← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 201

Sashe 62

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni ina ji araina wani laifi ka aikata musu shiyasa ka gudu da ni, saboda hujjar daka bani bata gamsar da ni ba.."
Sunnar da kanshi kasa ya yi, jikin shi ya yi sanyi lakwas, baisan ya zai yi ba, ya jefa rayuwarsu a cikin bala'e da masifa, ya yi danasani tafi sau a
irga, yana matukar jin kunyar Hajjaty, yana jin nauyin tasan miyagun laifukan da ya aikata wa'iyazubillah!!

Bata
ara yin magana ba, ta juya ta nufi kofar fita da sauri ya bi bayanta, shigowa cikin dakin ta yi, jikinta na kerma ta nufi bedside drawer ta soma kwashe magungunanta tana jefa su cikin dustbin din dakin, shigowa ya yi da sauri ya dam
i hannayenta, kokoyi suka kama yi..

"Pls ki saurare ni, zanyi maki bayani, ki daina zubar da maganinki, da tsada na siye su saboda lafiyarki..."
Wani kallo ta wurga masa, "Ban damu ba Pravin, bana son lafiyar tawa, nafi son na mutu, saboda wanda na yarda da shi yana neman ya karya min zuciyata..."
Bai san sa'adda hawaye suka wanke fuskar shi ba, duk yadda ya so ya dakatar da ita abun ya ci tura,
arfi yasa gurin
aukarta
ungurugum ya kwantar da ita kan gadon, ta dinga kuka tana bubbuga mattress da hannayenta, bin ta ya yi saman gadon ya janyota jikinshi tana turjewa, ya rungume ta kan
irjin shi, duk yadda ta kai ga jin haushin shi da ya yi mata hakan sai da ta ji sassaucin damuwarta.

Cikin sanyin murya ta ce, "Pravin dan Allah ka fadamin meyasa ka gudu da ni?

Meyasa ka bar Obie estate?

Wani laifi ka aikata?

Kada ka yi min karya Pravin, babu sirri atsakanin mu, kasan bani da kowa in ba kai ba, kaine majinginata,
ashin bayana, bana so ka ci amanar yardar da na yi maka Pravin, dan Allah ka fa
amin na yi maka alkawarin zan rufa maka asiri kuma zan taya ka neman mafita.."
wani irin tsantsar sonta da tausayinta ne ya mamaye zuciyar shi, tsoma yatsun hannayensa ya yi a cikin sumar ta yadinga caku
a gashinta kamar yana mata susa,
Cikin sanyin murya ya ce, "Ki yi hakuri na boye maki ne saboda bana so na
aga maki hankali, amma gaskiyar abun da ya faru, Hajiya Saratu ta gano ina zuwa dakin ki, harma in kwana, bayan mun dawo an fara shirye shiryen family meeting, sai na shiga
akinta don in canza kayan dake a jikina, ina kokarin cire riga na jiyo muryarta a cikin toilet tana yin waya
asa
asa kamar bata so aji, saina lallaba na je bakin
ofar dakin na yi mata la6e
a nan na ji tana fa
in wallahi bazata sa6u ba, dama ta jima tana zargin kin asirce mata miji saboda yadda kike gayu, wallahi ba zata
yale ki ba, sai ta kashe ki da poison..."
Zare ido Hajjaty ta yi,
Pravin ya sha mur ya ci gaba da zabga mata
arya, "Da na ji haka gabana na faduwa na fara tunanin me yakamata in yi saboda nasan mugun halinta na kishi wlh tsaf zata kashe ki, ni banma san wani munafukin bane ya kulla maki makirci, na so inji da wa ta ke yin wayar, ina jin alamun ta gama yin wayar na ma fasa canza kayan, jiki na na kerma na baro dakin nata, na nufo
akin ki don in fa
a maki abunda ke faruwa, shigowata keda wuya ina kokarin in tashe ki na ganki a kudundune cikin bargo, kwatsam na jiyo muryar hajiya Saratu daga waje tana tambayar maids ina ne
akin ki? da sauri na la6e bayan labule ina jira inga me za ta yi maki, tana shigowa
akin ta nufi gadonki hannunta ru
e da poison..."
Dafe kirji Hajjaty ta yi jikinta ya hau 6ari, da
i ya ji acikin ranshi ganin ta fara yarda da maganarshi..

"Ji nayi bazan iya bari ta cutar dake ba saboda nasan ba imani gare ta ba, saboda tashin hankali banma san lokacin dana yi wuff na fito daga bayan labulen ba tana jin motsi na ta juyo mu ka yi ido biyu, ta ware baki zata fasa
ara na sha
eta tana ta sambatu tana fa
in maciya amana, zarginta ya tabbata akanmu, wlh saita kashe mu, da na ga ta turje ta
i saurarena kawai saina sumar da ita, na sungumeki na bar estate
in da ke, don nasan muddin ta farka kwanan mu ya
are..."
Cike da damuwa Hajjaty ta ce, "Banji dadi ba, amma koma wanene ya
ulla mana makirci Allah ya isa tsakanin mu da shi, mutane basu tsaron Allah.

