← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 197

Sashe 17

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

take kamar a mafarki komai ke faruwa, har yanzu bata amsar tambayar na’ima ba kuma Still idon na’ima na kanta kamar tasamu t.v ganin tana hawaye yasa na’ima cewa asha kam sannu wallahi indai taipot ne haka yake mugun ciwo ne taipot wllh daurewa zakiyi ko maigidan naki zan kira maki ko kina bukatar wani abun bata jira amsar aydarh ba ta tashi tafita.”a office ta tarar da malik da Doctor ibrahim zuwa yanzu malik ya dan sake dashi suna fira akan abunda yashafi halin da kasar ke ciki , washe baki tayi tace sannunku yallabai ta farka naga kamar tana bukatar wani abu shiyasa nace bara nayi maka magana, Doctor ibrahim yace oh ta farka kenan, Bayan san son san halin da suke ciki hakan yasa shi daukar bags dinsu ya nufi dakin data ke ciki, can kasa yayi sallamar ko da hankalinta wajan yake ba lallai taji sa ba balle sam hankalinta baya tareda ita, cikin few seconds yakare mata kallo shekarun ta kwata kwata bazasu wuce na maryam autarsu ba amma sam yarda yanayi jikin su ba daya ba, jin alamar tsayuwar mutun akanta yasata dago idonta ta sace kallon shi batace mashi komai ba shima bai ce mata ba, kusan 10 minutes sunyi shiru babu mai magana sai celling fan dake nata aikin kawai ka ke jin sautin, duk ta takura ga wani irin fitsari da take ji kamar zai fito, ganin ba tada mafita ga kunya takeji ta ce mashi tana son pad ko zatayi wanka, sai taji daman tayi ma na’ima maganar, kwata kwata tasan bakinta bama zai iya furta ma mutun kamar na’ima ko da kalma daya ce ba,duk ta zama abun tausai kallo daya zakayi mata kasan batada lapia ba karamin gayu da hutu suka samu muhalli da waje a jikinta ba real definition of beauty classy ce aydarh “kallonta kawai ya ishe ka jin wani abun a rai, still kanshi nakasa idonshi na rufe , kamar zatayi kuka muryar ta tamkar sarewa zallar shagwabar hallita da kuma gata dasuka samu mazauni a murya game da rashin sabo da kuka sanin ta yarda zata furta maganar, tace tau ai ummi ta hada mun kaya ,shiru tayi kuma kamar wace aka daka ta fashe da kuka, wallahi shi mamaki ma tabashi baisan ma mi zai ce mata ba amma ya jinjina zallar yarintar ta sai yanzu ma yakara fahimtar wannan tamkar raino ne ma aka bashi, bai ce mata komai kamar yarda itama ba tasake magana sai kukan da tacigaba dayi kasa kasa, daukar bag din yayi ya dire a gabanta sannan ya juya yafita, nurse din yayi ma magana ta shiga ta taimaka mata ta shirya. Ahankali take shafa masa oily rublet hair din a kai kamar wacce ke shafa ma jariri abu haka take bi ahankali tana tafiyar da hannunta a sumar gently take rubbing mashi man, sanye take cikin wata mad dubai abaya yellow mai haske tayi matukar karbar jikinta sosai kanta babu kallabi sai wani hadaddan hair style da tayi akan,, kamshin jikinta dana jikinshi dana dakin baki daya hadin gwiwa da a.c dake fitar da kwantacan sanyi yahade wajan bada kamshi na musamman mai kwantar da hankali dasa nutsuwa, ahankali ya fesar da iska a bakin shi tareda tashi zaune ya maido ta zauna sosai kan cinyarshi, yadan fada kadan domin har yanzu da sauran tunani abun a ranshi duk da oum tana son mantar dashi komai amma yakasa ,cikin salihar murya cike da tausai kauna dakuma soyayya yace. Yace zarah ina son mu bar Nigeria cus zamana a Nigeria zai haifar man da mumunan ciwo a zuciya na yakarasa maganar yana zuba mata idonshi, ajiyar zuciya oum ta sauke tareda yi ma kanta masauki a kirjin shi tace, babu damuwa abba “duk yarda kace haka zaayi bani da fahimta ni kaina duk abunda yafaru bada son raina ba,bansan ta yarda komai yafaru ba “Amma hakan na nuni da wani iko ne na ubangiji, wani darasi ne na rayuwar dakuma bayanar da gaskia da na shekara sama da 22 ina kokarin nuna ma,amma kayi watsi da hakan, shiru tayi tana sauraron yarda bugun zuciyarshi ke fita, kusan 3mins bai ce komai ba ahankali ta dago kanta tace Abba nasan bayan mu dasu yayah babu wanda yasan abunda yafaru mi zai hana ka fahimce gaskia mai zai hana ka gyara laifin da ka aikata baka ganin Allah ne yaso ka da rahama a faruwar wannan alamarin, tun anan dunia yabaka damar gyara abunda ka aikata! Still Abba was quite sauraron ta kawai yake amma har cikin ranshi sam duk da faruwar wannan alamarin babu abunda ya chanza a zuciyar shi game da yayah ibrahim din da ahalin shi baki day abaya son duk wani labari ko tarihin da zai nuna tsohon asalin shi baya son alaqar da kuma zumunci da zai nuna yan’uwartakar su da abby sam yasa kafa yayi kwallo da alaqar dake tsakanin su yasa cleaner yayi cleaning tarihin da zai nuna asalin ko shi waye, tuni dunia tayi naam da shaharar shi a matsayin mai kudi dan