← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 201

Sashe 56

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wallahi we must take revenge for what she did to our mom, She must feel the pain our mom felt, jiya daga mu har ita babu wanda ya runtsa, muna jiyo sambatun da ta dinga yi tana ambaton sunan hajjaty da na daddyn mu..."
Maganar Zayn ta
ara karfafa zargin su akan Pravin da Hajjaty tun da har Saratu tayi sambatun sunayen su, hakan na nufin sune suka yi mata aika aika, senate Lateef ne ya ce su yi hakuri yanzu haka su kansu basu san inda daddynsu yake ba, amma suna sa ran zai dawo nan bada jimawa ba, ita kuma hajjaty sun yanke shawarar zasu baza jami'ai cikin gari su nemo ta.."
Dakyar suka shawo kan su, bayan kamai ya lafa suka karasa shiga dakin, a kwance suka hango hajiya Saratu sanye da patient gown, fuskarta a na
e take da bandage, idanunta da lips dinta ne kadai abude, baiwar Allah ta galabita sosai ko idanunta bata iya bu
ewa, jikinta sai kerma ya ke yi musamman yatsun hannayenta da suka raunata har
auri aka yi masu saboda gocewar da su ka yi.
cike da tausayawa suke kallon ta, biyu daga cikinsu ne suka ruke hannayen ta, yayin da docs din dake a tare da su suka fara kora masu jawabi akan abun da ke damunta, abun da ya
ara daga hankulansu jinin ta da ya hau, tun jiya ya
i sau
Duk da doc din sun ce zasu yi iyakar bakin kokarinsu don ganin ta samu lafiya, kuma tafi bukatar duk wani abu da zai kwantar mata da hankali saboda akwai depression atare da ita.

Koda jin wannan maganar nan fa suka hada baki gurin lallashinta da bata baki kuma suka tabbatar mata cewa sun gano wadanda suka jefata a halin da take a ciki kuma soon zasu kama su don su hukunta su, da kanta ma suke so ta dauki fansar abun da su ka yi mata.

Lokacin da suke fada mata maganganun nan, ta yi ta kokarin bude idanunta don ta samu ganinsu sai dai ta kasa saboda raunin da su ka yi mata, la66anta na kerma ta furta, "babb..pur, hahaj"
Bata
are maganar ba, Sharafudeen ya yi saurin tarar numfashin ta da cewa, "Don't force yourself to talk, you'll hurt your wound, I know what you want to tell us, As we told you, we've already found out everything, and we'll take action So, please calm down, we don't want you to worry, and we don't want to lose you.

In sha' Allah, you'll feel better soon"
Kalamai masu da
i mr. president ya gaggaya mata duk da halin jinyar da take a ciki saida ta ji sanyi aranta, musamman da ta ga yadda suka nuna damuwa akanta, kowa lallashinta ya ke yi da bata baki, kamar kar su tafi su barta saida su ka shafe rabin awa adakin anan ma har sharafudden ya kira p.a dinta ya sanar da ita cewa bata da lafiya an kwantar da ita asibiti, don haka ya dakatar da ita zuwa aiki, har zuwa lokacin da zata ji sau
i, p.a din ta nuna damuwarta bayan ta yi addu'ar Allah ya bata lafiya, ta ce zasu zo tare da sauran health staffs don su duba lafiyarta, bayan sunyi sallama kafin su bar room din saida kowan nan su ya yi mata addu'a, duk tana jin su sai dai ta kasa bu
e idanu ta dube su.

Lokacin da suka fito daga dakin yayi dai dai da zuwan Sarauta tare da hajiya Laura, da Turai tare da Jazz daga cikin villa suka nufo asibitin don su
ara duba patient din nasu, kowan nan su ka kalla babu walwala akan fuskarsa.

Gaba
aya suka nufe su, Jazz da sauri ya nufi Sir Mubarak ya yi hugging dinsa, bayan sun gaggaisa da junan su, Hajiya laura ta ja hannun Sharafuddeen suka koma gefe daya, Hajiya Malikat ma ta bi bayansu, tunkafin ma su fara magana ya labarta masu abun da ya faru da Saratu ya ce suma basu san me ya kaita dakin Hajjaty ba, amma suna zargin fada ne ya kaure atsakanin su, ita kuma tsohuwar da suke magana akan ta
ar uwar baba ce..."
Kwata kwata bai bayyana masu abun da ya faru na tonuwar asirin babansu ba saboda ba ya son su sani.

Cizon yatsa Hajiya Laura ta yi rai a 6ace ta ce, "Ni dama nasan za'a rina, hajjaty makira ce, ba dan Allah take a tare da ku ba, na jima ina zargin akwai wata makarkashiya da take yi maku, munafuka yar tsibbu, ba irin gargadin da banyi ma Saratu ba akan ta kore ta daga gidan, tama bar
asar ta koma India amma ta
i jin maganata ai ga irinta nan, kun kawo mugun abu kun aje a gida gashi nan tana neman ta halaka Saratu, dama ita take ha
o, tana bakin cikin ganin hajiya Saratu tafi ta komai, da yake bata san halacci ba, ni ban san ma tayaya akai har tafi
arfin Saratu ba, koda yake ai matsafiya ce da rauhanai take amfani, watakil ta asirceta ne shiyasa ta kasa tabuka komai har ta yi mata jahilin bugun nan, kuma wlh koma gidan uban wa hajjaty ta shiga dole a nemo ta.."
tun da ta fara maganar bai katse ta ba, ya fahimci ranta ya matukar 6aci, da zata ga hajjaty ba abinda zai hana ta binne ta da ranta.