Amma hajiya Saratu bai kamata tana daukar zigar wani ba, ko da ya ke dama ta tsaneni, tasha fa
amin saita raba ni da gidan ubanta, amma bansan tsanar da ta yi mini ta kai har haka ba, kuma dama kwanaki ko hanya bata son ha
awa da ni, abinci ma indai ni na dafa bata cin shi.."
Pravin ya ce, "Hmmm,
an adam fa ba abun yarda bane, indai ka biyewa mutane zasu kaika su baro ka, kuma dama bata sonki ta sha saka ki kuka, ta
untata maki saboda tana jin haushin zaman da kike yi agidansu, ni kaina da nake mijinta bata
yaleni ba, kullum saita goranta mini saboda ina zaune gidan ubanta.

Saratu bata da wayau, sakarya ce, kwata kwata bata da halin kirki, zaman hakuri kawai nake yi da ita, amma ni kaina ba sona ta ke yi ba, wahalar da ni ta ke yi, taita juyani son ranta." Yana magana yana yamutsa fuska,
"Amma pravin meya kamata mu yi yanzu?

Ni ina ga kawai mu je mu basu ha
uri mu fa
a masu gaskiya, In ba haka ba za su mana kallon mutanan banza kuma maciya amana.."
Waro idanunsa ya yi, "Ke!

Kina hauka?

Tab lallai, ay wlh muddin muka koma estate din nan sai sun hukunta mu, sai ka ce kin manta irin yadda baba Obie da yayyanta suke ji da ita?

"Pravin, koma me zai faru mu ne masu laifi, mutanan nan sun yi mana hallaci, sun yarda da mu, tsawon shekara da shekaru muna rayuwa acikin su basu ta6a gudun mu ba, amma mu muka
i fada masu ala
ar dake atsakaninmu, bamu kyauta ba, kuma nasan zasu fahimce mu in har mu ka je muka basu ha
uri muka kuma fa
a masu akwai aure a tsakanin mu za su yafe mana, koda hajiya Saratun bata yarda ba nasan za su yi
arin sasanta mu da ita, tun da su din mutanan kirki ne suna da hankali da kuma tausayi...."
Bata
are maganar ba ya tari numfashinta da cewa, "Hmmm, na lura har yanzu baki san halin hajiya Saratu ba, nasan mutanan kirki ne amma wlh akan Saratu zasu iya komai, kin manta labarin dana baki lokacin da ta zo da ni don inga danginta?
iri
iri suka nuna basu sona sun tsaneni saboda ni ba jinsin su bane, kuma bani da asali da arziki irin nasu, a lokacin ba don baba Obie ya goya mini baya ba ai da basu bani auranta ba..."
Dafe kai ta yi da hannu
aya, "Me zai hana mu tuntu6i baban toh? nasan zai taimaka."
"Har yanzu kin
i fahimtata, nifa bazan ci gaba da zama
asar nan ba, saboda hajiya Saratu ba zata raga mana ba,
wara mu tattara yanamu yanamu mu tafi, don yanzu haka nemanmu suke yi ruwa ajallo don su hukunta mu.."
Maganarsa ta
aga hankalinta, da damuwa ta ce, "Pravin meya kawo maganar barin
asa?

Ka san me kake fa
a kuwa?

Ina zaka kai
an naka da matarka? kaima kasan wannan bamai yiwu bane, kawai saboda asirinmu ya tonu sai mu gudu kamar wa
anda suka aikata wani mugun laifi...?"
dafe kanshi yayi da hannu
aya baisan tayaya zai shawo kanta ba..

"Pravin ka daina wannan maganar, ba zan ta6a baka shawarar ka tafi ka bar iyalinka ba, bamu aikata laifin daya kai har mu gudu ba, kawai kuskuren mu shine
arya da muka yi masu tun farko muka boye masu gaskiya, in har muka nemi yafiyarsu bayan mun fa
a musu komai wlh zasu yafe mana Pravin, mun sha
u da mutanan nan, mun saba da zama cikinsu, sun zama kamar danginmu da muka rasa!

Sun
auki nauyin komai namu Pravin, wlh idan muka gudu baza su ji dadi ba, zasu ga kamar dama da wata manufa muke atare da su shiyasa bayan mun samu abun da muke so muka tafi, kai baka tunanin halin da
anka da matarka za su shiga?

Wai kuwa Pravin anya kana jin kanka amatsayin ubansu..."
bata
are magabar ba ya toshe mata bakinta da yatsan shi..

Ta rasa meyasa take ji aranta kamar pravin ba gaskiya ya fada mata ba!

Saboda yanayinsa da kuma maganganunsa abun tuhuma ne!

Kawai saboda
aramin laifin da bai kai ya kawo ba sai ya gudu ya bar iyalinsa?

Ganin kamar ta fara
ago shi ya sa shi saurin daidaita nutsuwarshi cikin sanyin murya ya ce, "Na gane kuskurena, kawai bana so ta cutar dake ne shiyasa na yi wannan maganar, amma ba har cikin raina ba, ni ba zan iya tafiya na bar iyalina ba, banma san na fada ba, ki yi ha
uri idan na 6ata maki rai.." Ajiyar zuciya ta sauke, "Yanzu da yaushe zamu je estate din mu nemi yafiyarsu?"
"Me zai hana mu bari sai an kwana biyu, lokacin da suka yi kewarmu, koma suka neme mu da kansu don su ji ba'asi sai mu je mu fa
a masu gaskiya,..."
ta aminta da maganarsa saboda a halin yanzu tasan jiran su suke yi.

"Na yarda, amma tayaya zasu neme mu?
Chapter 62 · 0% Book details