← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 197

Sashe 5

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kamshin rosemary air freshener hakan yataimaka matuka wajan fitar da siring kamshin a parlor din bude warms din tayi taga white spaghetti da kayan lanbu anyi slices dinsu in very attractive shape dan bata fuska tayi tabude dayan warmer din itama dai vegetables stew ce taji kayan ciki fresh watermelon juice ne cikin jug din wanda hakan yana daya daga cikin aladar oum baa taba shan wani drinks apart from fresh juice kadan ta zuba tafara ci ahankali tamkar wacce ke ci dan dole ba dan yunwar cikinta bah takai 30mins tanacin abinci da bai fi yaro dan shekara 3 ba zai ci shi kusan rabin hankalinta yakoma kan tunanin abunda ke jawo mata faduwar gaba duk kwanan bah so take Abba tafada masa haka kawai take jin kamar wani abu na damunta to miye wannan tasamu kanta dayiwa kanta wannan tambayar sam bata san oum bata cikin gidan duk tunanin tana dakinta ko part din auntie rufaideerh karar danna door bell din da akayi shi yaja hankalinta ta mayarda da dubanta kan kofar maids din da aka tanada domin aikin tuni ta tambaye waye tareda bude kofar bayan amsa mata da salma tayi ,masha Allah salma itama bai laifi komai nata daidai bazata wuce shekarun aydar bah koma tawuce sai dai da 1or2 years sanye take cikin dinki fitted gown din atamphar yayi matukar amsar jikinta kasancewar ta mai dan murjajan jiki saidai ko kama kafar aydarh batayi bah wajan kyau da ma surar jiki baki daya ta sallama takarasa dining din iyakar lips kawai aydarh ta amsa sallamar ganin yanda tayi ne yasa salmar tuna ita fa mai laifi ce takirata bata dauka,sannin halin aydarh yasa salma yin murmushi tareda fara ba aydarh dalilin dayasa bata shigo da wuri bah tunda tafara magana aydarh ke kallonta ko kiftawa babu saninin bazata amsa bah yasa salma chanza labarin,aydarh miya faru naga kamar ba yarda nasake ganinki ba wani abu yafaru ne ita dai aydarh batace komai tacigaba da kallon salmar harararta salma keyi tace wait kinga bana son rashin kirki ina maki magana kin mun shiru can tamike tace mata sannu da mamaki salman ke kallonta wannan hali nata bata san ranar chanza ce shi dakinta takoma ta zauna kan sofa daurin datayi ma kanta ne take warwarewa zuba mata ido salma tayi tace aydarh oum pah mutsa bakinta tayi tace she is in room mikewa salman tayi tafita domin gaishe da oum sosai suka saba da oum wacce take ma kallon mahaifiya itama oum na mata kallon diya da sallama ta bude kofar dakin amma shiru babu kowa girgiza kanta tayi tana jinjina irin halin aydarh bata ma san oum bata gidan ba ma girgiza kayi takoma dakin aydarh cikin wannan muryarta ta mai nuna zallar shagwaba da kuma aji tace nakiraki baki daga ba kuma baki tambayeni dalilin kiran salma tayi kasa da murya tace naga dana shigo har fara baki hakuri nayi amma tsabar rainin hankali kika zuba man ido sorry tafada agajarce salma tace to miya faru kika kirani bana kusa ban daga bah nayi kokari nazo gidan kuma kika zuba ido kina kallona kamar wata yar iska tashi tayi tareda daukar wayarta tace babu komai kuma sakin baki salma tayi tana kallonta kamar taga abun mamaki tace hala kanki babu dadi yanzu kuma shiru aydarh tayi har salma tagama masifar tayi shiru tace kingama wani katon bakin ciki ya tsayawa salma a rai ta watsa mata harara bag dinta tadauka tare nufar hanyar kofa cikin masifa take cewa in sha Allah ankusa yi manah maganinki miskilar banza miskilar wofi murmushi tayi kadan ita dai duk nan bataga abun masifa amma dayake salmar ita komai na fada ne da masifa shine har taji haushi wayarta ta dauka tashiga playing games amma kaf hankalinta na kan faduwar da gaban takeyi runtse idonta tayi tanajin wani yanayi tamkar bada ta lapia tun tashinta yau duk tunanin ta cramps zatayi rau rau tayi da ido gabanta na faduwa domin ba karamin wahala take bah idan tana cramps har allura ake mata sometimes har dayan ciwon nata yake tasowa watau asthma hakanan taji tana so daga curtains din window dinta Allahumma bareek yanayin jikin su aydarh shi ake kira da package shape gyara zip din gaban abayar nata tayi boobs dinta dake cure waje guda suka fitar wani shape mai kyau da daukar hankali fatar wajan tasamu Hutu da tsabata game da kulawa ciza lips dinta take tana takawa ahankali zuwa yanzu ta fahimce ciwon marar ne take komawa tayi ta kwanta kan gado. Kasancewar garin da alamar hadari yasa ummi fitowa tashiga dakin su aysher zaune suke halime ce ke gyarawa maryam (autarh) kallabar da aysha tayi mata take complain din yayi zafi har aysha ta saba da complain dinsu na zafin hannu da suke cewa tana dashi tun tana biye musu suyi chapter har takoma idan sunyi saidai tayi shiru tana kallonsu gyaran murya ummi tace tau fadan da bai karewar ne kuka dasa koh?takarasa maganar alamar tana tambaya dasauri maryam