← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 201

Sashe 86

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Doc din yace"har yanzu bai farfa
o ba, amma muna ganin cigaba a lafiyarsa, kuma muna sa ran zai iya farfa
owa a kowani lokaci..."
da jin maganar da doc din ya fa
a nan fa hankalinsu Ya
ara tashi..

Jikin Taj ya hau yin kerma
"in kuwa hakane, Koma wanene ya
auke su zai iya yiyu wa daga Elders ne, tun da har ya iya sauya kamannin shi, hakan na nufin matsafi ne, amma tayaya za'ay mu san wanene Ya
auke su? chief ne ya jefa ma kanshi tambayar da bashi da amsarta.

Damuwace tsantsa akan fuskar taj "inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un bana fata hakan Ya kasance saboda nasan ba zasu masu dakyau ba, da nasani ban tafi nabar su ba, laifina ne, da duk hakan bata faru, rashin sani yasa dukan mu bamu ga
kiran Unaisah ba, ni nasan
tayi iyakar kokarinta donta same mu awaya, kuma inaji raina ba hakanan aka tafi da su ba, saboda Unaisah tana wayou dole akwai wani abu da akayi masu..."
zafafan hawaye ne suka wanke Fuskar shi, ga wani zazzabi da ya rufa sa.

Sum ma rasa ta ina zasu fara binciken wannan al'amari?

Wanene Ya dauke su?

Meyasa aka sace su?

Da wata manufa akayi hakan?

Me kuma zai biyo baya!.

Babu wani mai kwanciyar hankali a cikin su, sam sun manta da batun Ummi.

Taj Ne ya kawo shawarar Su jaraba Bin diddigin Layin Unaisah, yana tunanin Ta tafi da wayarta tun da basu ganta a dakin su ba.

A hanzar ce Chief Ya fara
arin yin tricking din layin ta ta hanyar wayar sa, sai dai bai Iya gano komai ba duk
warewar sa.

Har Number dinta Ya turama wasu Cyber Experts daga Cikin jami'an su, amma daga baya suka kira tare da sanar da shi sunyi iyakar bakin kokarinsu don ganin sunyi hacking layinta, amma sun kasa gano ta
amaimai location din da wayar ta ke, suna tunanin tana a gurin da babu network ko kuma an jefar da wayar wurin da baza a iya tracking ba.
bakin Ciki ne Ya cika Zuciyoyin su.

Daga shi har Taj an rasa me lallashin wani kowa Ya shiga damuwa.

Tunanin komawa Cikin gidan su ka yi don su kara bincikawa su tabbatar babu su din don jin abun su ke kamar ba gaske ba.

Babu inda basu duba ba, suma officers din gidan sun tayasu neman su, babu su babu alamar su, Kowan nan su sai da ya ha
a gumi akan fuskarsa.

Falo suka koma su biyu shida Taj suka zauna saman Sofas kowan nan su ya zabga Uban tagumi kamar marasa galihu.

Unexpected suka tsinkayi sautin tafiya, kusan atare suka kalli Mai shigowa cike da sa ran su Unaisah ne.

Kamar mahaukaciya ta fa
o Falon, Ko takalma babu a kafafunta, fuskarta jaga jaga da hawaye, idanunta sun kumbura suntum, gyalenta ma A hannu Ta ruke shi, har suna ha
a baki gurin ambaton Sunanta UMMI..

Kusan atare suka mike suna Kallonta ganin Yadda ta sauya lokaci
aya kamar wadda tasha bugu.

Kaitsaye Ta nufi Chief Tana karasawa gaban shi, Ta zube kan gwiwowinta, kamar zata haukace masu, Cikin Kuka da wata irin raunanniyar murya ta furta"zai..

Zai kashe su!

Shine Ya
auke su!

Suna a wurin shi, Kashe su zai yi..." gaba daya ta ru
ar da su sun kasa gane kan maganarta.

Faduwar gaba suka ji, daram dararam, a razane suka kalli juna.

