← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 197

Sashe 61

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

iya wankin?ta dago tana kallonsa kafin tace erh yace kinyi kokari tayi murmushi kallonta yake ko kiftawa babu yace bana son asaka hakuri amma your own looks cute tayi murmushi tace thank you hakurin gwal din yasake kalla wanda yazauna mata dass a jerin white teeths dinsan sai shine shine yake sau dayawa idan tayi dariya yana so yayi magana shiru kawai yake can dai suka karasa nata ya kwasa ya wuce can bayan part dinsu zai shanya shanya su yayi kafin yadawo yana dawowan yace tau kiji ki huta sai na karasa nawa ko? Ta girgiza tana wasa da foam din dake cikin bucket dinta tace ah’ah zanyi “yayi shiru kafin yace okay wankin suka cigaba dayi babu wanda ke magana a cikinsu kowa da abunda yake ransa sallama akayi suka amsa dr hafsa ce tsaye suna hada ido tayi murmushi tace yau wankin kauna ake tau sannunku malik na murmushi ya amsa gaisuwan datake masa kafin Aydarh tace welcome auntie ina kwana? Dr hafsa tace lafiya alhamdulilah ya gida?aydarh tace lapia lau “kafin ta mike tana wanke hannunta tace ki shigo Auntie dr hafsa tace aaa kawai tunda mun gaisa bara na wuce ai aiki kuke, malik yace no sai fa kin shiga ai mun kusa gama ku shiga kawai nakarasa aydarh ta bude kofan babu yanda dr hafsa zata iya haka tashiga anan parlor suka zauna Aydarh nasake tambayan dr hafsa ya jikinta ina inna? Dr hafsat ace naji sauki sosai Aydarh ina na nan lafiya tama tafi kasuwa maybe yau ma ku ganta saboda naji tana cewa yau bazata kwana bata shigo ba “kwana biyu bata ga audu ba kila ke kika hanasa zuwa Aydarh tabude ido sosai kafin tace ah’ah auntie Wallahi bani bace,banma san yadaina zuwa ba tayi hakuri “dr hafsa tace ahtau idan tazo dai sai kuyi mata bayanin komai kenan Aydarh ta mike tana cewa Allah yakawo ta lapia shiga tayi kitchen ta fito hannunta rike da plate sai pure water biyu akai ta ajiye gaban dr hafsa,dr hafsa nayi mata sannu ta dauki ruwa daya tafasa tana sha,.hibba tayi shiru kafin tace tau yanzu wa zakayi wa maganan kasan yarda zaka samu shi Doctor? Dr ibrahim yayi shiru kafin yace akwai wani yaron gidansa abokina na ne munyi dinki shago daya kafin yasamu aiki a gidansa nikuma nakoma clinic duk karshan wata yake zuwa kano saboda Doctor usaman yasa mar masa aiki a can wani babban private hospital a lagos in sha Allah idan yazo komai yake nan nayi tunani abunyi,hibba ta gyada kai tace nan da kwana sha daya kenan? Dr ibrahim ya gyada kai tace tau Allah yakaimu lafiya asa munada rabo baki daya dr ibrahim yace Ameen wifey “kafin yawani marairaice fuska yace massage please,batace komai ba domin tasan abunda yake nufi hannunsa kawai takama suka tashi, anan bedroom suka zauna kan gado hibba ta cigaba dayin ta mijinta, kafin kuma suyi tafiya can.bilki ta dinga kallon rabiah ko dauke ido babu batace komai ba rabiah tace kiji wani iskanci niga banza sai surutu nake kinyi mun shiru bilki tace aaaaa wai ai jirana nake kigama tunda na lura kaman kin fara samun damuwa a kwalwa,rabiah tayi wani zagi tace ban ma gane ba mikike nufi ne?bilki tace rabiah banda mu bamu san ciwon kanmu ba kawa isai muje mu kama masa mata mu daka tsabar ke baki da kugu ke kanki dakikayi maganar kinji abun ya hau daidai fisabillahi?rabiah tayi shiru tana kallonta,kafin bilki tacigaba dacewa yoo ko shi bai ce manah komai yayah ibrahim bazai ya hallaka mu ba har lahira “balle wannan bawan Allah da idan kika yana kallon matar sa kamar ya afka mata jikin jamaa ke kalan jikinta ma yayi maki kama da jikin da ake duka?tau idan baki da lissafi ni inda shi babu ruwana kawai kibari mu samu kudi sai a koma wajan malam muga abunda Allah zaiyi,rabiah dai tayi shiru amma bakin ciki kamar ya kasheta so tayi suje su chanza mata kama ko kila ko sau dayane ya kalli ita rabiah da idonsa ko sau dayane tunda duk wani magani data karbo baya aiki har kudinta ma yakare yanzu haka so take tahada su koma amma abun ya faskara shiyasa take ganin shine mafita hakan. Bilki tace tau Wallahi babu ruwana a wannan hau din idan kingani a lahira fa kaine akai wooo ni shegiya kina ganin mutane jiki duk Hutu bakisan daga inda suke ba, kice zaki haye musu billahi babu ruwana, rabiah dai tayi shiru tana sauraron bilki har tayi shiru kafin tace tau ni Wallahi wayata zan siyar na koma wajan madawaki asan abun yi, bilki tace tau shknn ai yafi dai kafin ta mike tana daukar mayafinta tace rakani wajan anty hibba mu gaisa nawuce gida babah tace kar najima rabiah ta mike tace mutafi Allah yasa yayan bai nan kinsa sa mayyanta ne Wallahi ko da yaushe ya baibaye da ita Wallahi bilki tayi dariya tace halinsa guda da abokin nasa kenan rabiah tace uhm Allah ya kyauta bilki Tace Ameen , Sallama