← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 197

Sashe 54

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kunya da nauyi sun hanata tambayar ta cigaba da wasa da zoben hannunta hibba tace k ici abincin fa kar ya huce naga tun dazu kadan kika ci,aydarh ta girgiza kai tace ah’ah ya isa,hibba ta bita da kallo tace yanzu dan abincin nan dakika ci har ya isa? Hibba tace tau auntie aydarh ko dai ciki ne gareki? Aydarh ta girgiza kai tace Allah ah’ah kawai na koshi, hibba tace tau shknn bara na ajiye chops din su sai nayi maki packaging a leda idan zaku tafi gida sai ki tafi dashi aydarh tace to “nagode “ abinci hibba ta dauka tasanya hijab dinta ta fita suna parlor suna kallon kwallo sannu tayi musu suka amsa ta wuce sai data dawo malik yace madam yarinyar nan bata cin abinci yau cikin ta tun rabin kofin shayi ne ko zaki taimaka kisa taci?hibba tayi murmushi tace Wallahi nagani kadan taci nayi nayi da ita takara tace aaaaa malik ya gyada kai kafin ya juya ya cigaba da kallonsa,dr ibrahim ya kalli matar sa yace tau ko wani abun zaa samu mata ko fura can wajan iya sai nakira rabiah ta miko?malik ya girgiza kai yace ko ankawo bazata Sha ba kawai a rabu da ita “hibba tace aaa yayah malik ko a jaraba karbo mata manah?malik ya sake girgiza kai yace tunda tak’I bazata cin ban e komi aka kawo “dr ibrahim yace tau shknn,hibba dai ta koma bedroom din tana kallon Aydarh kafin tace ohh ni ke kam abinci ne makiyinki tau ana haka mutun yadinga zama da yunwa har kin saba shiyasa ga cikin ki nan kullun kaman babu hanji yanan a shafe very flat, Aydarh tayi murmushi kawai kadan bata ce komai ba,hibba ta zauna tace tau baki da kawa anan kano aydarh ta girgiza kai kafin tace erh auntie hafsa ce kawai muke magana sai inna sai few students a class din mu, hibba tace Allah sarki islamiya? Aydarh ta gyada kai hibba tace ai yafi sauki aydarh naji dadin da baki ma da kawan, amma Banda nan gidan da gidan inna shima bai zuwa ko’ina,aydarh tabude hannu alaman bata sani ba, hibba na kallonta tace baku da saurin sabo da mutane ne kawai “Aydarh ta gyada mata kai,kafin hibba tace idan zaku tafi zan baki wani perfume ki dinga amfani dashi kinji?aydarh ta gyada kai tace to nagode “.malik yayi shiru har sai da dr ibrahim yagama bayani kafin yace kayi kokari ranka ya dade dr ibrahim yace amma fa har tsoro naji nayi tunani ta suma fa Wallahi,malik yawara ido yace kai haba Allah yakare dai Dr ibrahim yace Ameen ni fa har bana son hutun nan yakare na koma clinic Allah,malik yace tau ai sai kadawo gida da zama kabar musu aikin “dr ibrahim yace kai wuyanka bakan magana kaman wani mai nama lallashi na naso kayi malik ya hade rai kafin yace tau sannu ASSEIYARH “dr ibrahim yayi wani kalan dariya yace oh ita kawai zaka iya lallashi kenan malik ya gyada kai bai ce komai ba ya cigaba da kallonsa dr ibrahim yace kai dinnan da shegen masifa har ita din baka wani lallashi hakuri kawai take dakai “Malik ya mike ya zuba hannunsa a aljihu yace tau idan batayi hakuri ba sai tayi hauka tunda duk duniya bayan ni bata dawani mijin aie “dr ibrahim yabisa da kallo har yafice kafin shima yadauki wayansa yabi sa baya,a kofan gida ya gansa yace wai tun yanzu zaka tafi can din?malik ya gyada kai yace tau muje tare “bai ce komai ba suka juya suka tafi,Allh musa yace malik kaji kiran gagawa ko?malik yace ehhh sir ‘Allh musa yace tafiya zanyi na kusan five months abuja “malik yace Allah sarki Allah ya tsare yabada sa’a Allh musa yace Ameen kafin yace malik saidai fa kayi hakuri amma zaa tsaya da aiki “ har sai na dawo sauran works din duk nayi musu bayani a jiya already daman duk karshan shekara ina wannan tafiyan sun sani, kafin nadawo sai kasamu wani dan abun yi saboda ka samu abun rike kanka da mai dakin ka,malik yayi shiru kafin yace Alright sir “Allh musa yatashi ya shiga daki kusan ten minutes kafin yafito hannu 20k ya mikawa malik yace gashi ba yawa Allah yasa maka da alkhairi yabaka abun yi nagari dr ibrahim yace Ameen yallabai sallama sukayi suka fita, dr ibrahim yace yanzu miye abunyi yallabai? Malik yayi shiru yace ni kaina ban sani ba dr ibrahim yace in sha Allah,Allah zai kawo mafita let’s keep praying yafada yana patting shoulder dinsa, ba gida suka wuce bas ai dasu ka biya general hospital zasu duba wani abokin dr ibrahim dake jinya can. Cikin firan dasukayi yau aydarh kaman wani sabon class ne tashiga domin kau hibba ba ruwanta babu wani abu datake sayawa ko boyewa aydarh komai yazo fada mata shi take abu dayawa mamaki yake bata wai duk shi malik din ke da wannan matsayin? Ikon Allah akwai questions dayawa datake son yiwa hibba amma nauyin ta yahanata duk firan yawanci hibba keyin abun ta, hibba tace duk irin fa