← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 201

Sashe 38

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

At same time ziyad da captain Yaseer dake kwance kasa suna bacci suka farka sakamakon kira'ar imam data cika kunnan su kamar wadanda suka sha kayan maye a kasalance suka mi
e zaune tare da jingina bayansu jikin Sofas.

Kowan nan su saida ya shanye ruwan dake acikin robar sa, kafin suka jefar da robobin...

Sai lokacin
walan su su ka dawo bakin aikinsu, sunyi mamakin ganin gari ya waye, ko da suka ga shiekh Imam dake a zaune Yana kira'ar alkur'ani, kusan atare suka sauko daga kan sofas din ko mikewa sun gaza yi saboda rashin kuzarin jikin su, da rarrafe suka
arasa gaban shi, gaba daya suka kewaye shi kamar zasu lullu6e shi da karajen su, babu wanda bai jigata ba a cikin su, jiya izuwa yau saboda tashin hankali Har fa
awa sunyi, kwarin idanunsu sunyi ja musamman masu hasken cikinsu cheeks dinsu sun yi ja.
shesshekar kukan su ce ta cika kunnuwan shiekh imam malik, baisan sa'adda ya dakata dayin karatun alkur'anin ba yabisu da kallo mai cike da ru
ani, hankalinsa ya tashi da jin yadda juraman maza kamar su suke kuka da idanunsu..
hankalinsa atashe ya fara tambayarsu meke damunsu?

Me yasa suka fita hayyacinsu.
rurru
e hannayen shi sukayi cikin raunanniyar murya su suka soma fadin .

"Baba Imam mun shiga uku, mun bani shiekh, muna a cikin musiba, baba yaja mana bala'e, zuciyoyin mu sunyi rauni, hankalinmu ya tashi, anyi mana bakin tabon da bazai taba goguwa ba..."
gaba daya sun ru
a Imam malik Ya rasa gane ina maganganunsu suka dosa.

Tun da suka fara yin magana su Captain suka shiga rudani, sun rasa gane ina zancen su ya dosa?

Shin me baba ya akai ta ne?

"baba ya kunsa mana bakin cikin da har abada bazai taba barin Zuciyoyin mu ba, Ya ha'ince mu, Ya zalunce mu, ya kashe mana rayuwa, kuma ya cuci kan shi, sheikh tun jiya gobara ta kama ci acikin zuciyoyinmu bamu iya kashe wutar dake konata ba sai da kayi mana karatun alkur'ani mai girma tukunna muka samu sassaucin radadin da muke ji" wani irin fa
uwar gaba Imam malik yaji adabarbarce yake rarraba idanunsa akan fuskokin su..

"Baba Imam ka tayamu rokon Allah ya dauki ranmu mu huta, watakil hakan ya zama sauki agare mu, saboda bazamu iya cigaba da rayuwa ba, da wani ido zamu dubi duniya? kowa zai juya mana baya, zamu zama abun gudu, baba imam bakin ciki zai kashe mu,...." ya fahimci wani mummunan abune ya faru da su kuma daga maganganunsu ya gane baban su ne ya jefa su a halin da suke a ciki..

Jikinsa ne yayi sanyi tamkar babu laka, tsantsar tausayinsu ne Ya kama shi, tun kafin ma yaji abun da zasu fada masa..

A hankali ya soma
aura tafukan hannayensa asman kawunansu kamar kamun ciwon kai ya ke yi masu, addu'oi ya soma karantowa yana shafe masu kai..
cikin ikon Allah nutsuwa ta fara shigar su, numfashin su dake fita a hargitse ya fara daidaita, wani irin gumi ne ya soma wanke goshinsu alamar zazzabin jikinsu ya fara sauka..

"Ba sai kun fada min abunda ke damun ku ba, na riga dana sani, sai dai karin bayani da zan nema..." arude suke kallon shi da tsantsar al'ajabi .

"Shiekh, taya akai ka sani?

