← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 201

Sashe 150

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar kuwa ta sani, bayan rasuwar Uncle dinta, ta canza salon cuzguna mata, har maza take dauka haya ta biya su ku
i don su farmaketa saboda kawai ta shiga tsakaninta da mijin ta, amma Allah bai nufa ba, kullum batayin nasara akanta, kuma takasa tankwara zuciyar Abraham akan ya rabu da turai saboda a lokacin ya kara sonta fiye da da saboda kafin mutuwar daddynsa lokacin dayake jinya agadon asibiti saida ya roke shi akan ya kula da rayuwar yar uwarsa, ya bar mashi amana, Yasan step mom din sa bata sonta, zata iyayin komai donta rabashi da ita, don haka ya kula da rayuwarta, duk runtsi duk wuya karya rabu da ita, wannan wasiyar da babansa yabar masa ce tasa baya sauraron maganar Beatrice, akan Turai sun sha samun sa6ani da ita, saboda ya bijire mata akan Umarninta.
a lokacin da Jazz yakai shekaru Biyar, daddynsa ya rasa ranshi a wata tafiya da ya yi tare da abokan kasuwancin shi, daga London zuwa turkey, Jirgin su yayi Crashing, yana
aya daga cikin wadanda suka rasa ran su.

Turai tayi bakin cikin mutuwar shi har saida ta yi rashin lafiya kamar bazata rayu ba, bayan da ta samu lafiya, ta fara tunanin menene mafita?

Saboda tasan a yanzu bata da gata daya wuce Allah, Wadanda suke kare ta daga sharrin Beatrice sun mutu, ta kuma san bazata kyale ta ba,
tunda yanzu ta samu damar da zata iya salwantar da ita, aikuwa awata rana kwatsam tajiyo firar da su ke yi tare da aminiyarta adaki akan yadda zasu kasheta su gaje dukiyar Abraham, har tana fadin ita babban bakin cikinta, gaba daya sunan Turai ne akan kadarorin sa, ga lauyansa dake kokarin tsaya ma turai da danta don su kar6i hakkinsu, sai kawar tace"abun daya kamata suyi kafin araba gadon dukiyar tashi, su bi ta bayan fage su kashe Turai, sai su bar danta su ruke shi a hannun su ta yadda ba za'a zarge su ba"
Koda jin wannan firar tasu hankalin turai ya tashi matu
a, tayi mamakin jin furucin matar Uncle din ta, ta rasa gane meyasa ta tsaneta har haka?

Bata san cewa ita bata damu da dukiyar shi ba, burinta ta zauna lafiya da ita, amma da taga da gaske kasheta zasuyi sai tayi dabarar kiran lauyan mijinta ta fada mashi abun dake faruwa, ya nuna damuwarsa yace in ba damuwa su dawo gidansa da zama zai basu tsaro, sannan zai kai
arar Beatrice akan furucin kisa da ta furta mata, turai ta nuna kin amincewarta akan shawarar shi, tace ita kawai bata jin zata iya cigaba da zama a kasar, ta rasa gatanta, ta tsani zaman london tafi son tayi nesa da su ta tafi can wata kasa inda zata raini danta, kawai ya taimaka mata su siyar da kadarorin mijinta da komai nashi batare da sanin Beatrice ba, Lauyan baiso shawarar data yanke ba, amma da dayaji irin barazanar da Beatrice keyi mata sai ya go yi bayan ta bar
asar, kuma hada karin kalaman data furta na cewa ta tsani zaman kasar kuma shi mai biyayyane ga umarninta saboda amanar dake a tsakaninsa da Abraham.
ta bayan fage suka siyar da kadarorin Mijinta, dama Black card dinsa Yana a hannunta, tun bayan rasuwarshi ta ke boyen shi, Beatrice tasha tayi mata barazana akan ta bata komai nashi, a lokacin harta
wace mata key din motar, nema take ta kore ta daga gidan, amma saboda gadon Abraham data
wallafa rai akai Yasa ta dakata tana jiran ta kwace komai kafin ta koreta.

Batare da sanin Beatrice ba, Lauyan ya taimaka mata suka siyar da kadarorin Abraham gaba daya kudin ya zuba mata a account din sirri daya bude mata, shine ya bata shawarar ta dawo abuja ta zauna ta bar nahiyar su, saboda shi dan asalin nigeria ne mazaunin abuja anan family dinsa suke, karatune yakai shi england harya zama lauya acan.

A takaice da taimakonsa Turai ta gudu daga england tare da danta jazz suka zo Nigeria, agidan daya kama masu haya suka zauna, komai da ta ke bukata da kudin gadon su ta ke yi masu, Lauyan nan shike kula da su, duk da ba anan yake da zamaba amma baya gajiya da kiranta awaya don yaji ya lafiyar su..

