Sashe 19
Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
waccan dayar balarabiyar ita bata da mai so ne komai? Allah na tuba tunda nasanta ban taba jin labarin wani na neman auranta ba gaskia, mai aikin tace wacce balarabiyar ? Hajajju ta juya ta juyo Kamar mai gudun wani ya ganta tace waccan abun manah watake yauwa rufaidarh, “mai aikin ta girgiza kai tace aaa mama tanada masu so sosai amma kila ita ce dai bata bada fuska”hajajju tayi shiru can kuma tace kai kuji rubabba yoo Allah na tuba bata ga ita yar uwar ba ma da auranta kuma tafita komai ma,amma sai ita tau nidai ba ruwana bara nakama bakina nayi shiru kingan ni nan babu abunda yashafe ni da rayuwar mutune, ni ko maganar mutane bana son ana mun, shiyasa kullun nake zamana lapia,kema ga shawara ki kama bakinki ba ruwanki da maganar bil’adama “ ta sake kasa da murya tace kinga habibu duk cikin mu shine kawai ba rubabbe ba da kudinshi tau sai ni din nan dakika gani tsaye a gabanki famelin mu duk sun yaye sun rasu daga ni sai wata mata da muke uwa daya uba daya muka rage sai kuma ibrahin da ya’yanshi “ ta gyara tsayuwar ta tace wai fa shine dan tsoron Allah da kaunar ma’aiki da yanzu ba ‘ayi za a hadani da jafa’I wai wani abu na koma kuturun gidan matar da zama “ita a wa?ita ame? Da zasu hadani da zama waje daya da ita babu iskan kirki gidan ba kai babu kugu haka take rayuwa ba da ba jikah daman mu famelin mu munada tsari bama sakin jiki mu dinga zazaga yara kamar tsuma shiyasa kikaga bamu da yawa ma “ ita dai mai aikin har ta gaji da sauraron hajajju she see no reason da zata dinga mata wannan zubar, bata ce mata komai ba har tayi shiru “sannan tace tau Allah ya kyauta mama”hajajju tace haram haram badani ba aikata wannan baqin kantameman zunubin miye wani mama, sau biyu ina zuwa makkah fa wanda a famelin mu bayan ni sai habibu da wannan matar tasa dakuma diyarsu wanda a halin yanzu bamu san inda suke ba, still dai maid din she is eager hajajju tafita takarasa aikinta tun tana bata dariya har labarin yafara fita kanta nan fa take ce mata ita bata maganar mutane amma tun dazu take bata labarin abunda bai shafe ta ba “ can wani dabara ya fado mata tace am hajiya mi kike bukata na kumallo “hajajju ta washe baki tace daman tun jiya rabo na da sa ma cikina wani abu tashin hankali ya hanani sakat billahi “maid din tace Allah sarki, hajajju tace shayi zaki hadaman ki suya dankali da kwai takwas sai sabon biredi da farfesu yanzu ina jiranki ,maid din tace tau shknn hajiya dana gama sai na kawo maki a nan dining hajajju bata ce komai ba ta juya tafita. Doctor hafsa ta kalli malik tace ya jikin nata tasamu bacci kuwa? Sai da malik ya sace kallon aydarh dake zaune ta rabe waje guda kamar marainiya kallo daya zakayi mata kaga alamar tana cikin damuwa sosai she is helpless and she’s alone,can ya kalli dr hafsa yace jiki da sauki alhamdulilah amma ina ga gaskia batayi bacci ba, duk maganar da suke aydarh na jinsu ko kallo basu ishe ta ba,ahankali dr hafsa ta taka kusa da ita tace good morning ma’am how was your body? Kamar bazata magana ba kamar batagane da yaran da dr hafsa ke tambayan ta ba , bata motsa ba kuma bata dago kanta ba jikinta na cure waje daya daidai numfashinta ahankali take shakar sa take kuma fidda shi, dr hafsa dake kallonta ko kiftawa babu bata gaji ba tasake maimaita tambayar da take mata, kusan 2mins lokacin dakin yayi shiru malik kau bakin ciki kamar ya kashe shi ji yake kamar ya rufeta da duka ganin irin yarda ta maida dr hafsa kamar wata shashasha tana tambayar ta tayi mata shiru, dr hafsa tayi murmushi ta girgiza kai tace Allah yakara sauki bara na hada mata ruwa tayi wanka malik yace tau nagode,daga haka dr hafsa ta fita zata dago flask din ruwan zafi data sa aka kawo mata daga gida “kallo daya yayi mata ya dauke idonshi sannan ya mike tsaye baya son raini baya kuma wulakanta mutane duk halin san e rashin son magana amma idan har yazo wajan fagen kulawa yana nuna juriya da hakuri akan kowace tambaya dakuma amsarta ita amana ce wajan shi da kuma alaqar dake tsakanin su na yan uwa bayajin zai bar tarbiyyarta da rayuwarta su cigaba da wanzuwa ahaka ba, yana cikin jerin mutanan masu saurin karantar halin dan adam tsaf ya karanci girman kai izza izgili dakuma raini a tattare da ita, yarda yayi alkawarin karbar wannan kaddarar ahaka yayi alkawarin rike amanar da hallita mafi daraja da ki’ma a idonshi mafi koluluwar soyayyya a idonshi ta basa, bayajin sonta ko diko a ranshi kwata kwata halinta baya cikin jerin matan dayake son zama dasu matsayin matar aure tanada amfani da kyau wajan raina duk wani bil’adam shikuma bazai dauki hakan bah, wata zuciya tace masa tau wannan ai ba aure