Mun shiga uku, shikenan kowa ya riga daya san miyagun ayyukan da baba ya ke aikatawa, kowa ya sani, tamu ta kare, mun bani .."
Senate Lateef ne ya fada tare da daura hannayensa asaman kansa..

Cikin sanyin murya Imam yace"Lateef, babu wanda Ya sani, daga Allah, sai ku sai kuma ni, nima din bakomai na sani ba.."
"Kwana daya da banganku a masallaci ba, Hankalina Ya tashi, bani kadai ba, hatta jama'ar dake halartar masallacin sun damu da rashin ganin ku, kowa muka kira layinsa a cikin ku bama samu, shiyasa na yanke shawarar zuwa nan din dan in duba ku, saboda naji araina ba hakanan ku ka ki zuwa masallaci ba..." ya dan dakata tare da jan numfashi kafin ya kuma cewa" Ba jiya bane ku ka yi family meeting ba?

Ina Owais ina kuma sauran ahlin naku"?

Sai lokacin suka tuna da shi, Kowa Yana ta kan shi, cike da rashin
warin jiki sharafudeen Ya mike tare da juyawa a hanzarce ya nufi cikin gidan ya bazama neman sa, saboda yaji aransa bai fita ba, watakil ya fada wani gurin daban..

"Bakowane Ya samu damar halarta ba..." His excellency deen ne ya fada yana sharce kwallarsa, da yatsan hannunsa Ya nuna su Justice yace "su kadai ne, suka zo, sauran Uzirurrukane suka ru
e su..."
kwata kwata bai nemi su fa
a masa ainihin abun da ke faruwa da su ba.

Takun tafiyar su ne Yaja hankulansu ga duban inda sautin ke fitowa, Sharafudden ne ya 6ullo Hannunsa ruke da damtsen Owais dake ta layi kamar wanda yasha kwaya..

Gwanin ban tausayi suke kallon shi, Hankali atashe su justice suka mike tare da nufar shi, kwata kwata basu san yana a gidan ba, sakar musu shi Sharafudeen yayi, cikin sauri suka tallabesa tare da rungumesa suna tambayar shi meke damun shi?

Meke faruwa da shi?

A ina ya kwana?

"Can na tsinto shi a back room din baba, Ina tunanin tun jiya acan ya kwana..."
Hankalinsu Ya kara tashi basu taba ganin Owais a mawuyacin hali irin wannan ba, ko magana bai iyayi, fuskarsa duk jirwayen hawayen sa..

"Ku miko min shi nan" sheikh Imam ne Ya fada Tare da mika musu hannu, Ruko shi Captain yayi ya taimaka masa Ya karasa ga imam, Jikin nasa ne babu kuzari gaba daya ya durkushe saman gwiwowinsa agaban Imam Malik.
tallabo keyarsa yayi tare da janyoshi Ya fado kan kirjinsa, cikin sigar lallashi Yake dan bubbuga tafin hannayensa akan bayansa, a hankali ya fara karanto addu'o'i yana tottofa masa asaman sumar kan shi..