Hajiya Malika kuwa tsabar al'ajabin abun da Sharafudden ya fada ya hana ta furta kalma, ta gaza yarda cewa Hajjaty ce tayi ma Saratu haka duk da bata mu'amala da ita, ko magana bata ha
a su in ba ta zo gaishe ta ba idan suka je gidan baba, amma tana kyautata mata zato, bata tunanin zata iya aikata abunda suke zarginta.

Sai da ta bari hajiya Laura ta gama magana da shi tabar gurin, sannan ta fuskance shi tare da marairaice fuska ta ce ya fada mata gaskiyar abun dake faruwa, saboda tun da ta gansu ta lu
ra da akwai damuwa atare da su, kuma ta ga alamun kamar sun yi kuka, sannan abun da ya faru da hajiya Saratu tana kokwanton in hajjaty ce ta yi mata hakan duk da ba agabanta komai ya faru ba, amma sun yi bincike dakyau?

Shiru ya yi batare da ya iya furta kalma ba, saboda ya rasa amsar da zai bata, yasan halin kayansa dama saida ya yi fargaban ta tuhume shi, babu mai iya karantar halinsa bayan shakikinsa sai kuma ita.

Jin yayi shiru bai bata amsa ba yasa ta ce, "kada ka boye min pls, damuwarka tawa ce, ban ta6a boye maka damuwana ba, saboda babu sirri atsakaninmu, abun daya shafe ku nima ya shafe ni tun da nima yar uwa ce, bawai iya matsayin matarka nake ba, ka taimaka ka fadamin in ba haka ba hankalina bazai kwanta ba, kuma matar da ka ce dangin baba ce, kayi hakuri amma ni ban yarda ba, nafi tunanin dangin momma ce saboda tayi kama da ita..."
Duk yadda ya so ya canza mata tunaninta ta
i bari, a karshe da ta kafe ya lallabata ya ce ta yi hakuri, tabbas akwai abun da ya faru da su, amma bazai iya sanar da ita ba, kada ta matsa mashi akan ya fada mata, ta yi hakuri har zuwa lokacin da ya ji zai iya sanar da ita.."
tace mashi in sha Allah zata jira har zuwa time da ya ji zai iya sanar da ita.

A bangaren Sir Mubarak, tuni shima Turai ta ja hannunshi suka ke6e, ta tambaye shi menene makasudin abun da ke faruwa? ta tambayi su twins sun ce mata hajjaty ce ta lahantata, sai dai ita bata yarda hajjaty zata iyayin hakan ba saboda ta yarda da ita, aminiyarta ce, tasan halinta ciki da bai, hajjaty ko kiyashi ba zata iya kashewa ba saboda tausayinta balle har ta iya yiwa hajiya Saratu haka, ita a saninta ma Hajjaty tsoron hajiya Saratu take ji saboda rashin jituwar dake a tsakaninsu"
Sir Mubarak ya ce, "Su kansu basu tabbatar da abun da suke zargi ba akanta, amma abun da yasa suke zarginta saboda guduwar da ta yi tun jiya har yau bata dawo ba.."
Hankalin Turai ba karamin tashi ya yi ba, cike da rashin jin dadi ta ce, "Pls duk da haka ku yi mata uziri, kada ku zarge ta, zai iya yiwuwa wani ne ya ke son
alla mata sharri, saboda a jiya kafin ta zo birthday celebration din Owais ta kira ni a waya har ta fa
a min bata da lafiya tana fama da zazzabi, bayan na yi mata sannu da jiki na ce mata zan shigo in duba ta, mutumin da baida koshin lafiya, ina ya ga karfin da zai iya fa
a da babbar mace irin hajiya Saratu?"
Yakamata kuyi bincike da kyau, Hajjaty matsoraciya ce bata da karfi, wallahi bata iya fada ba ko na baki..."
Maganar Turai ta dan sanya shi kokwanto acikin zuciyar shi, ya ce mata in sha Allah za su yi bincike idan ma bata da sa hannu za su gano ne.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta kuma tambayar shi ina pravin?

Ya akai bai zo ba?

Ko dai baisan me ya faru da Saratu bane?"
Ya ce mata pravin tun jiya bai dawo gidan ba, sun kikkira layinsa a kashe, amma suna sa ran zai neme su ne!

" Shiru ta yi jimm kafin ta ce Allah ya sa ya yi tunanin dawowa ko dan saboda twins din sa, watakil in suka gan shi hankalinsu ya kwanta, saboda sun bata tausayi jiya, ko ruwa basu sha ba, a zaune suka kwana, shiru kawai ya yi bai tanka mata ba.

Kafin tafiyar su, saida suka sa kitchen staff suka shiryama su twins abinci kuma suka tursasa masu dole su ka ci abincin, sannan su ka yi wanka, kowan nan su ya sauya kayan jikin shi da wanda Hajiya malika tasa aka kawo masu.
Chapter 56 · 0% Book details