← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 175 OF 201

Sashe 175

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 7 min read

A Lokacin da Danish Ya dam
i jeremiah ya ingiza su cikin rijiyar, Tun kan su dira kasan rijiyar a saman iska, suka fara gabza fa
a a tsakanin su baka iya jin sautin komai saina buge buge da naushe naushe da nishinsu hadi da gurnanin su kamar zakuna, bugun mutuwa sukewa junan su, babu imani babu tausayi, kowa jininsa akan akaifa ya ke, zuciyar su a wuya take, musamman jeremiah daya kasance mugun mutun, Ya tsani Danish tuntuni, ba dan komai ba sai don saboda lokacin da suke
anana yafi Danish yiwa elders biyayya idan suka bashi Umarnin ya aikata rashin imani jiki na bari zaiyi, danish kuwa kafiya da taurin kai ya ke yi masu, gashi Allah ya jarabce su da son shi, sai da takaiga sai sun ha
a da yi mashi sihiri suke samun abunda suke so, saboda yadda suke gatanta shi yasa Jeremiah ya ke yi mashi hassada, ya kullaci abun aran shi, yasha kulla makirci don ya sanya tsanar danish a zuciyar elders sai dai bai ta6a nasara ba, shiyasa a yanzu dayaga sun fada rijiya su biyu ya ke ta kokarin kawar da shi don ya fanshe bakin cikin daya kunsa mashi.
wani jahilin naushi ya kaiwa Danish a tsakar mararsa, har saida Ya firgice saboda azabar daya ji, bai kaiga dawowa dai dai ba, jeremiah ya tallabe kansa da faffa
an tafukayensa Ya buga jikin bangon rijiyar, tuni kuzarin jikin shi Ya ragu dama ya fara galabaita sosai saboda yakushin da Evil giants sukayi mashi a filin daga, duk da haka bai sare ba, jini na fita ta bakinsa da hancinsa, da bayan kansa, a haka Ya dam
i kan jeremiah Ya daddage da dukkan karfinsa ya maka shi jikin bango, amma kamar ya hada dutse da dutse kwata kwata babu alamun jeremiah Yaji jiki kamar ana kara masa karfinsa abunka ga sabon garkuwa, don bala'e kusan sau uku suna rikida su canza halittar su, kamar zasu kashe junansu babu tausayi ko kadan burin kowan nan su yayi nasara, kafin kace me tuni Wata irin kura mai hade da hayaki tamkar guguwa ta bude su baka iya ganin su kwata kwata, cakumar Danish yayi ya nutsa da su cikin rijiyar burinshi ya kaishi
asanta don ya azabtar da shi kafin Ya karasa kashe shi, shi kuma baya son yakai kasan rijiyar saboda yana jin tsoron Evils din cikinta su fusata zasu iya tarar mashi yasan cikin dakika zasu iya shafe babin shi.

Duk yadda yaso ya turje saida Ya kasa saboda raunin da yayi, ta karfi ta tsiya Jeremiah Ya ingizasu suka kundumo kasan rijiyar gaba dayansu saida kawunansu suka daku.

Duk da mawuyacin halin da yake a ciki hakan bai hana zuciyar shi tunanin Angel dinsa ba, har lokacin idanunsa basu daina tariyo masa irin haukan da tayi na za'a rabata da shi ba, kalamanta sun tsaya mashi a kahon zuciya, Shagalar da yayi da tunaninta yaja har Jeremiah Ya yi nasarar azabtar da shi, saboda rashin imani da sihiri yayi amfani gurin zane shi da bulalai yayi mashi jina jina, har saida Ya suma kusan sau uku jeremiah Yana farfado da shi.

A lokacin Gaba
aya ya fidda rai da rayuwa, kamar jaki haka Jeremiah ya mayar da shi jini da majina ya hada mashi akan fuskar shi, saida Ya raba shi da kakin jikin shi, Yayi mashi zir haihuwar uwarsa dayaga Ya kusa kashe shi gaba daya baya iya ta6uka komai sai ya fara kokarin yin homo da shi saboda ta hakane kadai zai iya
wace sihirin jikin shi ya dawo nashi jikin saboda ya
ara
arfi na fitar shari'a, bai kaiga cimma manufar shi ba, kwatsam rijiyar ta fara jijjiga, Lokaci daya sautin dariyar Evils mai matukar tsoratarwa da razanarwa Ya cika rijiyar, alamar Evils sun fusata, A lokacin Danish baisan inda kanshi ya ke ba yana akwance cikin jini rai hannun Allah, soft skin dinshi duk ta 6aci da munanan raunuka ko yatsansa bai iya motsawa..

Jeremiah Yana akansa Yana kokarin cimma manufarsa, Kwatsam ba zato ba tsammani evils suka fara
ewayesu da suffar halittun da suka sauya masu tsotarwa, kamar kyankyasai saboda yawansu, manyansu da kananan su, koda Jeremiah yaga haka sai ya fara sakin shu'umar dariya yayi zaton zasu goya masa bayane akan abunda yake kokarin yi saboda yanzu shine garkuwar kurkuku.
bai yi aune ba, kwatsam Yaga bakin hayaki ya soma kurdadowa yana fita ta bakinsa da hancin shi, kaitsaye hayakin ya ke shiga ta kofofin hancin Danish da bakinsa da duk wata kofa da iska zata iya ratsa jikin shi.
lokaci daya yabi ya ru
e ya zazzare jajayen idanunsa kamar na kwartan mazuru, jikinshi ya kama 6ari kamar mazari, yayin da tsoro da fargaba hadi da tsantsar rudanin al'ajabi
suka mamaye zuciyarshi, abin da bai ta6a zata ba, ya rasa gane tayaya akai evils suka bar jikinshi tare da sihirinshi suka koma jikin Danish, da alama reshe ne ya juye da mujiya.
cikin rawar murya ya furta bazai yiwu ba, meyasa zakuyi min haka?

