← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 198 OF 201

Sashe 198

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk in ya rigata tashi daga bacci da karatun alqur'ani ya ke farkar da ita, sometimes da kissing yake tashin ta har saita farka, saboda dadin da takeji Yasa itama ta dinga tashin shi ta yadda shima ya ke tashin ta cikin salon soyayya..
rayuwar farin ciki da jin da
i su ke yi, sun sangarta junan su, gatanta kansu su ke yi kamar ran su, One week sun kulle kansu a cikin kurkukun masoya ba shige ba fuce, abun da ba zata ta6a mantawa da shi ba arayuwar arayuwarsu shine daren daya kar6i budurcin ta, da kuma kyautar bazatan da yayi mata a washe garin ranar, saboda yaji dadin faranta masa rai da ta yi ne yasa ya bata kyautar Black card with A brand new Mercedes-Benz S-Class and A brand new BMW X5, ita kadai, Aranar kukan farin ciki ta dinga yi masa, sai da takai ga shi ya koma yana lallashin ta.

Tun ranar da Taj Ya hana Benazir zuwa gidan Unaisah lokacin da ta kira su a daren auren ta, Ya fayyace mata komai game da wanda Unaisah ta aura, tsantsar al'ajabi ya kamata, tayi murna Har kukan farin ciki sai da tayi saboda murnar Unaisah ta auri za6inta, mutumin da take ta hauka akanshi ya rayu, da tana ta jin fargaban Kada Owais Yaga zanan tattoo dinta amma da taji cewar mamallakin sunan ne ta aura sai taji hankalinta ya kwanta bata da sauran damuwa.

A bangaren Batool, Sai da ya rage saura Kwana biyu dinner din auran su, aranar abi dinta da mommynta suka kirata a falo suka zauna tare da fayyace mata game da bayyanar dan uwansu Danish da kuma auran shi da Unaisah harma da Auranta da aka daura tare da Owais, Tsabar rudani da al'ajabine yasa ta kasa furta kalma, ta razana da jin Danish yana araye tsawon lokacin nan yana tare da Iyayen sa, kuma ta ru
e da jin cewa Yaya Owais mijinta ne, farin ciki biyu a lokaci
aya, jin abun tayi kamar a mafarki wai ta zama matar dg Owais, nan Ta ke ta fashe da kukan farin ciki, ta dur
ushe kan floor ta yi sujudusshukur.

Sam bakinta kasa rufuwa yayi saboda zunzurutun farin cikin daya cika zuciyarta, kamar wadda akayima albishir da gidan Aljanna, Ummi da Shureim sun ji dadi da ganin yadda ta nuna farin cikin ta, dama burinsu ne su faranta mata rai, sai da takaiga su ne suka dinga lallashinta don tayi shiru ta daina kukan, Ummi ta soma zolayarta da cewa yanzu sai hankali ya kwanta, tun da ta auri muradin ranta, qiyamul laili tayi aiki, yanzu sai ta daina kishi da yar uwarta, tun da bata aurar mata miji ba kowa da nasa.
ko da jin wannan maganar ta Umminta tana kuka ta zarce da dariya, suma suka kama yin dariya, sham ta shafa'a ta daka tsallan farin ciki, da taga sun saki baki sototo suna kallon ta da murmushi akan fuskokinsu saita watsa da gudu ta nufi bedroom dinta, tana shiga ta fa
a kan gado cike da farin ciki take tariyo abin daya faru a tsakanin da chief, dama saida tayi mamakin nemanta da tayi saboda tasan shi din mutunne mai tsoran Allah ba zai iya aikata abin da zai sa6ama mahaliccinsa ba, yanzu tagane jarabata yayi saboda yasan matarsa ce ita, cikin sanyin murya ta furta Am sorry My husband duk da ko a lokacin banyi maka mummunan zato ba, bansan kana sona ba Ya Owais, meyasa ka boye mi ni, ka barni da ciwon sonka! ka hanani bacci ka hana zuciyana sukuni, amma tun da ka aure ni bani da sauran damuwa, naji dadi da Allah ya amsa addu'ar dana da
e inayi akan ka, In sha Allah zan zama mata tagari a gare ka, zan yi maka biyayya sau da
afa...

"
ita ka
ai ta dinga sambatu cikin nisha
i da annushuwa.

A yammacin ranar da ana saura kwana
aya ayi dinner..

Batool tana saman darduma ta kudundune kanta a cikin hijab
inta, daga sallame sallar La'asar bacci mai
an karan da
i yayi awon gaba da ita,tun dazu take ta sharar bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, sautin ringing din wayartane yayi silar farkawarta ba dan tagaji da baccin ba, mikewa tayi zaune tana mi
a da hamma cike da kasala ta tashi Tsaye ta dauko wayar idanunta biji biji take kallon screen
in ko da ganin sunan Heartbeat nan take ta wartsake, jikinta na 6ari tayi picking call din ta kara a kunne kamar tana agabasan, ta nutsu ta zauna daga gefen gadon ta..

"Assalamu alaikum, yaya Owais barka da marece, ya kake?

Ina wuni?

Ya Aunty Nazli"
On the Other hand taji ya furta"wa'alaikissalam my baby girl,Alhamdulillah, muna lafiya, ina fata kema haka"
"Eh," ta bashi amsa a takaice..

"Inason ganin ki, zanzo after magrib..