wahalan dazaa baka labari baka tunani yakai haka sai kaji da kanka billahi,mudai Allah ya tsallakan damu,aydarh tace mi? Hibba tace shi wajan disvirgin din Aydarh tasauka da kanta kasa gabanta yayi wani irin faduwa batace komai ba tayi shiru hibba tace hmmm ni har bana son tunu zafin Doctor kanshi yaji tausai na shiyasa har yau said ai a tsaya sama sama Amma can kam sai nakara hutawa “duk nasan yau dawuya ya hakura jiya dakyar nasamu yayi bacci fa shima sai da boobs a bakin shi Allah,Aydarh tawara ido bata masan ta maimaita abunda hibban tace ba tana bude manyan idonta tabarakallah,hibba tace Wallahi kinsan dai zafin da ake jib a,ita duk tunaninta aydarh saboda zafin ne ta firgita Ko tausayinta taji,hibba tace Ku ai inda sabo ma kun saba mu ma zamu saba ahankali, aydarh tace eyyerh sorry tafada tana sukunyan da kanta kasa, can hibba tace auntie aydarh kinji dadin jikinki ke kam Allah “Aydarh tace kai haba, hibba tace Wallahi fa kiji ki fa idan ba rashin tsoron Allah na maza ba shikam ya malik mi zai gani ajikin wata Allah natuba billahi ban taba ganin structure mai kyau ba irin naki ban taba ganin skinny mai kyau ba kallan naki ke wllh ban taba ma ganin abu mai kyau ba irin ki, Aydarh tayi wani dariya hibba tasaki baki tana kallonta kafin tasa hannu ta rufe bakinta Still takasa daina dariyan tace you are funny Wallahi auntie hibba, ke kam ai kinada kyau ku kullun kullun sai ku dinga cewa abu daya, tafasa tana rufe fuskanta, tana dariya “hibba tace ai yayah malik nasan a rana sai yafada sau dubu kema haka shima ai yanada kyau da kinga sa kinsan jinin ku guda wannan yaran ku ai said ai ku dinga boyesu billahi saboda baki, aydarh dai batace komai ba can ta mike tace auntie hibba sun fita ne?hibba ya gyada mata kai kafin tace ehhh fita sukayi amma nasan zuwa anjima kadan zaki gansu,aydarh tace eyyerh daman auntie hafsa c eke zazzabi zan mi shi magana muje mu dubata hibba tace Allah sarki Allah yabata lafiya aydarh tace Amen. Sai wajan 5:00pm suka dawo suna dawowa ko shiga ciki malik baiyi ba yace wa dr ibrahim yace ta fito su wuce, hibba ta bata turaran datace kafin ta gaya mata yarda zatayi amfani dasu chops din da bata ci ba, hibba ta zuba mata a Leda kafin tasaka hijab har bakin kofa ta rakota inda malik da dr ibrahim ke tsaye suna jiransu, sallama sukayi malik yasake yiwa hibba godiya aydarh ma haka hibba duk sai taji wani kala kaman kar ta tafi, anan bakin titi suka samu keke,har kofan gida yakawo su malik yabiyasa kudinsa kafin suka shige tana gaba yana baya biye da ita, kofan part din yabude suka shiga bedroom tawuce ta ajiye kayan hannunta pics din dake jiki ba karamin sa ta kunya suke bay au daga labarin dasukayi da hibba sai takara jin girma da nauyin dake kanta na auransa,ya idan yanzu fa shima yace suyi irin wannan rayuwa?da sauri ta girgiza kanta tace bana sonshi shima baya sona to babu abunda ma zai faru dawannan tunani ta tattare su ta jera a wardrobe kafin tawuce toilet flask din ruwan zafin ta bude ta juye a bucket tawuce toilet tayi wanka tareda dauro alwallan magriba, vaseline kawai tashafa sai perfume, tasake gyara parking dinta kafin ta saka inners da gown din atampha, bude kofan tayi yana parlor shima da alama yayi wanka amma bai Chanza kaya ba singlet ce jikinsa sai dogon wandon shadda da karamin towel yana goge suman kanshi da ya wanke wanda tayi kusan na wata macen mai gashi a Nigeria yanda sumansa yake kaman na larabawa kallo daya tayi masa ta dauke ido tashige kitchen dasauri yana kallon duk abunda takeyi bai ce komai basai cigaba da abun yakeyi dayayi , har tashiga kafin ta bude idonta da ta rufe ta kulle kofan dasauri, bata taba ganinsa haka ba, ahankali tace katuwa kai tafada kasa kasa tana harara kofan kitchen din kaman yana jikin kofan, ruwa ta tara a tukunya kafin ta kunna gas, ta daura white rice zatayi kadan sai aci da mai tunda yasiyo yaji tana son shinkafa da mai da yaji sau daya ya tabayi tagani shine zata gwada yau tana daurawa ranar hadda wake,bude ledan da taga wake tayi ,tasa cup din data gani ciki ta auna half kafin ta tsince sa tass duk da babu wani tsinta a ciki,wankewa tayi ta zuba kafin ta mayarda tukunya ta rufe,gently take takowa cikin parlor yana zaune kan carpet ya chanza kaya zuwa black shirt sai black jeans, zama tayi can nesa dashi kafin ta saukan da kanta kasa tana wasa da gefen carpet din kallonta yayi yanda inner cap dinta yaja baya bakaramin kyau yayi mata ba, shiru yayi baice komai bay ana sauraron ta, can dai tace “ kasiyo salad din da cucumber”sai tayi shiru kallonta yake ko dauke ido babu can yayi kasa da murya kafin yace mi za’ayi dashi? Tace white rice and beans zan dafa shiru yayi bai ce komai
Chapter 54 · 0% Book details