Ni ne sabon garkuwarku, Danish maci amanane, baya atare da mu!

Ku dawo min da sihirina, Ku dawo jikina, ni ne nafi cancanta in samu karfin sihirinsa ba shi ba, ko kun makance ne?

Baku da hankali ne"?

Kamar mahaukaci ya dinga sambatu tare da mikewa ya bi halittun dake kewaye da shi Ya dinga yi masu tsawa yana zaginsu kamar zai doke su.
sai masifa ya ke zazzaga masu ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, wata irin kururuwa ya fasa kamar zaiyi hauka ya tallabe kansa da tafukansa, Ya dinga sakin kara mai tattare da bakin ciki, Har tsalle yakeyi kamar kwa
o dama ba sutura a jikin shi.

Girgizawar da rijiyar tayi ne yasa shi dawowa hayyacin shi, tunkan ya juya idanunsa suka safka akan Inuwar Evil din dake abayan shi, yawu ya ha
iya mai daci, gabanshi ya shiga fa
uwa.
juyawar da zaiyi keda wuya idanunsa suka sauka akan Danish Dake atsaye kan kafafunsa, gaba daya idanunsa sun juye sun koma fari fat babu launin su, wani abun
aure kai ko
warzane babu akan fatarsa gaba daya raunukan da yaji sun 6ace 6att ko tabo babu in ka cire tattoo dinsa, bakin cikine Ya turnuke zuciyar Jeremiah, kamar ya hadiyi zuciya ya mutu.

Cikin fushi yace"burinka Ya cika Danish, Ka yi nasarar rabani da sihiri na, ba zaka ta6a bari in fi ka ba, ko da na sakanni ne ko da yaushe kaine agaba, na tsane ka danish, bana son ganinka, mutuwarka nake kwa
ayin in gani, bazan kyale ka ba, sai na kwace sihirina sannan In kashe ka.
tun daya fara maganar Danish bai motsa ba, saboda a ba
ini ba shi bane, Evils ne suka tada shi shiyasa harya iya mikewa tsaye, tsautsayi ne Yaja jeremiah Ya durfafesa da gudu Ya daka tsalle Ya dura akanshi kafin yayi wani yunkuri Danish Ya dam
i wuyan shi duk girman jikinshi Ya daga shi sama, nan take ido Ya raina fata, Ya dinga gurnani yana kokarin kwace kansa sai dai Ya kasa, idanunsa suka zazzago waje, Da azaba ta ishe shi Ya fara yi masa magiya akan yayi hakuri Ya kyale shi, kada ya kashe shi, koya manta abokantakar da ke tsakanin su.

Wata shu'umar dariya Danish Ya fasa hahahahaha da wata irin budaddiyar Murya ya furta"baka cancanta ka rayu ba, saboda baka da tausayi, mugunta da zalunci kadai kasa a gaba, burinka kaga bayana, saboda nafika a komai, yanzu zan saukaka maka kishin da kake akaina, Idan na kashe ka ba zaka
ara ganina ba, balle har ka
ulla ce ni aranka"
ya karashe maganar tare da matse wuyansa, ta yadda ko numfashi bazai iya fitarwa ba gurnani ya dinga yi yana ta kokarin kwatar kansa, azaba tasa ya saki fitsari, majina ta dinga zalalowa ta hancinsa..
saida ya tabbatar bazai kara amfanuwa ba, tukunna Ya jefar da gangar jikin shi kasa.

Kunaman dake a cikin rijiyar da macijjai suka daddabe shi, suka dinga kai mashi sara da
alli..
ya dinga sakin Ihun azaba, Danish yana atsaye yana kallonshi har saida ransa yabar gangar jikin shi tukunna Ya daka tsalle Yayi sama Ya nufi murfin rijiyar yana karasawa Ya sakar mashi naushi
aya nan take murfin Ya balle biyu ya duro akan kafafunsa kuma nan take ya dawo cikin hayyacinsa..
yanayin fuskarsa ne ya sauya zuwa tsantsar tashin hankali da damuwa ganin gawarwakin sojoji barbaje a kasa, wasu gawarwakin ma ginin daya ruguje Ya rufe su ba'a iya ganin su, babu wani mai rai, kuma kwatata babu gawar giants a gurin sun 6ace 6att..
bawan Allah, aru
e ya shiga neman gawar Chief da ta daddyn Unaisah, da Salsabeel, ya dinga bin gawarwakin yana dudduba fuskokinsu, tuni ya hada gumi, zuciyar shi ta karaya ganin babu corpses din su kwata kwata, da karfi ya dinga kwala masu kira tamkar makoshinsa zai balle shiru babu mai amsa mashi, bakin cikine ya turnuke zuciyar shi, yaji takaici, ganin duk kokarin da yayi don su rayu ya tashi abanza, wata irin
ara ya fasa mai kuwar gaske har saida ginin Ya girgiza.

Bakomai ne Ya fa
o masa aransa ba face tsohuwa khala, cikin sauri Ya zu
unna a gaban gawar wani soja, Ya tu6e kakin sa Ya zura a jikin shi..
Chapter 175 · 0% Book details