" zare idanu tayi cike da zumudi tace"toh, shikenan sai kazo" bayan ya katse kiran, ta mi
e tana rawar murna ta tube hijab din jikinta ta jefar kan gado,jallabiyane a jikinta da sauri ta shige toilet, mintuna
alilan ta fito ta nufi dressing mirror, ta shafe jikinta da lotion din ta, saida ta gama shafe shafenta sannan ta dauko Atampa riga da skirt ta saka a jikinta tana gama sawa ana Kiran sallah magrib, hijab dinta ta mayar tare da kabbara sallah bayan ta gama taci gaba da shiryawa,tana cikin daura kallabi ya kira yace gayanan a waje ya iso da sauri ta qarasa daure kanta da dankwalin, gyalen ma a kafada ta yarfa shi, bayan ta saka high heels a kafarta, ta koma gaban mirror ta shafe jikinta da humra mai
amshin gaske..

Cike da rawar jiki ta fito daga dakin, ganin babu kowa a falon yasa ta nufi bedroom din abie dinta don ta fada masu game da zuwan yaya Owais, har takusa isa ta dakata tunawa da basu nan, abi dinta tun da ya fita office bai dawo ba, Ummi kuma ta tafi gidan Aneelerh, kuma shi zai biya su dawo tare..

Tunawa da cewa mijintane Yazo ba wani ba, yasa ta yanke shawarar fita tasan ko su ba zasu hana ta je gurinsa ba, duk da hakan saida ta turama ummi sako ta waya..

DG OWAIS
Yana a zaune a driver seat na motarsa, ya jinginga kansa jikin headrest, sanye yake da riga da wando na voile launin dayafi so, Blue sky, ya lumshe idanunsa sam baiga tafowarta ba, sai dai yaji motsin bu
e Cardoor
in..

A hankali ya bu
e idanunsa akanta, yayin da take shigowa ciki, zama tayi saman seat tare da sunnar da kanta kasa cike da jin kunyarshi batare data furta kalma ba..

Tayi mashi kyau a cikin atampa ya danyi mamakin yadda ta amsa kiranshi cikin sauri batare da jin shakkar zai iya maimaita abun da yayi mata rannan..

Jin yayi shiru bai motsa ba, yasa ta dago da idanunta da niyar ta dube shi, kaitsaye suka shiga cikin nata, har saida taji gabanta ya fa
i saboda kyawun da yayi mata..

"Kin san meyesa na kira ki"?

Girgiza kai tayi"a'a"
"Okay, Unguwa nakeso ki rakani, zakije"? da sauri ta jinjina ma shi kai..

Da mamaki ya danyi shiru yana tunanin meyasa ta sake da shi?

Kwata kwata bai kawo ma ransa tasan komai game da kasantuwarsa mijinta..
key yayi ma Motar, yayi reverse ya fuce daga gidan, yana driving tana satar kallon shi, komai nashi burgeta ya ke yi, kyawawan idanunsa, dogon hancinsa, karamin bakinsa, uwa uba yalwatacciyar sumar kan shi maikyau da santsi kamar ta jinjiri..

Sarai yana lura da irin kallon da ta ke yi mashi, ya yi kamar baisani ba, don ya bata damar da zata
arewa mijin nata kallo..

Wani katafaren Bridal boutique su ka je, bayan yayi parking din Motar, suka fito tana ta kallon katafaren store din, duk da batasa dalilin zuwansu ba, amma tanaji aranta siyayyar kayan amarya zaiyi, daga sunan Store din ta fahimci kayan amare suke siyarwa..

Tana tsaka da kalle kalle, batai aune ba, taji ya ru
e hannunta a cikin nashi, wani shock taji, a rude ta saka idanunta cikin nashi har ya sanya mask akan fuskarsa saboda bayason a shaida shi yanzu mutane sun fara taruwa domin kallon shi..

Bayan sun shiga cikin Shop din, Bridal Consultants din dake agurin suka tarbe su tare da yi masu barka da zuwa, Dg ya fa
a masu Bridal gown ya ke son gani, daya daga cikin ma'aikatan ce ta kaisu sashen bridal gowns, kala kala masu kyau da tsada gasunan birjik jikin hangers, yana lura da yadda Batool ta ru
e cike da mamaki take kallon rigunan tana
an zazzare brown eyes
in ta..

"Ki za6i wadda kikeso" ta ji ya furta, aru
e ta nuna kanta da yatsa"Ni"?

Jinjina mata kai yayi batasan sa'adda ta saki murmushin farin ciki ba,
"Ki taimaka mata ta za6i wadda zatayi mata daidai" ya fada yana duban ma'aikaciyar wadda keta kallonsu tana ji aranta kamar tasan muryar hamshakin mutumin..
o hannun Batool tayi a cikin nata, takai ta gaban wasu tsadaddun Bridal gown Limited edition, tana tsaka da kallon su Unexpected ta hango irin Bridal gown din Unaisah banbancinsu ka
anne Hannunta na kerma ta soma shafa rigar.

Ganin kamar tayi matane yasa matar tace"kina sonta"?

Jinjina kai tayi"Eh"
"Kin iya za6en riga, tana da kyau da tsada, kuma zata dace da ke.." ta fa
a da fara'a akan fuskarta ta curo rigar daga jikin hanger"muje na taimaka maki ki gwada rigar a jikin ki" ta fa
a tana nuna mata ke6ataccen gurin dake a kewaye da dogayen labulaye
Amsawa tayi da toh, ta dan juya tana neman yaya Owais, can ta hango shi a zaune kan Arm Chair, ya kara waya a kunnansa..
Chapter 198 · 0% Book details