← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 197

Sashe 93

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tace tau muje sai na baki sakon daga haka suka shiga bedroom din “hibba tace dan girman Allah aydarh ki daure ki ding asha saboda kalan wahalan da aka sha kafin kayan nan su karaso daga can nijer din “Aydarh ta gyada kai tace in sha Allah hibba tace promise don bawai yarda nayi dake ba ,aydarh tace Allah I promise zan dinga sha hibba tace tau shknn aydarh tace thank you auntie Allah yasauke ki lapia hibba tayi murmushi tace Ameen aydarh kuma Allah yakawo muku masu Albarka aydarh batace komai ba tayi shiru daga bakin kofa sukaji ana knocking malik yace ki dauko takalmin ki sai mu fita tareda su kawai mu karbo sako aydarh tace ohk”kafin ta bude wardrobe tasaka ledan da hibba ta bata “suka fito tare rufe gidansu kayi a bakin hanya suka samu keke hibba tayiwa aydarh waving hannu tace sai mun hadu a airport mu zamu raka ku aydarh tace to auntie “kasancewan anan bakin hanyar ke da babban shagon boxes da textiles wani haddan box yasiya masu kwara uku sunyi kyau bana wasa ba yabiya kudin suka wuce gida this time a keke suka dawo,shi ya dauke kaff box ukun suka shiga gida bedroom yakai su kafin yakalleta yayi kasa da murya yace ko hakanan akayi takeaway din baza’a ci abincin ba?tayi murmushi tace acici “kawai tayi gaba ya bita da ido har ta shige kitchen din kafin ya zauna parlor murmushi dai yaki barin fuskan sa yadinga bin parlor da kallo hadda daga kai sama “he will surely missed this house he will surely miss kano bai taba tunanin sake samun wani farincikin ba tun bayan tahowar su daga adamawa bas ai gashi abubuwan dasuka faru dashi na alkhairi a kano ko dawasa baitaba ko da dreaming hakan ba “sai gashi cikin abunda bai fi one year rayuwarsa ta juya yashafa kansa yayi yana tunanin plan dinsa dakuma rayuwarsa a Washington lumshe ido yayi ya bude yace Alhamdulilah “ahankali ta bude kofan kitchen din tafito hannunta rike da plate din data zuba grilled meat din sai dayan kuma da spoons da fork da kuma cups dasauri ya taso yarage mata wasu kayan hannun nata kafin ya ajiye kan carpet itama nan ta ajiye kafin ta juya kitchen din yabi bayanta a tare suka karasa fiddo pizza da drink suka zauna “ya kalleta yace kinyi kyau tawara ido tana kallon jikinta tun rigan data saka dazu ne white sai kanta ma abude babu ko hula kitson nan kaman an zana ya rabbil alameen “murmushi kawai tayi kafin tafara mashi cutting naman hannunta yakama suka yi cutting a tare kafin yafara feeding dinsu tana masa fira kadan kadan “shi dai yashagala kallonta kawai yana bada naman shi ko ci ma bayayi can ta lura ahankali ta taba sa tace what’s wrong? Ya girgiza kai yace babu komai gashi yacigaba da bata naman can dai ta dauka shima ta kai masa baki Wallahi hadda hannunta ya hada “tayi yar kara duk da gangan ya ciza din kadan “ ta tura masa baki tace shine zaka hada da hannu na dazu daman budurwa ka ta dagan nidai nagaji both the girlfriend and the boyfriend are against me “malik yayi shiru yace sorry cuddle bug dawasa fa nayi aydarh dai ki kallansa “ahankali yajawo ta yace ni dai ki cigaba dabani am hungry fa “ sai sannan tace to idan kasake cizawa bazan sake baka bay ace yeah naji “ahaka ta dinga feeding dinsa har yakarasa grilled meat din kafin yajawo pizza shima sun ci kusan rabi kafin ahankali ta mike tace sir cikina zai fashe malik yayi murmushi yace ai naga kinyi kokari ma yau kin ci abincin dayawa tayi yar dariya tace so nake na fika kiba ai “malik yawara ido yace kai haba?ta gyada masa kai yace tau zo ki ga wani abu tace me?yace kedai ki zo kawai “ahankali yasa hannu yajata jikinsa “ya lumshe ido yana placing hannunsa a cikinta yana shafawa tayi lamo tana sauraron sa can yacigaba da zarce hannun har kan maranta dasauri ta rike masa hannu tana girgiza masa kai tace stop “yayi shiru duk jikinsa ya mace kawai yadaga ta suka wuce bedroom “kan katifan ya ajiyeta kaman wata yar baby kafin ya kwanta a jikinta duk da bai sakar mata nauyi bas ai datayi yar kara “daran sai da malik ya gama ruda aydarh kafin ya rabo da ita kuka ta dinga masa kaman zaa zare mata rai “duk bawai ko yayi attempting disvirgin dinta ba “a jikinta dai ne kawa isai wurin daya manta ke bai taba bak o yayi wasa dashi “ko daya dawo daga sallan asuba tana cure kan prayer mat still carrying ya matsa kusa da ita yazare hijab din jikinta yasata a jikinsa yacigaba da Patting bayanta har dai yaga tasaki jiki dashi ahankali yamike yace bara nashirya manah kayan box saboda zamuje bankwana dasu iya da inna aydarh ta gyada masa kai kafin ta mike ahankali tace I will help you yayi murmushi yace Alright darl “ kayan suka jera a box kowa danashi karamin ne ya rage malik