
Babu alamun zasu farka, har bubbuga kafadarsu su ka yi amma shiru, hakan ba karamin daga hankalinsu yayi ba, abunda suke ma fargaba kada ace sun mutu a cikin motar su, daga taimako?
Har sun yanke shawarar kaisu wani guri su jefar da gawarwakin su, kwatsam tarin tsohuwa Khala ya katse masu hanzarinsu, da sauri suka shiga tambayarta meke damun su ne?ba su da lafiya ne?
Cikin disasshiyar murya tace su taimaka su tafi da su gidan su, idan suka sauke su basu san ina zasu dosa ba, saboda su ba yan nan bane, taji suna wani yare da ba irin na su ba, koda suka tambayeta wani gari take a benin?
Tace masu ita ba yar benin bace, Yar nigeria ce,.."
waro idanu waje sukayi, alamar mamaki.
Basu kara tambayarta ba ganin halin da take a ciki, saboda basu yarda da su ba, shiyasa suka ki kaisu gidan da iyalinsu suke, don karsu cutar da su, sai su ka garzaya da su gidan gonar su, su ka basu
aki
aya mai toilet a cikin sa, Ko gado babu sai katifa.
Allah yaso sun fada hannun nagarin, Har abinci suka basu, duk da yunwar da su ke ji sun kasa cin abincin saboda ba irin cimarsu bace, sai dai suka sha kayan marmarin da suka tsinko masu na lambun su.
Bayan sun yi wanka, suka kwanta kan katifar dakin anan bacci yai awon gaba da su..
Dattijan suna le
an duk wani motsinsu a dakin, saboda suna kokwanto akan su.
Saida suka ga bacci yayi awon gaba da su, suka lallaba tare da shigewa cikin dakin suka soma laluba aljihun wandon danish don suji in akwai kudi su sace su, Yana jinsu yayi shiru kamar yana bacci, jira yake su wuce gona da iri su ci uban su.
Da suka ga babu kudi cike da takaici suka bar
akin, tafiya su ka yi sai dare suka dawo a lokacin suna zaune kan katifar suka shigo masu bayan sun gaida khala tayi masu godiya, su kace su yanzu so suke su san komai game da su, tace suyi hakuri zata sanar da zasu amma kafin nan tana so su fara bata waya zata kira gida..
Dakyar ta samu suka ara mata waya, bayan sunyi deal zata biya su kudin katin da zata ci ma su saboda sunga international call ne tace karsu damu zata biya su konawa su ke so.