mai kudi jikkan mai kudi kuma jinin mai kudi, tau taya suke tunanin zai iya fallasa gaskiyar tarihin sa?its unbelievable! Ita kanta oum shaida ce baya son abunda yashafi talauci baya kaunar sunan baya kaunar talaka duk abunda aydarh key i akan talaka duk hudubar shi ce duk tarbiyyar sa ce babu yarda oum ta iya said ai kallon ikon Allah, Kamar tasan abunda ke mashi yawo a kai kamar tasan abunda yake rayawa a zuciyarshi yasa ta cewa ABBANARH lokaci yayi dazaka…… da dan karfi ya kira sunanta zarahhhh bygone should be bygone please ! Daga karki sake yi man magana kalar wannan and get ready we are leaving tomorrow ! Bai jira amsarta ba yayi hanyar fita “oum ta bishi da kallo tana jin wani iri a zuciyarta , mike shirin faruwa?ta tambaye kanta duk wani efforts dinsu ita da rufaidarh yatafi a banza kenan? Inalilahi waina illahil rajiun shine kalmar da ta ambata a fili, wannan kuma wata sabuwar kaddarar ce ko mai? Wata zuciya ta gargadeta “ lumshe ido tayi ta bude kafin tace yah rabbil alameen kace man burina yah rahaman kasa nayi nasara kan abunda na shirya yah arrahamar rahimin kasa malik yazamo garkuwa haske da kuma madubi a rayuwar aydarh ya rabbi ka bashi iko da juriyar daukar duk wani kuruciya da shirme nata, yah azeez kasan yarda nake son gyaruwar komai yah rabbil arshi kasa komai ya gyaru cikin hikima da dabarar ka yah Allah. Nurse din ta sake kallon aydarh wannan karon kanta a kasa yake idonta rufe amma ba bacci take ba tayi wanka duk a takure take jin ta har wani kyankyanmin jikinta take ji ( ah🙄abun naki yayi yawa aydarh) asalin abayar ta ce da tafito daga gida tun farko ta mayar domin tak’I mayarda wanda ta cire, ta fada sosai sai asalin kyauwun fuskarta yafito tarr gashin gabanta kanta yayi luff luff kasancewar veil din abayar da ta daure kanta yayi baya “ can nurse din tace please can I asked you ma’am? Bude idonta tayi kamar bata taba kuka dasu ba wani irin haske da kyau garesu mai matukar daukar hankali da fizga, washe baki nurse Saratu tayi tace dan Allah daga Qatar kuke ko Egypt ni nakasa gane da yan wace kasar larabawan kukayi kama wallahi kunada mugun kyau ke da mijinki kai har kama ma kukeyi auran zumunci ne hala? Aydarh dai tayi shiru domin surutun nurse saratu ya dameta ko gane abunda take fada ma batayi,ganin aydarh bata amsa bay asa nurse saratu tace ko dai ke bakya jin hausa amma naji shi mijin naki hausa raddam a bakinsa wallahi daman baya son yawan magana, still aydarh was quite ganin bazata amsa ta bay asa nurse saratu kama kanta tayi shiru tace mata zan fita idan kina bukatar wani abu sai ki kirawo ni bara nayi ma maigidan naki magana yasamu maki abunda zaki ci, daga haka ta juya ta fita, sai sannan aydarh ta bude ido tana bin dakin da kallo. Dr ibrahim yayi murmushi yace kai kam baka son magana sam sai muna labari sai ka fada tunani, ko dai duk halin da mai dakin naka ke ciki ke damun ka nagaya maka babu wani damu ko zuwa gobe ma zamuyi iya sallaman ku, dan murmushi malik yayi yace tau Allah yakaimu “nurse saratu ce tashigo da sallama office din cikin girmamawa takalli malik tace yallabai asamo ma madam abunda zata ci zuwa yanzu alluran sun sake ta nasan ta isa tafara jin yunwa, kallonta yay isai kuma yace tau a ina zan samu wurin siyarda abinci? Da sauri dr ibrahim yace aa abokina bara nayi waya yanzu a ba yaro yakawo muku daga gida “ kallonshi malik yayi zaiyi magana dr ibrahim ya girgiza kai yace aaa babu komai gidan ai babu nisa kuma ance bakon ka annabin ka duk da ba wajena kazo ba amma ai garin mu kazo, murmushi malik yayi tareda shafa sumar kansa yayi kasa da murya yace tau angode Allah yasaka, Ameen dr ibrahim yace tareda fido android phone dinshi yayi dialing contact din da yayi Saving da iya, bugu biyu aka daga cikin nutsuwa yayi sallama daga can bangaran aka amsa mashi yace iya idan rabi’ah na nan a bata abinci takawo mun yanzu, amsa mashi akayi sannan yayi godiya ya katse wayar, Ko 12mins ba ayi bas ai ga wata matashiyar yarinya kamar aysharsu tashigo da warmer abinci kwara biyu cikin leda sai jug da cups biyu a hannu, tana tsananin kama da dr ibrahim koba a fada maka bak asan sister shi ce ta kalli malik ta gaishe sa ya amsa ta, tace yaya ga abinci amsa yayi yace mata sannu, yauwa tace tana satar kallon malik dayayi kamar bai office din dan ko motsi bayayi, duk abunda take dr ibrahim na kallonta. Kallon malik yayi yace gashi sai kaje ku ci don kaima tunda kuka zo banga ka kai komai bakin ka bah, hannu yasa ya dauki kayan abinci yafita zuwa dakin da take. Bayan fitar malik rabi’ah takalli dr ibrahim tace yaya a ina kasan shi please? Wannan ba balarabe bane kam? Ibrahim ya kalleta yace aaa ba indiye
Chapter 17 · 0% Book details