"tun da yanzu kun riga da kunsan komai babu batun boye boye a tsakanina da ku, maganar gaskiya daliline yasa na shiga jikin ku don in samu kusanci daku saboda in tabbatar da abun da nake zargi akan family din ku..." da rudu suke kallon Imam, maganarsa ta daga hankulan su, owais daya fara dawowa hayyacin sa, cikin kunnansa ya tsinkayi maganar Sheikh Imam da mamaki ya dago da kansa yana dubansa..
yadan numfasa kafin ya daura cewa"ni Allah yayi min wata baiwa In har zan zauna tare da mutum mai bakin sihiri a jikin shi wlh sai naji a jikina, Mahaifinku da surukinku pravin na dade da sanin suna da sihiri a jikin su amma ban taba bayyana maku ba, saboda bani da isassun hujjojin da zan tunkare ku da maganar, lokacin dana fara kutsa kaina ga mahaifinku har na samu ya yarda dani rana ta farko daya gayyaceni don inzo in gana daku, sai da gabana ya fadi ganin yadda kukeyi masa biyayya sau da
afa, kun yarda da mahaifinku kuna son shi, jikina yayi sanyi dama tun kafin na gane ma idona, sai da naji abakin mutane amma dana gani da ido abun ya karya zuciyata, nayi al'ajabi yadda kuka kasance masu kyawawan halaye da dabi'u kun fita daban, samun irinku zaiyi wuya, Allah bai rageku da komai ba, sai dai kash mahaifinku yayi muku cikas, 6atacce ne ku kuma tsarkakakku ne, wallahi a lokacin koda na fadamaku ba zaku yarda dani ba, zama ku iya tunanin turo ni akayi don inyi masu kazafi, watakil ma kusa a daure ni, shiyasa naja bakina nayi shiru, amma duk da haka ban hakura ba, saboda Allah ya jarabceni da kaunarku, naji inason in taimake ku shiyasa nabiyo ta bayan fage batare da sanin kowa ba, na fara kiran Owais ta boyayyiyar number, na fada masa ya bincika family dinsa akwai bara gurbi a cikin su...." dafe kai Chief Owais yayi da tafin hannunsa bakinsa abude da tsantsar mamaki yake kallon Imam wai ashe shine boyayyan mutumin dake kiransa awaya..

"Sheikh dama kaine boyayyan mutumin dake kirana awaya?

Ya fada arude, murmushi Imam malik ya sakar masa"Nine Owais, nasan za ka yi mamaki, kamar yadda kake amfani da brain dinka nima haka nake amfani da kwakwalwata, ban taba bari ka gane nine ba, na toshe duk wata hanya da zaka iya bin diddigin layin da nake kiran ka da shi, bayan haka duk idan zamuyi waya ina canza murya saboda bana so ka gane nine..." dafe kansa yayi da tafukansa Shiekh Imam Ya basa mamaki, yayi zaton malamin addinin islama ne ashe bayan kasancewar shi alkali har ilmin computer gare shi saboda ba karamin wahala ya bashi ba, yasha ya zauna ya baje basirar sa gurin gano wanene boyayyan mutumin dake kiransa amma ya kasa kamar Aljani haka ya koma masa, kowa dake awurin yayi mamaki sosai..
e hannayensa Chief yayi"meyasa tuntuni baka fito fili ka fada min kaine ba?

Why pls?

Da ka fadamin ay da tuni na dauki mataki akai"
Shafa sumar kanshi imam yayi"Owais, koda na fada maka ba zaka yarda ba...."
"Dan Allah ku fada mana meke faruwane?

Tun jiya kunbarmu a duhu, ku sanar damu mana!

Kunce baba Ya kulle kansa adaki, meyasa yayi hakan?

Wani laifine ya aikata da da yaja har kuka shiga mawuyacin halin nan.."?

Cike da damuwa Ziyad ya tambaya yana binsu da kallo gaba daya fargaba ta hana su bude baki su furta..

Captain yaseer daya gama Fusata zuciyarsa tazo wuya rai a6ace yace"nagaji da jiran ku fada mana, gaba daya kun tada mana hankalinmu, kuma kunki ku sanar damu meke faruwa, wlh da nasani da banzo ba.." ya fada yana girgiza kansa..

Marairaice fuska justice yayi tare da kallon sheikh Imam tamkar zaisa kuka yace"Dan Allah baba Imam ka fada mana tunda su sun
i su sanar damu, pls ku taimaka ku fada mana meke faruwane mun kasa gane inda zancenku ya dosa...."
bai
arasa maganar ba, Chief Owais Cikin raunaniyar muryarsa da ta disashe ya fara zayyana musu abunda ya faru jiya kafin a fara family meeting, tiryan tiryan ya fayyace musu tun daga biri har wutsiyarsa..
Chapter 38 · 0% Book details