"Ummi ki yi mana bayani meke faruwa?

Su wanene zai kashe?

Kuma wanane kike magana akai"?

Cikin shasshake murya tace"U..U..Unaisah, da Bab..

Ba tool, Ya fa
a min komai, Ya cuce ni, ya yaudare ni, shiya rabani da mahaifina Ya kuma rabani da kowa nawa, Batool diya ta ce, Ita ce babyn dana bari, bata mutu ba, tana araye, shiya sadaukar da su yanzu kuma Ya kara
auke su ....."
Tsantsar tashin hankali ne
arara akan fuskokin su, Sun riga da sun gane wanene Ya
auki su Unaisah, dama sunata hasashen zasu kawo masu farmakin bazata, ba zasu ta6a kawo ma ransu ta kansu Unaisah zasu biyo ba, Wlh sun shammace su, ga kuma Mamakin kasantuwar Batool diyarta.

"Ummi Ki natsu ki fada mana komai da kuka tattauna da shi, watakin mu samu ta hanyar da zamu iya ceto rayuwar su, mu kan mu bamusan tayaya akai suka dauke su ba, saboda ba mu a cikin gidan"
Dakyar ta iya fayyace masu komai da Alhaji Musa ya fa
a mata.

Ba su yi mamaki ba saboda sun riga da sun san komai itace bata sani ba, abun da yafi bakanta ransu ta yadda ya bayyana mata komai da yayi mata batare da tunanin wani hali zata shiga ba.

Kwata kwata basu tambayeta meyasa tayi gangancin daya gano ta ba, duba da halin da take a ciki ba.
uwa sukayi atare suna Lallashinta tare da yi mata alkawarin zasu yi iyakar bakin
arin su don ganin sun Ceto rayuwar su.

Dakyar suka shawo kanta, Taj Yace Ta shiga ta kwanta, ta huta.

Tace mashi ita da hutu Har abada, bata tunanin zata iya rayuwa batare da Yar ta ba, don basu san me take ji a cikin zuciyarta ba.

Tsananin tausayinta ne Ya kamasu, kamar zasu zubda mata
walla.

Tace ma Taj ya ara mata wayar shi, Tana son tayi kira.

Ya tambayeta wa zata kira?

Tace Ya shureim tana son Ta fada masa komai.
chief Yace tayi hakuri ka da ta daga mashi hankali, Ta bari su fara samun mafita tukunna
Kuka tasaka masu tare dayi masu magiya tana rokonsu akan su bata ta kira shureim tana son ganin shi tana son ta nemi yafiyar shi, sannan tana so ta fa
a mashi game da babyn su.
in amincewa su kayi, gaba daya ta rikice masu kamar ta fara fita hayyacinta sai sambatu ta ke yi masu, can Kuma data galabaita wani matsanancin ciwon 6arin kai Ya taso mata, ta fara ganin jiri jiri tun tana karanta addu'o'i harta kasa, ta fada masu kanta ciwo yake mata, kirjinta zafi, numfashinta zai
auke.
da sauri chief ya juya yaje medical room din gidansa ya
auko mata sedative, ya dawo falon tare da Glass of water a hannunsa ya mika ma Taj ya kar6a tare da mi
a mata maganin hannunta na kerma ta kar6a ta tura abaki, ya kanga mata ruwan ta sha, har saida takusa
warewa kamar za ta yi amai ta kama kakari.
sun bata maganin da nufin ta samu tayi bacci amma sai ya zamana kamar sun
ara ninka mata azabar radadin da take ji, baiwar Allah kamar
aramar yarinya ta dinga rusa masu kuka tana ambaton sunan Baba imam, shureim, Babynta.

Har tambayar ta su ka yi ta fada masu address din Guest house din sa, tace bata sani ba, sau biyu ta ta6a zuwa, kuma duk zuwan da zatayi shi ya ke zuwa
aukarta da motar shi, baya bari drivern daya
aukota ya karasa da ita, ba zata iya gane komai ba, ko sunan anguwar bata sani ba.

