← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 197

Sashe 141

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kai tace ah’ah yayah ga auntie nan ai Allah yabata lapia “ta karbi key din hannun rufaidarh tace zatayi driving da kanta hajajju tace ke kam dai anyi marar lafiyar kai fatiee yoo wannan ai rashin wayewa ne jamaa kit saya kiduba yarinyarki mutun ya dankara mata ciki tana ta wahala anzo da ita asibiti rai ahannu Allah don ni isowa ta nan nayi tunanin zan ga kuna fasa makoki ma ashe abun duk bana arziki bane “ oum dai tayi musu sallama tawuce baba ta girgiza kai tayi murmushi tace Allah sarki fatima Allah yasaka maki alkhairi da duk mata zasu zama kamanta da anji dadi ubangiji Allah yayi muku albarka Allah yacigaba da hada kanku Allah kuma ya aurar da sauran ummi tace Ameen yah Allah mama “Abby yace bara nakira nababa na fada masa ankusa manah mata ko aboki rufaidarh tace yakamata kam yana can abuja abby yagyada kai yace ni nakai sa airport da asuban nan yace zaije yayi signing wani contract ‘’rufaidarh tace ehh hakane baba tace Allah yataimaka yabada sa’a abby yafito da wayansa yayi dialing number abba bai shiga ba “Yana zuwa dakin yatura kofan ahankali yashiga “ yamaida yarufe ya jinginar da kansa jikin kofan “ yana mata wani kalan kallo kallo mai cike da so soyayya kauna shauk’I burgewa dakuma tausai “ All praise been to Allah ‘ hakika bashi da bakin yiwa Allah godiya he cannot pretends or deny anything amma Allah yayi masa kyauta dakari Allah yamasa ni’ima da rahama a rayuwa cikin abunda bai fi shekara daya ba Allah ya chanza masa rayuwa Allah ya aiko masa da ita cikin rayuwarsa tazama haske da salama a rohi da rayuwarsa! Ta zaman masa abun Alfahari “inda yace bazai mata so irin son mutuwa ba yayi karya idan yace bazai mata gata irin na nunawa a duniya ba ya cuce rayuwarsa “ bayan ummi da abby bazai taba hada kaunar daya ke mata dawani abun ba a rayuwarsa yana mata so irin son dake daure jijiyoyin jiki “ kwance take kan gadon ansaka mata karin ruwa sai yanzu yake lura da wani extra haske da glowing din data kara komai na fuskanta kaman an dai zana “ saidai tafada tayi rama murmushi yayi kadan abubuwa dayawa nadawo masa a kai game da ita “komai nata na burgesa tun farkon haduwar su “ karasawa yayi yaja kujera yazauna ahankali yana kallonta ko kiftawa babu ga murmushi kwance a kyakyawar fuskan shi sajan sa ya cika sosai yakarawa farin fatan sa kyau da haiba “ kaman tana ido biyu yanda yake wani dage gira irin na bad boys tunani kawai yake yanda zasu kasance da ita idan tafarka tasan tanada ciki yah Allahu yasan akwai daru tsakanin su koma miye zai iya handling matansa ko ba komai yasan tana shakkarsa “ hannu yasa yana rike hannunta mai karin ruwa har yanzu akwai zafi amma ba kaman na dazu ba ‘ahankali yafara tofa mata addua kafin yakai hannu yayi placing daidai kasan maranta yaji tayi tauri mamaki yake yana kara jinjina ikon Allah yanda Allah yaboye abunsa “ko kadan bai taba tunanin yarinyar nan nada ciki ba “ ko kadan alama bai nuna masa yasan ita kuma bata sani ba duk sai yanzu yake recalling abubuwan da duk zaya nuna masa alaman hakan amma bai gane ba “ hakika Allah shi ke yarda yaso a lokacin daya so Alhamdulilah, ya dinga yawo da hannunsa a cikin ta dan motsa bakinta tayi hankali yalura so take ta tashi yayi murmushi yana dauke hannunsa a cikin ya dinga kallonta dai. Ba ita ta farka basai bayan daakayi azahar cikinsu babu wanda yatafi har abby tun oum data tafi babu wanda yakara tafiya lokacin suka shigo kowa ya dubata da jiki ita dai sai binsu take da ido Allah kawai yasan halin wahalar da ta shiga yau sai ita “ tasha wahala ba wahalar wasa ba bakinta yayi mata nauyi ma bazata iya jin zatayi magana ba ummi ta lallaba ta sukaje toilet tayi mata alwalla suka fito ta taimaka mata tayi salla nr Asmau ce tashigo tasake dubata ta rubuta wasu drugs din kafin tace asamu ko da tea ne a gwada bata ko zaya zauna a cikinta yunwa babu dadi ba kaman ita da yanzu ba ita daya bace “ abby yace rufaidarh ta taso sai ta karban mata shayin a gida tunda tafarka shi zaya koma campany “baba ta tashi tace bara ta bisu “har zasu fita abby ya juyo yace kai malam bazaka koma gida bai dan yaso sai ka dawo tunda aie ba kwana zatayi anan ba right?babu kunya malik yace aaaa yallabai ina nan hajajju tayi mitsi mitsi da ido tace nan fa zaya zauna ya dinga gadin matar yasan yana sonta yake bata wahalar dazaa dinga kwantar da ita gadon asibiti gashi kaza wannan bazai iya zuwa ya siya yakawo ba Allah dai yasawwake nidai kingani nan babu ruwana “ fita sukayi yarage daga ummi sai malik da hajajju “ummi takalli aydarh datayi shiru idonta a rufe amma ba bacci take bas ai faman sauke numfashin wahala take kana kallonta