← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 197

Sashe 48

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta dinga bin rabiah da kallo kafin tace rabiah ,rabiah ta kalli dr hafsa kafin tace na’am ina wuni dr hafsa tace lafiya bilki ma ta gaisheta ta amsa ranta fal mamakin abunda yakawo rabiah gidan aydarh tace mutafi? Dr hafsa ta gyada kai kafin Aydarh ta koma bedroom ta dauko hijab din tabude wardrobe ta fiddo da 5k din da malik ya saka mata,Still basu tafi ba suna gani aydarh ta fito rabiah ta mike bilki ma haka rabiah tace sai anjima idan munyi waya da yayah malik din na fada masa nazo, dr hafsa najinta tayi shiru aydarh ma haka kafin tace sai anjima suka fita, suna fita bilki tace wai Allah billahi kawata banyi tunani aie ta kai haka ba rabiah tace hmm nima sai naga Wallahi kaman ta kara wani abu bilki tace ko ciki gareta?rabiah tace nima shi nake tunani kiji structure dinta Kamar cikin ta kamar bata sa masa abinci amma ji kugu tafiyan nan maybe ba da biyu takeyin ta Wallahi bilki tace bawani da biyu haka take ajin ta har yayi yawa ma wallahi ahh. Dr hafsa tace tau muna ta shiri baki tambayi yallabai ba, aydarh ta zaro ido tace ah’ah fa,dr hafsa takalleta tace aa fa mi?tayi kasa da kai tace zai hana ne,dr hafsa tayi murmushi tace ohhni aydarh kullun ke kaman yarinya idan yahana ai sai a hakura amma kin taba ganin inda mata tafita ba da izinin mijinta ba? Aydarh tayi shiru kafin dr hafsa ta fito wayarta daga cikin handbag dinta tace bara nakira maki shi sai ki tambaye sa, dialing number malik tayi har ya kusa katsewa kafin yadaga batayi magana ba ta mikawa aydarh wayar, sallama yayi aydarh ta amsa yana jin itace yanemi guri yazauna yayi shiru yana jiran tayi magana itama shiru tayi kafin takama gefen hijab dinta tana wasa da shi kafin tace ina wuni voice dinta very slow and innocent yace lafiya lau,tayi shiru kafin yace talk,ta tura baki kaman irin yana gabanta tace henna “jin abunda tace yasa shi maimaitawa dan ba wai yagane bane yace henna? Sai sannan ta gyada kai tayi kasa da murya gabanta na faduwa kar yace bazata je ba kaman waccan ranan tace salon zamuje nida auntie daga nan ayi manah lalle takarasa maganan kamar mai shirin kukan murmushi yayi kafin ya girgiza kai yace tau ba auntie ta mikawa dr hafsa wayan da tun dazu take kallon ikon Allah wannan shagwaba har ina su yan gayu masu kudi komai nasu daban ne,wayan ta karba tayi sallama kafin ta gaishe bata ji abunda yace ma dr hafsa ba kafin tace aa yallabai abarshi wallahi babu damuwa,sai kuma tayi shiru tace tau shknn Allah ya amfana,sai datayi dialing acct digits dinta kafin ta tura masa,ta kalli aydarh tace cewa yayi na tura masa acct number yasaka kudin salon din Aydarh tayi shiru kafin tace to 10k yasa dr ibrahim yatura masu saboda shi bai da acct number yanzu suna shigowa dr hafsa tace masha Allah ya tura 10k aydarh tace to mutafi kafin kuma ta mikawa dr hafsa kudin hannunta tace gashi ai nasa 15k ma bazai isa ba dr hafsa tawara ido tace kai ai 3k ma ya isa aydarh da mamaki tace 3k kuma?dr hafsa tace aaa ai mu daku ba daya bane mu na mu babu tsada kai ta girgiza kai batasan lokacin da tace 35k ne henna kadan a nails sai salon hakane bill din,dr hafsa tayi murmushi tace ina gani a ig aydarh ai ba daya bane da namu aydarh tayi shiru kafin su fita sai da suka rufe kofan part din kafin suka fita,sai dasuka shiga keke kafin dr hafsa tace daman kinsan rabiah ne? Aydarh ta girgiza kai kafin tace sister dr ibraheem ne right?dr hafsa ta gyada kai kafin tace mi yakawo ta? Aydarh tabude hannu alaman batasani ba shiru dr hafsa tayi kafin tace datace idan sunyi waya da yallabai zatace masa sun zo shi ya aiko su? Aydarh tace I didn’t even know kawai ganin su nayi sun shigo, dr hafsa tace basu da hankali yaran nan at all bansan abunda ke damun su ba, aydarh dai tayi shiru har bakin babban plaza mai keken yayi Parking suka sauka dr hafsa ta biyasa kudin kafin suka wuce cikin plaza suka shiga wani irin faduwa. Wuri suka samu bayan Sadyyyy tayi welcoming dinsu cike da mutunci,tight friend din dr hafsa ce shagon babba ne mai kyau akwai komai a shagon, sadyy tayi murmushi kafin tace kawata ina aka samu balarabiya ne?dr hafsa ta girgiza kai tace gata nan dai kina gani she is my sister sadyyy tace Allah sarki kafin ta kalli aydarh da fara’a a fuskanta tace sannu fa aydarh ta mayar mata da murmushin tace sannu “dr hafsa takalli sadyyy tace jaa da baki zaayi mata lallan ni black kawai nakeso sadyyy tace tau shknn salon fa? Dr hafsa tace shima za’ayi afara yin lallan shi keda wahala,cikin few minutes aka hada komai kafin aka fara zanawa aydarh hadaddan flower a kafa, mai azaban kyau simple style ana farawa dr hafsa tafara warware mata