yayi kasa da murya yace tau ko mu hade inners din cikinsa kawai aydarh tace nawa dana ka?yace ehh tayi shiru kafin tace to “kaf brassiere dinta da pants yahade cikin box din sai yasaka boxers dinsa da singlet da few kayan dasuka rage “kafin yazage zip din yamikar da both the three akwatin “yakalle yace ko zaki koma bacci ta girgiza masa kai yace tau sauran kayan can su buckets dawani kayan kitchen kawai sai nasaka a fitan ma inna dashi tabayar kawai “Aydarh ta gyada masa kai yace ko muyi warming sauran naman can?tace to “sai dasuka gyara koi na na gidan suka mikar da duk abunda suka tarar nan kafin suka hade nasu waje daya da niyyar idan gari yakara haske malik yasa a fitan dasu a kai gidan inna “kaman yanda yafada warming nama sukayi kawai tahada musu tea suka yi breakfast wanka tashiga shima yashiga toilet din nan parlor.Bayan sun gama shiryawa already anfitan da kayan zuwa gidan inna yakalleta yace mu fara zuwa wajan iya muyi bankwana ba kafin mu dawo nan tace ohk “ sunyi kyau bana wasa ba farar shadda yasaka sabuwa dal Tabarakallah murmushi tayi kadan tana rage murya tace kayi kyau sosai kaman wani ango “shima murmushi yayi yace ai kin fi ni yin kyau pretty “tawara masa ido tace dagaske ya gyada mata kai taja cheeks dinsa tace mutafi kaga har twelve yanzu “Da murmushi iya ta tarbe su “rabiah na nan zaune sai fama kallon malik take kaman zata hadiye sa Wallahi aydarh don dai kawai wajan iya suka zo amma dasai tasa sun bar wajan saboda kallon da rabiah ke masa daurewa kawai tayi tana dai sauraron nasihar da iya keyi musu amma bawai tana fahimta ba kawai she is eager su tafi ji take kaman ta rufesa rabiah tabar ganinsa “ iya tace Allah yayi muku albarka abdoolmalik a rike gaskia in sha Allah zakuyi nasara a rayuwa ka rike yar uwarka “ka rike matarka Allah yabaku zaman lafiya “ malik yayi kasa da kai yace Ameen Ameen iya mungode Allah saka da alkhairi iya tayi murmushi tace Ameen abdool “kafin aydarh ma tayi kasa da kai tace angode iya Allah yakara girma “iya tace Ameen asiya Allah yamuku albarka a cigaba da biyayya asiya a cigaba da hakuri “Aydarh ta gyada kanta kawai malik yamike yace rabi’atu dasauri rabiah ta dago kanta tace naam yaya yace ki tura mun acct number ki zan Saka ma iya sako “Aydarh takallesa ohh tana number tasa kenan “ma dahar zai ce ta tura masa mikewa tayi ahankali itama kafin tace iya bara nashiga wajan auntie Hibba inna tace anya kam basa nan sunje can asibiti tare ko wani test zaayi mata amma ai naji suna cewa tare zaku tafi can filin jirgin malik ya gyada kai yace ehh iya “yanayin aydarh yakalla dasauri yace “ohh namanta samun yafada yana mika mata wayarsa aydarh tasa hannu ta karbi wayan kafin tamikawa rabiah acct number ta rubuta kafin tamika mata wayan karba yayi nan take yayi mata transfer 100k kafin yasaka wayan ajihu ya sukunyan da kansa yace iya zamu tafi ubangiji yasaka muku da alkhairi Allah yabar zumunci ana haka rabiah tace iya yayah ya tura dubu dari iya “iya tace kai haba abdool hadda wani wahala haka Allah yayi muku albarka “malik yace Ameen Ameen har kofa gida iya suka rakasu tare da rabiah “bayan iya takoma saboda hadda dan kukanta sabo “malik ma duk sai yaji wani kala aydarh ma haka “rabiah ta saukar da kanta tace “dan Allah kiyi hakuri da duk abunda nayi muku Wallahi ba laifi nabane shidai malik ko kallonta baiyi ba aydarh ta girgiza kai tace babu komai rabiah,rabiah tace nagode Allah yasaka da alkhairi “Allah yakara baku zaman lafiya aydarh tayi murmushi tace Ameen kafin sukayi sallama rabiah ma ta koma sukuma suka shiga keke sai dasuka yi salla saboda har kusan 1:30kafin suka wuce gidan inna “suna shiga tana zaune kan tabarma “ansha dinkin lace sabo fill ga samira datayi ma malik kwadon zogale a gabanta kusa da ita yazauna aydarh ta ta zauna daga dayan side din inna suna zama inna takama harbar zane tafashe da kuka cikinsu babu wanda ya iya mata magana sai da tayi mai isar ta kafin ta tsagaita tace “yanzu shknn shi daman sabo haka yake “inalilahi waina illahil rajiun shknn yanzu audu tafiya zakayi kabarni wayyo Allahna “malik yayi murmushi aydarh kam juyawa tayi tana dariya saboda bakaramin dariya inna tabata ba tama yi tunanin wani abun akayi mata “malik yace tau waya gaya miki bazan dawo ba?inna tasaki baki tace yoo kodai ni yar iskace ai bazan taba yarda zaka dawo ba wanene wanda zai bar kasar nan yace kuma zai dawo shknn masifa ta sauka dan wajan audu kawai nake samun rahama yanzu shknn anbar ni da wannan tsohuwar macan ta kasheni da bakin ciki sai ta sake fashewa da kuka “malik yace kinga kiyi hakuri ni dana son kina zuwa babu abunda zai hana nasa ayi miki visa mutafi tare!aydarh tace yanzu ma za’a iya miki inna sai kema kizo
Chapter 93 · 0% Book details