kaga marar lafiya “ ummi tace sannu baby “Aydarh tasamu ahankali ta gyada mata kai malik sai faman kallonta yake ko kiftawa babu hajajju tayi gyaran murya tace yanzu fa idan ba wasa bas ai kiga yarinyar nan tayi gadon uwarta “wajan wahalar kwaikwai kaiiiiii sam kwaikwai ba kyau “ haka uwarta ke wahala har tsawon wata shidda “Wallahi Allah dai yaraba su lapia amma sam laulayi mugun abune bashi da kyau “kaf aydarh najin hajajju amma bata ma fahimta da kyau kan abunda take magana taji tana cewa Allah yaraba su lapia tau hankalin ta da tunanin ta duk bai kai nan ba wahalar datake sha a yanzu kawai ya isheta ‘ Babu bata lokaci rufaidarh nashiga gida ko wajan oum bata karasa ba tasaka maids su hada lafiyayar lunch dakuma ruwan tea tafada musu abubuwan dazasu saka wajan dafawar wanda tasan favorites din aydarh ne “tana shiga parts din oum ta isketa parlor waya take da alama kuma cikin maaikatan mall dinta ne dake can lagos saboda maganar kayan datayi order suke a gefenta ta zauna har takarasa wayan tana zarewa a kunne ta waiwayo tana kallon rufaidarh tace amarya “ya jikin babyn ne?rufaidarh tayi murmushi tace alhamdulilah fa ta farka yanzun ma dawowa nayi namata tea nakoma “oum tace eyyerh Allah yaraba lapia rufaidarh tace Ameen yah Allah yo uktiee wannan miji yanata rawar kafa badole kunya tasa mu bar masa mata ba don ma maman tashi daidai take dashi cikinsu har karasa ma wanda yafi kula da baby saidai fa na zama yar kallo Wallahi “oum tayi murmushi tace shiyasa na taho ni babu dalilin zamana tunda yanda zasuyi mata ni ba lallai hakan zanyi mata ba “ rufaidarh ta gyada kai tace Alhamdulilah fa uktiee baby kam Allah yabata nidai fatana daya kada Allah yasa ke ta biyo da mun bani Wallahi Saboda da alama itama laulayin nan baya zuwan mata dasauki Allah dai ya inganta oum tace tau Ameen yah rabbil alameen amma dai baby dawannan rakin nata da lanbon ta da baaji dadi ba “rufaidarh tamike tace bara na watsa ruwa ina mukullin motana ina ganin daga kasa zan wuce basai nadawo nan bas ai dai mun dawo kawai oum tasa hannu tana miko mata tace tau shknn Allah yatsare sai kun dawo din rufaidarh tace yauwa kin fadawa babanta ne? Oum ta girgiza kai tace no idan yadawo yaji kawai mun daiyi waya yanzu dashi “ rufaidarh tayi yar dariya tace lallai kam kinada aiki yayansa baban mijin kina fitowa yadaga waya ya doka masa call don ma bai same sa ba oum tarike baki tace wai wai abun nasu sai su din rufaidarh tace gaskia dai “ dakin ta wuce bayan tasha maganin ta kaza ne daya dahu luguf mai mata gyaran jiki tabata wanka tashiga tayi amfani da magungunan wankan tafito wani kalan kamshi mai sanyin dadi na fitowa daga jikinta sharp sharp tashirya tasaka dogon rigan swiss lace orange and black tayi kyau sosai har kiba ta kara tsaban gyara datake sha har sunka mata baskets din cikin mota tashiga tawuce asibitin “sai wajan bayan Isha”I aka sallame su bayan an tura mata musu wani magani “suna shiga gida tace rufaidarh takama ta wanka take son yi har yanzu bata san tanada ciki ba malik na nan makale dakyar aka samu rufaidarh ta lallabesa yawuce gida shima sai da aydarh tayi masa magana ta ido “yanayi wanka Ko abinci bai tsaya yaci ba ya saka wani hadaddan cotton yard sky blue anyi masa dinki kafta kana kallon yard din kasan tsaban kudi aka saka wajan siyan sa “ parlor ya tarar dasu aydarh ta kwantar da kanta a laps din rufaidarh tasaka white sleeping dress sai katuwan rigan sanyi da safa sai hulan sanyi a kanta tayi shiru idonta a rufe “ sai oum dake gefe tana juya mata tea yahuce tasha ga drugs din a leda nan kasa “sallama yayi rufaidarh da oum suka amsa shi gently yakarasa cikin parlor yazauna nan kasan carpet yayi kasa da kai kafin duk ya gaishe su “ suka amsa shi da fara’a rufaidarh tace son amma Ko abinci baka tsaya ci ba nasani kayi saurin dawowa baice komai ba yadai shafa kansa yana murmushi oum tace yakarasa can dining sai akawo masa dinner yayi mai jikin dasauki Alhamdulilah ma “rufaidarh tace gaskia sosai rashin cin abincinne damuwa aman daman kuma sai ahankali malik yadago kai yasace kallonta kafin yace mom tasake aman ne yanzu rufaidarh takalli aydarh ta jinjina kai tace ehh Wallahi tayi yanzu ba dadewa kafin mu dawo parlor yace ohk “ yamike yace zanje nadawo mom “ rufaidarh ta gyada masa kai tace ohk son sai kadawo “ahankali tabude idon bakinta yamata nauyi don juya ma take gani tace masa zan ci fries “juyowa yayi dasauri yace tau fries kawai? Ta gyada masa kai his reaction only will explore what’s in his mind “zaka ga iya adadin so da damuwan dayayi da ita Wallahi bakaramin dadi oum ke jiba”dasaurin sa yafice daga parlor “rufaidarh takalli oum tace wai uktiee wani magnet ne ko kuma wani magic ne
Chapter 141 · 0% Book details