bane kamar kowane! “Cikin tsananin tsara gida ya kalle ta yace,she is not your mate she’s older than you so don’t take for granted, yasa kai yafice,kallonshi take ko janye ido babu batasan miyasa ba take wani jin shakku mai kama da tsoro idan yayi mata magana ba har faduwa gabanta keyi idan yayi mata magana wasu irin kwalla taji masu masifan zafi na bin kuncinta ta she can’t hold it but cry, kuka tafa rerawa kamar karamar yarinya har cikin ranta take jin babu wanda yayi saura a rayuwarta wani irin zafin oum da abba take ji har cikin ranta ko tuno bata son yi (subhanallah) Dr hafsa ce tashigo tasame aydarh na kuka kallonta tayi ahankali tayi dropping flask din kan med-drower ,kallonta takeyi batasan abunda zata ce mata saboda bata son kan mi take kukan bah almost five minutes suna haka ,sannan dr hafsa tace you are sick komai yafaru ki bar isai kinji sauki sannan ki ji da duk wani damun wanki for now dai keep anything aside recovered first,daga haka dr hafsa ta hada mata ruwa a toilet,sai da tayi wanka tass Doctor ta taimaka mata tashirya babu kayan da zata chanza illa rigar da ta kwana dashi hakan yasa ta jin kamar zatayi kuka dr hafsa na kula da ita bata ce mata komai ba tana son ta wanke mata pant din datacire ganin yayi stain amma gani take kamar batada wannan hurumin domin ta fuskanci daga matar har mijin bahagwaye ne gashi babu yarda zaayi ita aydarh ta wanke kasancewar da abu a hannunta, fitowa tayi daga toilet din tasame ta kwance ta rufe dukkan jikinta ruf, a reception ta iske malik da Doctor ibrahim cikin Fara’a suka gaisa sannan ya tambayeta ya mai jiki dasauki alhamdulilah Doctor ya aikin? Doctor ibrahim yace mata Alhamdulilah sannan yace tunda nazo sai ki tafi maybe yau ma ayi discharging dinsu tunda jikinta dasauki right?dr hafsa tayi murmushi tace ehh Alhamdulilah daman jira nake kazo sai na wuce nima,sai ta kalli malik tace ehen yallabai akwai abu a toilet nasaka a bucket akwai detergent sai ka wanke mata, then a nemo mata abunda zatace, tunda tafara magana malik bai ce komai ma sai da tagama sannan yace “thanks”.Bayan tafiyar dr hafsa suka cigaba da maganar dasuke shida dr ibrahim kan gidan dazasu zauna yana fada masa ai makwabta mane su da dr hafsa itama a anguwar take, Yau ma kamar jiya rabi’ah ce rike da food flask tasaha well ironed hijab dinta sai baza kamshin turaranta mai saukin kudi take,sai satar kallon malik tace bata taba ganin mutun mai kyaun shi ba,ko a indiyan flim din ma mamakin yarda yake da wannan mugun kwarjinin take bata ma iya kallonshi face face ko da ta gaishe sa ya amsa bata kallesa ba,taji yayan nata yace matar sa ce ba lafiya ita kam tana son ganin matar tasa taga ya take da har wannan mai zubin larabawan zai aureta,hakan yasa da dr ibrahim ke shirin karbar food flask din hannunta ya mikawa malik tayi karaf tace aaa yayah barsa kawai bara na shiga najiye sai na duba ta da jiki ma, dr ibrahim yace tau shknn, bude kofar dakin tayi ahankali tashiga “har numfashin ta sai dayayi barazanar daukewa, a kallo daya datayi ma aydarh Yah rabbil alameen, tau daga wace kasar suke tasamu kanta da wannan tambayar a zuciyarta,wani abu taji mai kama da bakin ciki hassada ya darso a ranta ganin aydarh da tayi ahankali ta ajiye food flask duk sai taji ta muzanta ashe karyar body structure suke ashe karyar kyau suke ashe karyar skin care suke ashe yar ubansu karyar body scent suke, warabul ka’aba she never imagined this type of beauty in the whole world? A gadon asibiti kenan fa tasamu zancan a zuciyarta bazata manta ba sun taba ganin hoton rigar jikin aydarh a wayar siyama kawarta itama a instagram ta gani wai three hundred k a lokacin mamaki suke wasu kalan kudi mutun zaiyi dazai siye wannan rigan sai yau taganshi jikin aydarh, ahankali tace mata ya jikin ki? Kallonta tayi lokaci daya taji wani irin bata ji haka ba kan dr hafsa da nurse saratu , sam ji tayi zuciyar ta tayi mata wani kala ganin rabi’ah ta bin ta da kallo kamar mayya, duk sun suna kallonta amma na rabi’ah yafi bata mata rai, rabi’ah tace daman yayah ne yace akawo maki breakfast, Akawo maki breakfast, aydarh ko kallon rabi’ah batayi ba balle tasa ran amsata “ rabi’ah dai natsaye ta zuba ma aydarh idon ta namata wani irin kallo, can tasake cewa magana nake maki malama ko baki jina ne ? cikin dan daga murya rabi’ah tayi maganar, Wani irin duba aydarh tayi ma rabi’ah cikin few seconds ta dauke kanta batace mata komai ba sai rufe ma fuskanta datayi da veil din kanta “ta bar rabi’ah nan tsaye kamar status “wani irin haushi ya kama rabi’ah watau yar iska ta mayarda da ita kenan marar lissafi da zata dinga mata magana tayi shiru “ juyawa rabi’ah tayi ta rufe kofar da