Gudun kada ta hadiyi Zuciya ta mutu Yasa suka yanke shawarar bata wayar donta kira su, bayan Taj Ya nuna mata Contact din su a wayarta yace ta kira su ta ce su zo amma kada ta fada masu meke faruwa ta bari sai sun zo.
dama Suna da burin Su sasanta tsakaninta da Mahaifinta, kuma a wannan ga6ar tana bukatar su saboda su kadai ne zasu lallasheta taji don wlh gab ta ke da ta zare.

Chief bai ga ta zama ba, yace ma Taj Ya kula da ummi, shi zai tafi tare da jami'ai su nemo su, Taj yace bazai iya zama ba,
wara su tafi a tare, saboda Hankalinsa ba akwance yake ba, in har ba dawo da su Unaisah akayi ba.

Chief yace ya kwantar da hankalinsa in sha Allah ba abun da zai faru da su, amma ba yadda za'ay su tafi da shi saboda har yanzu
afarsa bata daidaita ba, kuma gurine mai hadari zasu je, Taj yana sharar kwalla yace"bazai gane ba, tayaya ma zai iya kwantar da hankalinsa bayan yaransu suna a hannun fasi
in mutumin da babu imani a zuciyarsa?

Wa yasan me zai yi musu?

Dakyar Chief ya lalla6a shi harya amince zai zauna badan yaso ba.
*Dr.

Shureim
Bayan ya kammala Yin Nafila Ya bu
e kur'ani yana karantawa, wayarsa ce ta soma yin ringing, saida yakai aya, Ya dubi wall Clock Karfe shabiyu, Aransa ya ayyana wanene ke nemansa a irin wannan Lokacin?

Ko dai na cikin gida ne"?

Mikewa yayi daga kan prayer mat din, Ya nufi wayar dake aje kan gadon nasa.

Daukar wayar yayi da rudu Yake kallon bakuwar Number din da aka kirasa da ita.

Baisan wanene ba, Kuma ba ya jin zai iya picking call at this time duk da wani sashe na zuciyarsa yana shawartarsa dayabi bayan kiran.

Har zai aje wayar wani Kiran ya kuma shigowa.

Picking Yai tare da kara wayar Yana kokarin Yin sallama, kunnuwansa suka jiyo masa sheshshekar kukan mace ta cikin wayar, gabansa ne ya fadi
Bai gane wacece ba, addu'ar neman tsari Ya karanta a cikin zuciyarsa kafin Ya yi sallama tare da tambayar wacece?

"Ya shureim ni ce, Aishatu bintu imam ce.."
sa'ilin da muryarta ta ratsa dodon Kunnansa wani sanyi mai ha
e da dadi yaji a cikin Zuciyar shi, kamar wanda akayiwa albishir da gidan Aljanna
Adabarbarce Ya furta"Aisha dagaske kece?

Ba mafarki nake ba?

Ke da kanki kika kira ni"?

"Ni ce Ya shureim, Ba mafarki bane..." bai karasa jin zancen nata ba Ya zube kan gwiwowinsa Ya fuskanci alkibla yayi sujudusshukr..

Time din da ya dago Hawaye farin ciki ne a kwance saman fuskarsa ga wani tsantsar annurin farin Ciki daya bayyana a tare da shi.

"Aisha, har yanzu Ina kokwanto.."
"Ya shureim, Inason ganinka! pls ka zo, idan ba kazo ba zan iya rasa raina, kai kawai nake son gani.."
muryarsa da zumu
i ya firta"basai kin rokeni ba, Zanzo yanzu, Karki damu, ki kwantar da hankalin ki.."
Katse kiran yayi, jikinsa na 6ari Ya dauki Car key nasa, cike da zumu
i ya fito Jikinsa na bari cikin sauri Ya nufi Hanyar fita daga Main falo..

Kafin Ya
arasa Ya tsinkayi Muryar Benazir a cikin kunnansa.
Chapter 86 · 0% Book details