tace wallahi ummi adda zafin hannunta kullun karuwa yakeyi halimai ta turo baki tace ummi adda pah da gangan takeyi saboda ace ta daina yi kitso daman ai bataso aysha tace ummi ni duk banda lokacin wannan abun nasu abinci zaa daura ne? Eh ummi ta amsa mata tare da bata umarnin abunda zaa daura din ko da ta fito saida tafara shiga dakin malik ta mashi ya jiki tareda tambayar shi ko akwai abunda yake da bukata maida duban shi yayi gareta cikin wannan muryar tashi kamar mai magana dan dole yace mata tea tasan daga wannan babu saura abunda zai ce mata kasa tayi da murya tace wai yayah itama auntie tamu haka kake magana da ita?mugun kallo ya watsa mata da gudu ta fito daga dakin saboda tasan sauran ma ko bayan fitar aysha maganar tace tadawo mashi akai kalmar ‘ auntie’ tana nufin budurwa murmushi yayi yana shafa salkakiyar suman kanshi bakaa sol shi kam bai ga ranar bah ma kan murhun gawaye ta daura mashi ruwan zafin 5mins tagama ta hada mashi ta mika mashi daki idonshi na rufe amma ba bacci yake bah ta ajiye ta fita domin cigaba da aikin girkinsu, oum ta maida dubanta ga rufaidarh ganin cikin plan dinsu wani yazo dasauki domin kau harda gudun zuwa wajan hajajju garesu domin itace zata nuna masu kofar cikan burinsu madaidaicin gidan dake shafe da cement ko ina tsab a gyare gida tsofi ne babu wani hayaniya sam mama Rabi wace matsayin kaka take ga abba ita daya ta rage musu shi da dan uwan nashi kaf dunia amma rashin son zumunci irin na abba dakuma ware kanshi dayayi tun farko daga lamarin familyn shi tun bayan rasuwar mahaifinsu mahaifiyarsu ta jima da rasu tun suna yara Wanene dan uwan abba? Wane irin plan oum da rufaidarh garesu wanda suke ganin zasu jifi tsuntsu biyu da Dutsi daya? Miya kawo su wajan kanwar kakarsu abba wacce ke matsayin kakarsu? Salma tace ankusa maganin aydarh wani irin magani? Mi yajawo kamar da malik keyi da abba? Tun suna yara cikin tattare kwarin gwiwa da karfin zuciya oum ta fara ma baaba kulu magana tunda ta fara magana hajajju ke kallon oum da baaba kulu da rufaidarh baki daya kallonsu take kamar wasu zararru tana mitsi mitsi da ido tana jiran taji iyakar idan oum zata tsaya cikin sanyi murya game da raunin zuciya da sarewa oum ke magana tunda tafara baaba kulu ke kallonta cikin tausaya da tsabar kauna baaba har yaushe zamu bar cigaban wannan gaba da kiyayya dake tsakanin yan uwa biyu har yaushe zan cigaba da jure ganin ASEEYARH a wannan yanayin baaba fashewa tayi da kuka mai taba rai rufaidarh tacigaba da magana baaba maganar damuka zo ita itace mafita maganar da muka zo ita tace makama itace wukar dazata yanke duk wata damuwa da kowanin muke ciki! cikin gamsuwa da fatan cikar buri baaba tace rufaidarh kuyi saurin fadin abunda ke tafe daku kuyi saurin yin man bayani cikin gagawa kuyi saurin bani haske in sha Allah nayi alkawarin goyan bayan ku,bayanin duk plan dinsu sukayi ma baaba shiru yabiyo bayan rufaidarh takai ayar maganar ta ajiyar zuciya baaba tasauke domin ta yarda ta amince ta gamsu da duk bayanin da rufaidarh tayi mata zata fara magana kenan hajajju ta mike tamkar wacce kunama ta harba salati tagama tamkar wacce aka aiko ma sakon mumunan accident tace hala oum dai kun chanza addini daman ance waennan rubabbun larabawan sudan din ba hankali gareku ba Jama’a kuji wata maganar dauri tayi kasa da murya tace amma dai gaskia kulu baku da imani keda waennan masu zubin abzinawan nijer din haka kawai ku bankawa bayin Allah sharri saboda baku kaunar Allah wai wani saboda a gyara zumunci ita kuma adar ta gyara halinta tau sam babu ni a wannan bakin zunubi wannan sharrin ko a fim sai haka fashewa da kuka tayi tamkar wata tababba cikin daka tsawa da daga murya baaba kulu tace ke wai hajajju mahaukaciyar ina ce ina nan naga basu sa dake ba cikin wannan lamarin kuma saboda sun ga cikin mu guda dake yasa basu ce ke bamu wuri bah,haba dan Allah ki dinga abu kamar wata zararra ina amfanin wannan abunda kikayi haka tau ba ruwanki idan bazaki goye bayan wannan baiwar Allan ba a wannan sadaukarwa da tsoron Allah nata ba ba’a zage ta ba share hawaye hajajju tayi tareda fesar da majina ta mike tsaye tace tau gaskia kun zama abun tsoro tun zuwana yola nake ganin jafa’i kala kala babu irin mugun abun dake ban gani ba shiru sukayi babu wanda batayi mamaki bah domin a tunaninsu itace mutun ta farko dazata amince ta nuna yardar akan lamari amma har cikin rai rufaidarh tasan hajajju daga baya zata chanza magana ta amince domin idan da sabo kowa yasaba da wannan halin nata sosai baaba kulu ke jinjinawa oum wata irin kauna da soyyayarta na sake karuwa har cikin ranta addua tayi musu sosai da fatan alkhairi dakuma fatan cikar burinsu batare da wata matsala bah hajajju kau daki tashiga tayi zaman dirshan ta cigaba da hada kayanta a ghanan ta yau ban kwana yola gaskia duk idan dare
Chapter 5 · 0% Book details