suka hibba ta amsa musu shiga sukayi tana nan zaune parlor tana kallo tana ganin su tayi murmushi tace sannunku da zuwa bilki tace yauwa anty ina wuni? Hibba tace lafiya lau ya gida? Bilki tawashe baki tace lafiya lau, rabiah ma tagaishe ta amsa kafin ta mike ta shiga kitchen zata kawo musu ruwa bilki ta kalli rabiah tace ashe matar nan da kyaunta har kiba ma tayi nagani rabiah dai ta tabe baki tac eke kullun sai kin gama yabon mutane ina dalili kam tafada tana tsaki ruwa ta kawo musu sai chin chin batayi girki bat ace su zauna ta daura ko indomie bilki tace aaaa sauri take idan tadawo zata ci wata rana hibbah tace Allah yakaimu ruwan suk asha da chin chin sama sama sukayi fira domin hibba sam bata son rawan kan yaran, har bakin kofa ta rako su sukayi sallama ta koma ciki. Kallonsa take har yagama kafin tace to ka kwanta Allah zanyi fa nace maka, malik dai sai kallonta yake kafin yace nace miki ciwon kan kadan ne saboda nashiga rana ne,tayi shiru bace masa komai ba ya mike,yace muje kitchen din suka shiga yayi mata blending, kayan miyan duk da daurewa kawai yake ji yake kaman zaiyi fever tana lura da yarda yake ta ciza lips dinsa ,can tace ka fita zan karasa ya girgiza kai kawai yacigaba da abunda yakeyi, bata sake magana bai ta ta cigaba da yanka vegetables din, kasa daurewa yayi kawai yamike yafice daga kitchen din nan parlor ya dawo ya kwanta kan carpet kansa na wani irin sarawa rufe idonsa kawai yayi yana sauraron yarda yake kyarma,kaman kar ta fita sai kuma ta wanke hannunta ahankali tasa karamin towel ta tsane hannu “ fitowa tayi yana kallonsa ko dauke ido babu karasawa tayi kusa dashi kafin ta kai hannu ta a neck dinsa temperature dinsa yayi high sosai dasauri ta dauke hannunta gabanta nafaduwa kafin tace,jikin yayi zafi sir daman baka da lapia? Girgiza kai yayi bai iya ce mata komai ba mikewa tayi ta nufi bedroom very clean duvet dinta ,ta dauko masa tadawo ta yafa masa, har kai ta rufe masa tama rasa mi zatace masa can tace sannu, tazuba masa ido kawai hankalinta bakaramin tashi yayi ba,tana tunani ko ta kira dr ibrahim can tace sir ka kira Doctor manah hannu yasa cike da dauriya yabude duvet din yace kije ki karasa girkin zan kira sa bata tashi ba kuma bata daina kallonsa ba, can dai ta mike ta koma kitchen din ta cigaba da girkin amma hankalinta na wajansa, sharp sharp takarasa ta fito tasame sa,zuwa yanzu ya daina zufan sai ajiyan zuciya dake saukewa kadan kadan alaman yayi bacci bude duvet din tayi ganin he is sweating yasata bude duvet din baki daya bedroom takoma ta dauko tissue tadawo parlor gently ta matsa kusa dashi ta warwari tissue din tana goge masa goshin dan bude idonsa yayi yakalleta kafin yarufe ahankali , sai da ta goge masa tass kafin ta koma bedroom din wanka tashiga few minutes tadauka a cikin toilet din kafin tafito vaseline kawai tashafa sai perfume tasaka kaya ta dawo nan Parlor ta zauna can karshan carpet daga ka ganta kasan bata da nutsuwa, ganin kaman yana dan motsi yasata matsawa kusa dashi jin alaman ta kusa dashi ,yabude duvet dinta ahankali yace kingama?ta gyada masa kai yace kinci? Ta girgiza masa kai bai ce komai ba yadauko kansa dake ciwo sosai kaman zai fadi ya daura a laps dinta Wallahi malik ji yayi kaman an daura sa a aljannan duniya wani irin ajiyan zuciya yasauke nutsuwa na baibaye jikinsa, ganin yarda yayi din yasata jin gabanta yafadi duk ta rude jin ya kwantar da kansa a cinyan ta yakure kan wajan cikin kaman zai mai kan a cikinta,ahankali yace miyasa baki ci ba?muryanta na rawa kaman zatayi kuka Tace nakoshi bai ce komai ba ya lumshe idonsa shiru cikinsu babu wanda yasake magana kusan 20mins suna ahaka kafin ahankali yamike taga ya nufi toilet yana shiga tamike itama ta wuce bedroom alwalla tayi itama ta kabara sallan la’asar ,bai ji masallaci ba saboda bazai iya ba anan gida yayi sallarnshi nan kana bun sallan ya zauna bai tashi bah, tana fito tagansa zaune bata ce masa komai ba ta dauke ido ta shiga kitchen warmer ta dauko da plates sai spoon da serving spoon ta ajiye nan gefen sa kafin takoma ta dauko ruwa pure water a kan plate shidai bai ce komai bas ai faman kallonta yake ko kiftawa babu,bude warmer tayi serving dinsa abincin kadan badayawa ba ta tura masa gabansa abincin ya kala kafin yasa spoon baya son ya nuna mata bazai iya ci ba, Ahankali yake cin abincin ita dai bata zuba bas ai kallon wuri daya take girgiza kai yayi kafin ya ture abincin yana kallonta murya can kasa yace mata bazaki ci abinci ba ta girgiza kai tace zan ci yace tau sa k ici yafada yana mika mata spoon tareda tura plate din dake gabansa tsakiya,spoon din tasa tafara ci kafin shima yasa atare suka cid uk da bai dayawa amma babu wanda yakara cikin su ruwan ya sha
Chapter 61 · 0% Book details