Turai bata yi aikatau saboda rashin kudi ba, ra'ayin kanta ne, aranar da data tsinci Domestic Staff
Application daga Obie estate a social media yana yawo
hakanan taji tana son ta jaraba neman aiki, ko ta samu family din da zata jingina da su, musamman da taji labarin Family din Obie, nan take ta cike form din da bayanan ta, cikin Ikon Allah bayan kwana uku sai ga sakon Interview invitation ya shigo ta email din ta.
taji dadin da ba zai misaltuba, ko da ta tashi zuwa yin interview din sai ta sanya sutura mara tsada, ta tafi tare da Jazz, a lokacin ba hajjaty bace head maid ba, bata ma kaiga zuwa Nigeria ba a lokacin, bayan da taje head maid din lokacin ta yi masu interview ta tantance wa
anda suka kware gurin aikatau, Turai tana daya daga cikin su, taji dadi sosai musamman da suka ware mata dakin ta, gaba daya ta dawo da zama tare da Jazz dinta ta baro gidan da ta ke haya.
a lokacin tana jin dadin zaman gidan saboda baba Obie yana mutunta ta, yana kuma son danta jazz, Kowa ya tambayeta ina daddynsa sai tace masu bazata iya tunawa da rayuwarta ta baya ba, ta dinga nuna kamar tayi loosing memory saboda kawai batason kwata kwata labarin inda take ya komama Beatrice, tasan ba kyaleta zatayi ba, ta dade tana boye ma kowa identity dinta, ga dukiya tana da ita amma bata nunawa, ko jazz baisan tana da arzi
i ba, sai bayan Shari'ar Elders Ta damka mashi gadon shi, bayan ta labarta mashi komai game da danginta da irin rayuwar da tayi agidan Uncle dinta, ta kuma bashi hakuri na kin fada mashi da batayi ba da kuma dalilinta nayin hakan.

Turai ta musulunta ne saboda kyautatawar da musulmai yan uwanta masu aiki sukeyi mata, tana jin da
in yadda suke yin mu'amalarsu wannan ne yaja hankalinta har ta musulunta, ta sauya sunan ta daga Harriet zuwa Khadija, shi kuma Jazz daga Eric zuwa Abubakar, sunan Jazz nickname ne da baba Obie ya ke kiran shi da shi saboda yadda ya ke son Music.

Tsanar da hajiya saratu tayi mata ta samo asaline saboda auran ta da sir mubarak yayi bayan rasuwar matar shi ta farko, a lokacin Saratu ta tsani talaka bare mara asali, kuma tana zargin danta shege ne shiyasa batason asan labarin ta, wannan yasa ta
aura mata karan tsana a lokacin, taso ta shiga tsakaninta da sir mubarak lokacin da taji suna soyayya amma Allah bai nufa zataci galaba ba har saida Ya aureta Ya dauke ta daga gidan baban tare da danta ya mayar da su gidan shi karkashin kulawar shi
*(Wannan shine ta
aitaccen labarin Turai da Jazz)*
*BAYAN WASU SHEKARU DA RASUWAR ELDERS
Katafariyar Jami'a ce da ke a cikin birnin Abuja, tana
aya daga cikin makarantun da suka shahara a fa
asar, kuma tana daya daga cikin makarantun da suka wadatu da ababen more rayuwa.

Shin meke faruwa ne a cikin wannan Hamshakiyar makarantar, naga interior designers daga kamfanin Zahra World Of beauty sun dage damtse sunata
awata katafaren event hall din makarantar, da wajen Pool da kayan ado masu matu
aukar ido da jan Hankali..

Ashe Yau babbar rana ce mai muhimmanci ga malaman makarantar, kasantuwar yau ce rana ta farko da za su fara yaye
aliban jami'ar da suka kammala karatu.

Gaba
aya Glass windows din Makarantar, da saman gate din makarantar wani hadadden rubutune ke displaying
auke da sunan Jami'ar.

Da abaka labari
wara ka gani da idonka, don haka ni ma bazan bari abarni abaya ba, dani za'ayi shagalin yaye daliban nan, saboda in bawa idanuna abinci...

Around
arfe 12 na safe daidai agogon Nigeria ta buga, a wannan lokacinne School buses suka fara shigowa ta main gate din makarantar,
auke da Students a cikin su, daga jikin buses din hada Tambarin makarantar da suke mai
auke da sunan Imam Educational Institute (IEI)
Kaitsaye buses din suka nufi Parking space na jami'ar.
ura idanuna ina jira inga su wanene
aliban dake a cikin Buses din.

Lokacin da Bus divers din suka yi parking, kofofin motocin suka soma bu
Tabarakallahu
Gaba
aya na ru
e ganin Ex-prisoners na kurkukun
addara suna fitowa daga cikin buses, sanye cikin uniform din su kyawawan gaske sun sauya daga ka gansu kaga ya'yan hutu wadanda suka gaji arzi
Yan Secondry School
in suna a sanye da kyawawan Uniform
in su,
an matan sun yi rolling head scarf, ya yin da mazan kowan nan su ka kalli kanshi ha
en haircut ne na wayayyu.

Admins din makarantar ne su ka yi inviting
aliban Makarantar Imam da iyayensu donsu taya yan uwan su murnar kammala karatu, dress code din da suka basu shine uniform din su shiyasa kowannan su ya sanya uniform din shi banda Yan jami'a su nasu kayan gidane as usual suna asanye da Casual dress na kece raini.

Rayuwa kenan, waya taba tunanin bayin Allahn nan zasu samu yan'ci da canjin rayuwa?
Chapter 150 · 0% Book details