calaban there are experts shiyasa ba awani wahala ba aka gama jan yayi kyau sosai sai daya fara sha kafin sadyyy ta dinga bin rings din hannu aydarh da kallo aydarh na lura da ita batace komai badai dr hafsa na janta da fira sama sama, kafin sadyy tace ki cire zoben sai ayi black din aydarh ta gyada kai kafin tasa hannu tafara cire rings tana gama cirewa ta hadda duk three din ta mikawa dr hafsa karba tayi tasaka cikin handbag dinta kafin tace cigaba da labarin datakeyi, sadyyy tayi murmushi tace kawata ban taba wa wani lalle yayi kyaun haka ba Wallahi dr hafsa tace dan Allah fa masha Allah aydarh dai murmushi kawai take,sadyyy tasaki baki tana kallon dr hafsa bayan tagama warware ma aydarh calaban gently tasa hannu ta shafa gashin aydarh kafin tayi kasa da murya tace Allahumma bareek” yanzu nan wai gashin nan salon yake bukata? Dr hafsa tace haka yake wannan gashi sai ki dinga ganinsa kamar a gyare kullun “ sadyy tace amma baki jima dayin salon ba right? Aydarh ta girgiza kai kafin tace yajima,sadyyy dai tayi shiru tana kallon ikon Allah, tun shigowar su taso tagane aydarh sai dai tayi shiru tarasa ina ta taba ganinta, can takalli dr hafsa tace kawata kina shiga page din salmerh malami right? Dr hafsa tayi murmushi saboda tama san abunda sadyy zata fadi kafin tace ehh ina shiga sadyyy ta rage murya tace dan Allah ba suna kama da wannan yarinyar datake posting ba dan dai wannan tafi waccan haske da giba yarinya dana nuna maki hillis din nace miki a million kadan ke babu did you remember? Dr hafsa tayi saurin cewa ehhh natuna sadyyy “ sadyyy tace Wallahi kaman ita, dr hafsa ta kalli aydarh da kanta ke kasa bata son labarin yayi tsawo saboda ta fahimce labarin kaman irin rauni aydarh ne kar abunda yafaru jiya yafaru yau kar daga wannan labarin su sake taso mata inda yake mata ciwo, ta dinga irin kukan datayi jiya,dr hafsat ace ehhh itace kawata sadyyy tawani gwallo ido tasaki hannun aydarh tace ki rantse da martabar Allah dr hafsa tace ai bama wannan wasan, sadyyy tayi shiru tana mamakin abunda yakawo nan din ‘shiru tayi kafin tace Allah sarki “tana kallon aydarh kafin tayi kasa da murya tace ki godewa Allah you are more than fine you are more than beautiful kinfi kyawu kyau , dr hafsa tayi murmushi tace awwww sadyyy kice masha Allah yanzu dai ayi sauri agama lallan Saboda mu koma dawuri let her makes some preparation for her husband a gida “sadyyy tace miji? Is she married dr hafsa ta gyada kai tace sure “sadyy da bakinta yak’I rufuwa saboda murmushi tace masha Allah congratulations dear Allah yabaku zaman lafiya da yara nagari aydarh tace Ameen ahankali Still bata dago kanta ba, sadyyy tace kawata amma bata haihu bako? Dr hafsa tace ehh sadyyy tace daga waje zai dawo mijin saboda na lura kamar itama tafi zama waje, dr hafsa tace aaaa sadyyy batayi shiru ba tasake cewa a yola kuke ba?Aydarh ta gyada mata kai kawai,dr hafsa taga tambayoyin nayin yawa tace ki kira wata cikin su sai tayi mun ni ita kiyi mata kawai,sadyyy tajuya tace tau shknn bara nakira tunda ke baki ne kawai ba? Dr hafsa tace eh baki kawai sai mun retouch itakuma wash kawai zaa mata sai steaming baki daya sadyyy tace tau shknn,wasu hadaddun leaf sadyyy ta zanawa aydarh a hannu yah rabbil alameen yayi masifan kyau yayi endless kyau masha Allah kadan kadan akayi black henna kasancewan ta fara bakaramin zama lallen yayi hannun ba ga yaji kayan hadi ya kara baki har wani shine shine yake, ledan jan aka bude shima yafara. Dr ibrahim yace tau ka kira ta sai tabude data koh? Malik yace okay kafin yayi dialing number dr hafsa tana daga tayi sallama ya amsa kafin yayi kasa da murya yace kunna data ki ya kashe wayan wayan tabi da kallo kafin ta kalli aydarh sai tajawo ta kunna data kafin taga number dr ibrahim na kiranta vedio call accepting tayi tana mamaki vedio call kuma dr ibrahim , Malik tagani zaune kan katifan Wallahi zatin shi kyau kwarjini nutsuwa da kamala har a cikin waya masun bayana ba a fili kawai ba da sauri ta mika aydarh da aka cire ma lalle hannu daya wayar karba tayi tana ma dr hafsa alama dawaye murya can kasa dr hafsa tayi murmushi kafin tace yallabai “bin screen din wayan tayi da kallo shima ita yake kallo ganin yarda aka gyara mata gashi lumshi ido yayi kafin ya bude yana tasbihi wani irin kyau yaga an kara mata,kanta kasa kafin murya can kasa tace ina wuni sir? Bai amsa mata bas ai cewa yayi angama ne? Ta girgiza masa kai yayi shiru yana kallon yarda take wani dauke ido wani cute smile yayi yashafa hadaddan kwantatcan bread din yasa cikin ransa yace sturbborn bea very cute very demure “cuddle bug” yasamu kansa dafada ahankali a fili bai ma san yafadi ba itama bataji ba, ahankali yace the hair
Chapter 48 · 0% Book details